LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Toya gama fahimtar da biyu TAUDHAT take mishi hakan. Daya lura sosai ya gane raina mishi hankali take da zummar batajin dad’in jikin nata toh shine yayanke mata ranar ya gaya mata ta nutsu baya san iskancin banza da hofi. Kota manta shi doctor ne. Yasan yanayin me ciwo yasan yanayin wanda yake da lafiya.. Dan haka ta nutsuwa tadena b’ata mishi lokaci idan zai fitta office. Duk abinda zatamai tamai da dare idan ya dawo gareta..
Toh tunda ya mata haka saita dena mai hakan
NUFAISAT Kuma tadena kullemai ƙofar tata.????

ADAMS ya kanyi murmushi da cewa aransa mata halinsu sai su..

Hajjiya Rukayyat ko tasama zuciyarta hak’uri tana nan tana jiran lokaci yayi tatashi taci uban TAUDHAT

Mommy kullin kiranta ga NUFAISAT nasiha da jan hankali ne.

Zainab tayi nasarar koyama NUFAISAT duk abin daya dace na fannin girki atak’aice..


Da misalin qarfe hud’u4 na yamma TAUDHAT tatashi da nak’uda…
Ba shiri takira Adams awaya. Yace bata gayama NUFAISAT bane.
Tace wai takira number nata akashe.
Da sauri shi ya kira sai kuma yaji a kunne. Cikin saurin yake gayama NUFAISAT d’in taje part na TAUDHAT ta temaka mata da had’a kayan Baby gashi nan zuwa wai nak’uda tatashi mata ne..

Cikin tausayawa ko NUFAISAT taje gareta.. Aiko tsameta tana jin jiki sosai.
Nan tatambayeta inda tasa kayan baby bako musu ta gaya mata..

NUFAISAT na had’a komai saiga Ammi tazo dan Adams d’in ya kirata ya gaya mata.
Haka dai Ammi tadinga bata temako irin nasu na manya har sa’adda Adams d’in ya iso
Nan suka shigar da ita mota sai asibi….

TAUDHAT ba ita tasamu kanta ba sai wajen qarfe tara na dare. Inda tasamu Haifo Baby girl.. Bebinta mace kyakkyawa da ita fara soll

Dangi kowa sai murna yake da zuwan wannan jinjira..
Sanda ta kwana aka sallamota b’cos bata tare da matsala

Sosai TAUDHAT ta yarda dangin Adams suna san ganin jininsa.
Shuru tayi kawai tana saka dama ace namiji ta haifa…

Mamanta ta kirata akan zata aiko mata da kayan data siya mata dan asaka akayan suna..
Nan take ta dakatar da maman wajen gaya mata karta aiko mata da masu araha. Tabarshi ita tayima kanta kaya na gani na fad’a
Shuru maman nata tayi.. Itafa har yau bataje gidan nasu ba.. Dan tunkan bikin Adams d’in da TAUDHAT d’in rabanta da gidan NUFAISAT d’in
Amman ko kad’an TAUDHAT bata damu da taje d’in ba..

Dan haka ita sai tayi aiki da hankali ana kwana uku da haihuwan taje gidan nasu amman a d’akin NUFAISAT tatare.
NUFAISAT d’inko taji dad’in hakan. Dan har labarin yanda auran na ADAMS da TAUDHAT d’in sanda maman tagayama NUFAISAT. Bayan kuma abinda TAUDHAT d’in take mata
Sanda NUFAISAT tayi kuka. tace narasa wanda ya b’atama TAUDHAT tarbiya..
Mama dai shuru tayi mata dan ji take dama NUFAISAT d’ince y’arta

Ganin irin dad’ewar da maman tayi a part d’in NUFAISAT d’in sai TAUDHAT ta balbale maman da fad’a lokacin da taje part d’inta
Wai akan wane dalili zataje part d’in NUFAISAT ta zauna
Ai wannan munafunci ne. Dan haka karta qara zuwa mata gida dama ai ba gayyatarta tayi ba bare tazo ta nunama duniya bata qaunarta kishiyarta take qauna dan tsabar munafunci…
Ran mama yayi matuqar b’aci nan take taji LAMARIN Y’ar tata ya isheta haka. Dan haka saita kalleta cikin matuqar b’acin rai…
Tace “TAUDHAT Ni kike gayama haka.
Aiko TAUDHAT ta galla mata harara tace… “aa da iska nake badake ba. Kinsan ai mu d’ari ne acikin d’akin dazaki wani ce dake nake.
Tashi mama tayi da yafa gyalanta tace.. “Har abada bazan qara zuwa inda kike ba TAUDHAT.. Haka ni bazan hanaki zuwa inda nake ba saidai ni bazan qara zuwa inda kike ba… Maman na kawowa nan a zancenta ta ficce daga bedroom na TAUDHAT d’in tama y’an barka na falan nata sallama sannan taje gun NUFAISAT tayi mata sallama NUFAISAT ta bata turare da atamfa biyu. Nan tamata godiya sannan tabar gidan dajin haushi da tsanar y’ar tata…

Ranar suna yarinya taci Sunan maman TAUDHAT d’in.. Wato HAFSAT.
Dan Adams Sunan Amminsa yaso sawa sai Ammin tace ya saka Sunan maman TAUDHAT d’in..

