LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Dafe kanta tayi da kulle kofar tata tana cewa. “Najama kaina. Kai baka san kuncin danakeji araina bane idan naga ka fito daga part d’in TAUDHAT….

….
Da gaske Adams yaji canji agun TAUDHAT canjin dabai tab’a ji arayuwarsa ba.. Dan sanda ta aikata abinda da malamin nata yace tayi.. Dan zama tayi tajanyo sha’awa tayi amfani da ni’imar tata wajan kwab’a maganin.. Sannan tasaka bayan sallar Isha’i
Daqer da sid’in goshi Adams ya iya barinta acikin wannan dare
Shi kansa yayi mamakin kansa..
Dan kwata kwata wannan dare bai samu wani ishash shan bacci ba
Hakan yasa ana idar da sallar asuba bai wani tsaya zakirorin daya saba ba. Ya dawo gida ya kwanta. bashi ya tashi ba sai kusan tara saura
Kuma ahakan ma yana had’a ido da TAUDHAT saiya tuno da daran nasu na jiya nan take sha’awa ta kamasa. Har saida yasamu biyan buqatarsa agaggauce sannan hankalinsa ya kwanta..
Lokacin daya gama shirinsa na fitta office goma saura minti uku..
A hankali ya kalli TAUDHAT yace.. “bazan tab’a yarda da cewar ba abinda kikamin fittarki jiya da kikayi.
Kallansa tayi da murmushi tace.. “Ni TAUDHAT me zan yima mijina kuwa.

Murmushi yayi da cewa “Nafa jiki jiya fiye da yanda nasaba jinki..
“Inaga dai addu’atace ta karb’u wacce nakeyi babu dare babu rana akan Allah yasa kadinga jina fiye da kowace ranah arayuwarka..
Murmushi ya qarayi da fad’in.. “Hmm.. Najiki kuwa. Dan atahirin rayuwata bana tunanin natab’a kaiwa wannan lokacin ba ranar asabar da lahadi ba? ban fitta ba. Ina tunanin tun angwanci na da NUFAISAT..
Dariya tayi da cewa. “Wata qila nima dai kanasan kayimin kara ne wajen hakan…
“Ai kin rigada kinci amarcinki babu kara. Kawai dai naji can jin yayimin ne. Dan ALLAH gayamin miye sirrin..
Tashi tayi cikin shauqi tayafa gyalanta da cewa. “Babu wani sirri. Kaga jeka kaga qawata ina mota ina jiranku kar Ammi tace meyasa bamuzo da wurri ba..
Waro ido ADAMS yayi cikin wani hali yace.. “Ya Allah. Kinsan na manta momy na asibiti. Allah yasa su doctor Aryan sunyi mata wani qoqari..
“Lalle kace kanka ya kulle da yawa..
Bai kulata ba ya ficce daga falan ya nufi na NUFAISAT
Kallan harara NUFAISAT d’in tayi masa.. Yayi murmushi da rungumarta yana cewa.. “Amin afuwa nayi lefi yau ko
Kwace kanta tayi da cewa.. Sam ban d’auka da gaske zaka kai qarfe goman dakace ba..
Shi sai yanxu ma ya tuna wasan nasu na jiya. Dan haka ya fake dace mata ai alk’awari yayi mata…
Da hakan yasamu kanta.
A mota suka tadda TAUDHAT
Sanda sukama kansu kallan kallo ita da TAUDHAT kana ita TAUDHAT d’in tayi mata murmushin qarfin hali dace mata.. “Barka da safiya k’awa da fatan kin tashi lafiya..
Da nuna farin ciki sosai NUFAISAT tace da ita.. “Barka dai.. Fatan kema kin tashi lafiya..
Daqer tace mata lafiya lau. Shima dan taga Idan Adams na kansu ne…

Haka NUFAISAT ta shiga motar ADAMS shima ya shiga direban ya jasu masu tsaran lafiyarsa suka sasu a tsakiya cikin motocinsu suma..

