LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Sai sukayi shuru dukkansu kawai suna masu kallanta.
Gaskiya Adams bazai iya kwana da TAUDHAT ran girkin NUFAISAT ba.
Dan yayi mata alk’awari bazai nuna mata wani hali akan samun cikin da wata matarsa zata samu ba..
Dan haka yace da TAUDHAT.. “Zamuje mu kwanta tunda jikin da sauqi basai an tayaki kwanan bako
“Zanso hakan idan za’a tayani gaskiya. Danni nasan abinda nake ji..
Cikin sauri NUFAISAT tace. “Kaga kaje ka kwanta nina kwana da ita.
Kamar ya dalla ma NUFAISAT mari haka yaji. Saboda baiji dad’in hakan.
Shi bazai iya kwana haka batare dajin d’umin d’aya daga cikinsu ba. Kuma ya lura tsaf futuna TAUDHAT takeji Wallahi ba wani abinda yake damunta.
B’cos ba wani alamar komai na ciwo ajikinta..
Ahankali ya ficcewa daga d’akin yana cema NUFAISAT d’in.. “Hakan yayi..
Yana fitta NUFAISAT ta kulle kofar da zama gefan gadan tana meyi mata kallan tausayi.
Aiko nan take TAUDHAT d’in tatashi da cillar da bargwan jikin nata ta gallama NUFAISAT harara tace. “Ke kam ke kam wannan akwaiki da baqin hali
D’an kwanan dazaki bar shi yayi anan shine abin baqin cikin naki da zakiyi saurin cewa ke zaki kwana dani. Idan kin kwana dani me zakimin..
Kingafa lafiyata qalau. Ba abinda yake damuna.
Kawai Babyn cikina ne yake san jin d’umin babansa..
Da mamakinta NUFAISAT tace “Ikwan Allah.. Wai yaushe zaki dena san kanki da yawa ne TAUDHAT..
Toh har ki mutu baza kiji dumin Adams ranar girki na ba. Dan haka kinga tafiyata..
Kumama tsaya… Da kike maganar Baby nasan jin d’umin jikin ubansa. Ai saikije can wajen wanda yayi miki Cikin yaji d’uminsa dan ba abinda momy Rukayyat bata gayamin ba.
Kasan cewar kar tafito tace kece kika kwantar da itan nan asirinki ya tuno shiyasa tayi gum da bakinta dan bata san asirinta ya tonu. Dan idan naki ya tono itama nata dole ya tonu. Wannan dalilin yasa ta gayamin duk abinda ya faru tsakaninki da ita
Tace duk ran da kika fito kikace kina da Ciki ba Cikin ADAMS bane Cikin wani ne can. dan ita tasan abinda tayi miki. Dan haka tace idan kinfito kince kina da ciki na tona miki asiri nace ba cikin Adams bane.. Sai dai Na gaya mata bazan iya hakan ba.
Saboda Allah na ganinki ni bazan tona miki asiri ba. Amman nasan komin daran dad’ewa shiALLAHN zai tona miki asirin..
Wannan yasa nacika da mamakin dayanzu yake gayamin wai ai kina da ciki. Nayi mamaki sosai dan banyi tunanin zaki iya aikata hakan da gaske da auranki ba..
Dan abin da mamaki matuqa yanda kike da auranki da mijinki dan neman duniya ki iya zuwa wajen wani qatan gard’e ya danqara miki ciki kizo kuma kina pretending kan na mijinki ne..
Nasan komai akanki yanxu TAUDHAT. Dan haka sai gayama wanda bai sani ba kina da cikin Adams. Amma nikam kar nake ganinki. Dan haka kishiga taitayinki ki fitta daga idona karki qara gigin shiga min hakk’i ran girki na akan wannan shegen cikin…
Dan zan miki rashin mutuncin dahar ki mutu ba’a tab’a yi miki irinsa ba..
Sannan ina nemamma momy Rukayyat afuwa kije can wajen bokan naki kice yayi hakuri ya karya wannan mugun asirin da kikayi mata.. Idan fa kinga zaki iya. Idan bazaki iya ba! ba dole dan tsakaninku ke da ita..
Da matuqar mamaki TAUDHAT take kallan NUFAISAT.. Cikin borin kunya tace da ita.. “Kimma kanki gata dabaki ce komai akan cikin nan ba..
Dan wallahi da kince dasai kinga abinda zai faru dake..
Dallah mata harara NUFAISAT tayi da cewa. “Angaya miki tsoranki ne yasani in cewa komai. Ko an gaya miki ina jin tsoran kiyimin wani abu ne..