Bai san dalilinta nayin hakan ba.
Haka aka saka ma yarinyar sunan..

TAUDHAT ansamu abinda akeso dankam tasamu kaya kasancewar ADAMS me bayarwa ne hakan yasa kowa yake san yayi masa bajinta.. Anyi bidiri bired’e awannan suna
Dan qawayenta tantiran y’an iska sanda sukazo mata..
Kallo d’aya NUFAISAT tayi musu gabanta ya fad’i.. Dan ita ko’a mafarki idan akace mata TAUDHAT zatayi aminta da waƴannan qawayen zata qaryata.. Amma gashi dake ba’a shedar mutum gashi nan tagani a zahiri…

Baqin cikin da TAUDHAT taso taga NUFAISAT aciki ranar sunan nata sai taga Sam bata tare da wannan baqin cikin.. Dan Sai warwala takeyi abinta tana Shiga tana fitta hankalinta kwance.. (Yo Allah yaga zuciyarta ya kuma dafa mata)

Saiya kasance TAUDHAT d’ince kicin b’acin rai dan haka kawai taji ranta baya mata dad’i. ( duk abinda zakayi idan ba dan Allah zakayi ba na banza ne. Kuma ALLAHN bazai baka yanda kake so d’in ba)

Wasu matan masu jego suna barin miji agun abokiyar zamansu bisa al’ada…
Amman rashin barin shiyafi alkairi ga maso jegwan dan sune da riba.
Akwai wani d’umin juna na qara so da shak’uwa dayake samuwa yayin da me jego takwanta gado d’aya da mijinta da abinda ta haifa..
Wannan dalilin yasa masana sanin SOO da qauna basa barin matayensu dan suna jego. Haka Matan masana sanin K’AUNA basa tab’a yarda su yada mazajensu yayin da suke jego.
Duk da cewa ba wai wani abu bane zai faru tsakaninsu.
Kawai ana buqatan sudinga jin d’umin junan nasu ne..

TAUDHAT bata san da hakan ba. Amma ADAMS yasan da hakan.
Saidai dama ita TAUDHAT ko kad’an bataji aranta zata iya barma NUFAISAT Adams har na tsawan wata da kwana goma ba..
Wannan dalilin yasa tayanke hukunci akan koda Adams yazo mata da zancen tabarshi gun NUFAISAT zatace mishi bata yarda ba..????

(Toh tama kwantar da hankalinta inji Rahma Nalele)

Dan a washe garin ranar sunan dama itace da girki.
Dan haka Adams yazo gareta dan su kwana
Amma me. Sam taqi ta kula da jikinta yanda ya dace dan yana daga nesa da ita yake jiyo qarnin jininta
Dan haka yace mata dama yazo ne dan ya tayata kwana sanadin yanda take jego basai tazo garesa ba..
Amman tunda har yanxu qarnin jininta bai rabu da ita ba zaije part d’insa. duk sa’adda ya d’auke tamai magana.. Tace mai toh ammadai ba da NUFAISAT zai dinga kwana ba ko.
Murmushi yayi mata da mamakinta yace. Ko kad’an. Kamar dai yanda suka saba hakan ne zaici gaba dayi musu..

Murmushi tayi batare da tace mai komai ba
Ganin hakan yasashi ficcewa daga d’akin dan qarnin ya ishesa

Hakance ko ta kasance. Yana bama kowa hakk’inta na kwananta kamar yanda ya saba.
Ran girkin NUFAISAT yana manne da ita ran na TAUDHAT kuwa saidai ya rungumi filo

Ahaka TAUDHAT tayi arba’in amman duk da hakan sanda Adams ya qara mata kwana biyar kafin ya kulata ta fannin kwanciya…


Komai yayi daidai dan Haneepha yarinyar tasu (deke haka suke kiranta dashi). Tayi wayo ayanxu Dan shekaranta d’aya yau. gudunta take yi ko’ina ga baqin magana..

NUFAISAT duk da tasan ba y’ar Adams bace hakan baisa taji wani abu naqin ciki akan yarinyar ba..
Dan sosai take qaunarta..
Tun TAUDHAT na hanata y’ar hardai ta hakura tafara bata. Dan ba qaramin cin ubanta Adams yayi wata ranah
Da yayi mantuwa ya dawo d’auka yaji TAUDHAT d’in tanama NUFAISAT gori akan haihuwa dan kawai taje tace tabata yarinyar tamata wasa..
Ran Adams bai tab’a b’aci irin na ranar ba..
Anan yayima TAUDHAT d’in saki d’aya yace tatattara tatafi gidansu ya saketa. Sannan ya kuma kwace y’ar yaba NUFAISAT ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button