LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

TAUDHAT tasamu yanda take so. dan wani ji da ita Adams yakeyi kamar ya cinyeta..
Dan kam yana samun yanda yakeso agunta.. Shiyasa yake yaqice damuwar rashin samun NUFAISAT da batayi akan hakan…..

Hajjiya Rukayyat tananan yanda take. Dan Hajjiya Hadiza sai shafe mata jiki take da jiqakken ararrab’i a zunmar shine maganin da bokaye suke bata.
Hajjiya Rukayyat bata wani damu ba dan tunda Hajjiya Hadizan tagaya mata babban bokansu yace bazata samu lafiya ba saita d’auki shekara d’aya ahaka ana shafe mata jinkinta da maganin da Hajjiya Hadizan take shafeta dashi Sannan zata samu lafiya.
Wannan yasa tasama kanta hakuri har izuwa lokacin daya iban mata..
Ammi na kallansu dan kotace ga wani agwada mata Hajjiya Rukayyat bata yarda dan Hajjiya Hadiza ta hure mata kunne akan karta yarda a mata amfani da wani magani. Dan bokan yace kar’a had’a mishi maganinsa dana wani..

Yau mommy takawoma NUFAISAT ziyara.
NUFAISAT tayi murna sosai. Sai ajima mommy d’in nata take Wannan ta ajiye mata wancan agabanta..
Komai dai Sanda mommy ta cakala dan nacin NUFAISAT d’in
Sunsha hira sosai har mommy d’in ta buqaci da NUFAISAT takaita shashin TAUDHAT su gaisa.
Nan take gaya mata ai tun safe fitan Adams itama ta ficce daga gidan bata san ina taje ba..
Mommy tace.. “Bakwama junanku sallama ne..
NUFAISAT tace “Munayi. Yanxu ne dai daga baya bamama junan namu saboda ita ta faro hakan. Nima saina kasance idan zan fitta bana yimata.
“Toh hakan bashi da kyau NUFAISAT. Idan batayi miki ba ke duk sa’adda zaki fitta kiyi mata..
“Toh mommy na gode.
“Ba komai. Saidai naga alamu sun nuna kamar har yanxu kina da damuwa.
“Eh ina da ita gaskiya mommy. “Toh mecece damuwar.
“Akan dai wacce muka tattauna dake ne watan nin baya
Shuru mommy tayi.. Sai zuwa can tace. “Wai kina nufin wannan qaiqayi koma kan masheqiyar dana baki baiyi miki ba..
D’aga mata kai NUFAISAT tayi.
Hakan sai yasa mommy Jan numfashi da mamakin y’ar tata. Ganin yanda tad’auki wannan watannin ahaka..
Can taqara Jan numfashi taci gaba da cewa.. Aida kinyi min magana dabaki kai iyanzu da matsalar ba.
Dan duk cutar da take damun bawa idan ya duba qur’ani maganinta na nan
Dan haka ki kwantar da hankalinki. Zanje wajen malam me y’an makaranta nasa shi ya rubuta miki suratul maryam da suratul Alrahama insha Allah ni’amarki data dawo za kuma kisha mamaki
Murmushi NUFAISAT tayi mata dan taji dad’in hakan sosai
Nan mommy tayi mata nasiha sosai dace mata idan suka kammala rubutun zata turo mata dashi..
NUFAISAT tace mata toh.
Mommy d’in tafitoh kenan zata shiga motarta saiga TAUDHAT nan tadawo daga anguwar tata..
Aiko da sauri tayi parking ta fito daga motar tata tagaida mommy d’in..
Da murna sosai mommy d’in ta amsa mata. Kana ta shige part d’inta
Ita kuma mommy d’in ta shige motarta tatafi..

Ashe TAUDHAT d’in tana cikin farin ciki ne yau. Dan bata dena sheqa ayarta da malamin nata ba..
Kwatsam yau taje garesa dan ya bata wasu magungunan mata shine yake gaya mata anya ba ciki bane da ita.. Ai dajin haka tace mai ya duba mata.
Abincikensa na duba ya gane mata da gaske tana da cikin.. Ta kalle shi da murna tace.. mai yanxu zan fara rainan d’an malam bana mijina ba. Kai amma wannan tsinanniyar mata tacuceni..
Dariya malamin nata yayi mata kawai batare daya ce komai
Shine da take kan hanyarta na dawowa gida ta biya wani qaramin asibiti kan amata gwajin ciki dan Allah
Suma sun tabbatar mata tana d’auke da ciki..