Da suka iso asibitin NUFAISAT kamar tayi kuka ganin halin da mommy Rukayyat take ciki..
Ganin da gaske kukan take sanyi sai kawai taficce daga d’akin taje gun Ammi da kwantar da kanta kan cinyarta ta fashe da kuka tana ce mata. “Dama Ammi irin wannan ciwan yana kama mutum lokaci d’aya haka..
Ammi tace “bar kuka NUFAISAT addu’a take nema. Nima wannan shine karo na farko dana tab’a ganin ganin hakan..
ADAMS ganin NUFAISAT ta fitta sai yabi bayanta..
Ganin hakan yasa salim fitta shima danya d’auko wayarsa amota.. Saiya kasance daga TAUDHAT sai Hajjiya Rukayyat..
Dama Dady yana gida..
Dan haka sai TAUDHAT ta kalli Hajjiya Rukayyat da yatsina fuska tace da ita… “Hmm.. Bake tantiriya ba. Haka siddan dan baqin hali kika bani nama naci dan kawai karna haihu da ADAMS.
shine dana gane kece kikamin hakan nima nayi miki hakan. Dan haka kisa aranki bake ba tashi saidai abaki abinci a baki awanke miki kashi da fitsari har qarshen rayuwarki..
Zaba mata ido Hajjiya Rukayyat tayi da mamaki tace.. “Wai kina nufin kece kikamin wannan abun..
TAUDHAT ta gyad’a mata kai cikin taunar cingam tace. “Nice mana.. Yasan ranki. Wallahi nice nan nayi miki..????
Aiko nan take Hajjiya Rukayyat tafara gurnani nasan tashi amman abin ya faskara. TAUDHAT tayi dariya daci gaba da cewa.. kaji banza. Wai tunaninki zaki tashi ne.
Da b’acin rai Hajjiya Rukayyat tace.. “Zako kici ubanki idan natashi. Dan saina miki abinda harki mutu bazaki tab’a mantawa dani ba…
Dalla mata harara TAUDHAT tayi da cewa.. “Muci uban juna dai. Dan inke kin kwana kina shiri ni a hanya na kwana.
Kajimin muguwar mata haka siddan ki hanani haihuwa da mijina. Shegiya azzalima…
Shigowar Adams da NUFAISAT ne yasa TAUDHAT saurin yin shuru..
Dan fittan Adams rarrashin NUFAISAT d’in yayi dace mata.. Yanxu ba kuka momy take so ba. Addu’a takeso. Dan haka tatashi taje tayi mata addu’a zaifi da kukan da takeyi…

Muje zuwa y’an hannuna????????…

https://www.instagram.com/p/BkZOMcllfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15ya4yksqqc7d&r=wa1
[7/4, 3:13 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 16☆

Gefanta NUFAISAT taje tazauna tana cewa.. “Sannu momy. Bara nayi miki addu’a..
Shuru momy tayi mata dan ranta ba qaramin b’aci yayi ba. Jin TAUDHAT ce tayi mata wannan abu.
A hankali taji tana jin dad’i ajikinta kasancewar addu’ar da NUFAISAT take mata. Jitake kamar ana fusgar wani abu ajikinta. Idan kuma NUFAISAT tayi shuru sai taji abin ya dawo mata..
Anan taqara yarda da abinda TAUDHAT ta gaya mata..
Ammi ta koma gida tayi wasu y’an aikace aikace sanda tadawo sannan su NUFAISAT suka bar asibitin..
Saidai suna tafiya Hajjiya Rukayyat ta d’agama su Ammi da salim da Dady hankali akan amaida ita gida Wannan ciwan nata bana asibiti bane.
Abin ya basu mamaki sosai.. Nan suka shiga lallashinta kan tayi hakuri ad’an gwada sa’a anan d’in aga abinda Allah zaiyi..
Saidai fur taqi yarda.
Lokacin data tayar musu da borin bakwai na dare ne… Dan haka a lokacin ko suka maida ita gida..

Abinda dako yasa Hajjiya Rukayyat rikice musu shine.. Wata aminiyarta Hajjiya Hadiza ce tazo dubata bayan tafiyarsu NUFAISAT. Shine Hajjiya Rukayyan take bata labarin TAUDHAT ce tayi mata hakan.
Shine ita Hajjiya Hadizan take ce mata tota koma gida. Dan wannan ba aikin asibiti bane. Dan saidai su b’ata mata lokaci. Dan haka takoma gida zata dinga zuwa tana kawo mata magani harta samu sauqi
Hajjiya Rukayyat tace yanxu bazata iya samun sauqi lokaci d’aya ba
Kallan mamaki Hajjiya Hadiza tabita dashi tana bata amsa. Kema kinsan cuta lokaci d’aya take kama mutum. Sauqi ko sai’a hankali.
Kedai ki kwantar da hankalinki. Tunda yanxu munsan meyajawo miki ciwan. Baki da matsala wajen samun magani. Kawai bakin aljihu zaki bud’e dan idan tana taqama ita gwanace toh wallahi mune gwanaye. Zataci ubanta ne. Badai tatab’omu ba.
Murmushi Hajjiya Rukayyat tayi danta yarda da qawar tata Hajjiya Hadiza…
Toh wannan shine abinda yasa ta hura masu Ammi wuta kan sai ammaida ita gida..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button