Kawai dai naga dama ne na qashin kaina nace bazance komai ba. Dan bansan me Allah yake nufi da hakan ba..tana fad’in hakan ta bod’e kofa ta ficce daga d’akin…
Cije yatsa TAUDHAT tayi cikin matuqar baqin cikin yanda NUFAISAT tasan komai…
Adams yayi murnar ganin NUFAISAT dan sai juyi yake ya kasa baccin. Duk dako ba wani abu bane zai shiga tsakaninsu.
NUFAISAT ce mishi tayi TAUDHAT d’in ce tamatsa mata kan tatawo dan zata iya kwana mah ita kad’ai dan taji jikin da sauqi
Jinta kawai yayi dan dama alamu sun nuna mai lafiya lau take
Na gaida ku y’an hanuna…????????????????????????
[7/6, 11:50 AM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 17☆
Washe gari mah gar Adams yaga TAUDHAT..
Yace da ita.. “Wow kice jiki Alhamdulillah..
Murmushi tamai da cewa “Masha Allah..
Kwana uku da zuwan mommy ta aikoma da NUFAISAT rubutun suratul maryam da suratul Alrahaman.. Wanda aka wanke da ruwan kankana..
Aiko tunda NUFAISAT tasha taji tanata zuba. Nan murna ta cikata hankalinta ya kwanta.
Ita da kanta ta nemi mijin nata. Ya kalleta sosai zaiyi magana amman ta hanasa tana cewa “yau nice da ranar..
“Kwananki ne kiyi duk yanda zakiyi dani.. Ya fad’i hakan da murmushi akan fuskarsa. Sannan yaci gaba da cewa.. Amma Allah yasa an samu canji.. Ya fad’i hakan da wani hali..
Fari tamai da ido da cewa.. “Tunda yau kaga hakan. inama kaina fatan alkairi kawai.
Ai dajin hakan yayi saurin rungumarta. cikin farin ciki da jin dad’i dan wallahi duk da yana jin dad’in TAUDHAT sosai yayi missing d’in matar tasa..
Tabbas ya tabbatar tadawo normal
Dan yajita yanda ya dace.
Yaji dad’inta fiye da jin dad’in dayake samu agun TAUDHAT ayanxu..
Komai yayi daidai yanxu. Dan NUFAISAT matsalarta takau..
Sam ayanxu ta rage jin tsanar TAUDHAT aranta. Sannan tasaka aran nata zamanta da ita na wani d’an lokaci ne. B’cos duk ranar da Adams ya san ita wacece cikin dake jikinta ba nasa bane. Tasan bazai qara rayuwa da ita ba
Ita kam ko ajikinta Dan sai rainan cikinta takeyi yana girma dajin wani san shi cikin ranta.
Sam bata dena sheqe ayarta da malamin nata ba.
Haka tasaka aranta zatayi hakuri ta zauna da NUFAISAT tunda ba yanda zatayi da ita.. (TAUDHAT kenan)
Adams bashi da matsala takone b’angare.
Dan baisama zuciyarshi matsalar ba
Duk wani abu da TAUDHAT zatayi danta fake da cikinta dan ya nunama NUFAISAT wani hali toh yayi fatali da wannan abun.
Shi mamaki mah take bashi idan tana irin hakan. Dan Sam baiyi tsammanin hakan daga gareta ba.
Shi yama aureta ne dan yasan ita bazata nunama NUFAISAT d’in wani hali irin hakan ba
Amman sai gashi tana sai lalle saita nuna mata…
Shine tun da ya fuskanci hakan ya taka mata birki shi da ita.
Dan tun ranar da NUFAISAT tayanke mata bata qara gigin aikata mata hakan ran girkinta ba
Amman idan itace da ADAMS d’in tata ja mishi lokaci yayin dazai fitta tace nan na mata ciwo can na damunta. Bata jin dad’in komai. Ire Iran way’annan abubuwan dai. Haka takeyi dan kawai tadinga cinye masa lokaci duk ran da yake a d’akinta..
Saiya fuskanci NUFAISAT tafara fushi dashi
Dako yayi duba sai yaga duk ran girkin TAUDHAT baya fitta da wurri yayin zuwansa office..
Dan har sama da awa d’aya yake qarawa asaman yanda yasaba fitta..
Sai NUFAISAT tafara tunanin ko yafara gajiya da ita ne. Saboda ganin da tayi ita baya kaiwa tsawan wannan lokacin a d’akinta saina TAUDHAT d’in
Dan haka sai kawai tahau fushi dashi
Idan yazo da safen zai mata sallama saitaqi bud’e mai kofa
Dan tasan koya shigo cikin sauri sauri yake ficcewa wai yayi latti. Takance mishi tome yake tsayawa yi duk ran da yake d’akin TAUDHAT d’in dahar lokaci yake tafiya mishi haka..
Baya bata wata cikakkiyar amsa..
Wannan dalilin yasa tadena bud’emai ƙofar kwata kwata