Toh wannan farin cikin ne yasata fittowa da sauri ta gaida mommy d’in NUFAISAT tayi part d’inta d’azu

Sai juyin jin dad’i take afalo tana murnar yau dole Adams ya nunama NUFAISAT iyakarta.. Tana San kwana dashi kuma gashi ba girkinta bane..
Shine take San yanxu ta kirasa tagaya masa cewar tana da ciki. Dan idan dare yayi ta kirasa tamai qaryar bata jin dad’i dan Allah yazo ya tayata kwana.. Tasan tunda yana san haihuwa bazai mata musu ba. Qilama ko gayama NUFAISAT d’in bazaiyi ba zaizo gareta da sauri…

Dan haka da sauri sauri tahau kiransa yana d’auka tace mai.. “Ako da yaushe fatan alkairi nake agareka…
Jan numfashi yayi dace mata “Nagode qawarmu. Ya akayi ne.
“K’aramin labari ne. Amman bansan ko awajenka babba bane..
“Toh gayamin. ina jinki.
“Dama ciki ne dani…
Murmushi ADAMS yayi da fad’in. “Mun gode Allah
Tabbas awaje qaramin labari ne. Agun iyayanmu kuma babban labari ne..
Zanso ace da zaki iya kizo asibitinmu yanxu na tabbatar da hakan da kaina…
Duk da taji ba dad’in yanda yace awajensa qaramin labari ne amman hakan baisa tanunamai ba. Dan cike da murna tace mai gata nan zuwa..

Tana isa Adams ya tabbatar da hakan.. Saidai yayi mamakin zuciyarsa dabaiji wani cikken shauqi a cikinta ba..
Dan yayi tsammanin duk lokacin dayaji matarsa nada ciki zaiji mafificin farin ciki. Sai kuma yaga abin ba haka bane..
Wata zuciyar ce mishi tayi kodan ba NUFAISAT bace..
Haka dai ya nuna jin dad’insa ba wani can ba. Dan azahiri ma ita TAUDHAT d’in tafishi zumud’i..

Haka tadawo gida da d’an damuwa dan yanda tayi tunanin zai haukace mata da murna sai taga baiyi mata hakan ba.

Dan haka sai takira malamin nata tagaya mai wai bataga wani farin cikin Adams akan cikin ba
Dariyar mugunta yayi mata da bata amsa.. Haba TAUDHAT. Kema kinsan mutane d’ai d’ai kune matansu suke musu irin hakan sununa farin cikin su nan take
Amman wasu basa jin shauqin hakan aransu tunda ai ba jininsu bane.
Haka dai zasuji farin ciki dan sun kasance sune mazan nasu. Amman Sam basa jin irin sosai d’innan..
Yanxu TAUDHAT ta fahimta. Amma taso daya nuna farin cikinsa da yawa da abin zaiyi mata dad’i sosai
Tana kashe wayar dashi Ammi takirata dayi mata murna ita da Dady

Da daddare ne da misalin qarfe gama sha d’aya da rabi na dare lokacin NUFAISAT na jikin Adams har sun fara bacci sai kiran wayan TAUDHAT ya shigo wayar Adams d’in bayan ya d’auka ne take cemai. “Mijin Qawa bana jin dad’in jikina Sam bana jin dad’insa…
Da damuwa Adams ya tashi kad’an yace.. “Meyake damunki.. “Gashi nan dai kamar zazzab’i ne da ciwan kai harda amai da ciwan baya. Ga ciki na na juyamin kamar zai fitta. Abin dai gashi nan babu dad’i Sam. Dan ALLAH kazo ka kwana dani ko zanji dad’i. Wallahi duk a tsorace nake gani nake kamar mutuwa zanyi acikin daran nan.

Saurin qarasa tashi Adams yayi da janye NUFAISAT daga jikinsa yace.. “Gani nan..
Har yakai kofa NUFAISAT tace mai “lafiya.. me yake faruwa naji kamar kana waya da TAUDHAT cikin wani hali.
“Eh wai batajin dad’i ne. Kuma wai cikin kamar zai fitta.
Waro ido NUFAISAT tayi gabanta na fad’uwa tace.. “Wane ciki kuma.
Dafe kansa Adams yayi da cewa.. “Kinga na manta in gaya miki. Ai tana d’auke da Ciki har na tsawan wata biyu..
Jan numfashi NUFAISAT tayi cikin mamaki tatashi da fad’in. “Muje. Allah yasa karya fittan..
Haka ko suka nufi shashin TAUDHAT d’in sun sameta a can bedroom lullub’e cikin bargo.
Adams ya yayeta dace mata sannu…
Nanta amsa daqer.. Saboda b’acin ran dataji naganin da NUFAISAT yazo.
Nan ya fara duba jikinta baiga wani abin tashin hankali ba.
Hakan yasa shi cewa.. “Jikin da sauqi ashe.. Shine kika wanibi kika rikitani
Da Sanyin murya tace.. “Bakaga yanda yayi min d’azu bane..
“Toh Allah ya sawake ya bada lafiya
“Amiin tace..
NUFAISAT tace.. “Allah ya bada lafiya. Na tayaki murna sosai Y’ar uwa Allah ya saukeki lafiya..
Da baqin ciki tace mata Amiin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button