LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Hankalin TAUDHAT ba qaramin tashi yayi ba daqer da sid’in goshi Amminsa da Dadynsa suka samu kan Adams d’in ya dawo da TAUDHAT d’in
Dan maman TAUDHAT d’in da TAUDHAT d’in tazo mata da maganar ko kallanta batayi ba.
Dan tana nan da jin haushinta na wulaqancin data mata kafin sunan haleephan
Hakan ne yasa TAUDHAT jan tsaki taje tasa su Ammi agaba da magiya shine dalilin da yasa suka samu kan Adams d’in ya maida ita..

Tana dawowa ko NUFAISAT taje tabata y’ar tata. Da cewa wallahi TAUDHAT kibi duniya Ahankali idan da kara da mutunci baici ace kinyimin gori akan haihuwa saboda wannan Y’ar taki ba. Nasani kin sani ba y’ar Adams bace. Ta wani ce can daban Amman sabo mugun baqin halinki kina neman rasa igiyar auranki akan baqin tunaninki…
Dalla mata harara TAUDHAT d’in tayi da fizge yartata..

Tunda daga ranar bata qara hana NUFAISAT yarinyar ba. Idan har NUFAISAT d’in tazo d’aukarta zata bata ita..
Kawai shed’an ne yake yawo akan TAUDHAT dan sarai tasan NUFAISAT bazata cutar mata da Y’a ba…


Ayau ne Hajjiya Hadiza tagaji dacin kud’in Hajjiya Rukayyat. Tasaka aranta zata nema mata magani na Gaskiya
Dan takai shekara d’ayan da kusan rabi fiyema da haka shuru
Sai dad’in baki da take mata

Toh yazu gata gaban wani malami tagaya masa matsalarta ya bata magani yace taje tabata tasha sannan ta shafe mata jiki dashi…

Aiko tunda tazo tayi mata haka cikin iko na Allah saiga Hajjiya Rukayyat tatashi..

Kwananta uku da dawowa normal taje wajen bokanta akan ya haukatar da TAUDHAT

Aiko nan yake gaya mata aiki akan TAUDHAT ba qaramin abu bane..
Dan wani malaminta nayi mata aiki
Saidai idan tana san ayi mata wani abu toh tayi qoqarin kawo mishi jinin al’adar ita TAUDHAT d’in da ruwan ni’imarta

Hankalin Hajjiya Rukayyat ya tashi
Anan taqara tabbatarwa lalle dole TAUDHAT tacika mata baki.
Amman ba komai idan kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu had’u ne.
Wallahi tasha alwashin zaita wargaza rayuwar TAUDHAT..

Lokacin da TAUDHAT taji tashin Hajjiya Rukayyat d’in ji tayi kamar taji hauka
Nan takira malamin ta yace takwantar da hankalinta dama haukatata tasoyi. Amman ai tana dashi. Kawai taci gaba da lura mishi da y’arsa…
Jin hakan yasa hankalin TAUDHAT kwanciya kamar tsumma aranda..????

✋????✋????✋????✋????✋????✋????✋????✋????✋???? “Stop.. Ya kamata NUFAISAT TAUDHAT ku tsaya a haka… Naje can qauye nagano MUSLEEMAT… Nice Rahma Nalele ce me fad’in????
Junior RAMADAN dake gefena yace “Ya kamata kam my Aunty. Yanxu kin shiryane nakai ki can qauyen cikin daqiqa biyu..
Murmushi nayi da cewa. “Aiya kamata ADAMS yayima su NUFAISAT sallama me tsayawa arai.
Yace “kuma fa haka ne..
????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????Na gaida y’an hannu na????????????????????????

????????‍♀
[7/9, 2:44 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 18☆

Dalilin dayasa ADAMS yake tare da masu tsaro shine… Ashe shekarun baya tunda ya fara tashen kud’i sai mahassada suka sashi agaba.
Sam baza’ace gasu ba.
Saboda sunqi fitowa su nuna kansa bare ad’au hukunci akansu.
Wata rana yana dawowa daga wajen kasuwancinsa. Dan ranar bata zuwa asibiti bace agaresa. Haka wasu mutane suka taresa suka mai dukan mutuwa.
Sanda ADAMS ya shafe wata d’aya yana jinyar kansa.
Haka daya tashi bayan kwana uku da tashin nasa still suka qara taresa suka dad’a mai irin wannan dukan.. Suna gayamai Wanda yasa ogansu wannan aikin rayuwarshi yake so. Su basuso su kashesa saboda alkairin daya tab’a yima ogansu. Suna bashi shawara yabar garin Kaduna ya koma can wani gari da rayuwa…

Wannan karan sanda ya kai wata biyu kafin yasamu kanshi.
Shiga tunani yayi sosai wajen tuna kalaman da suka gaya masa yayin da suke mai wannan duka. Shi sam baisan waye wannan ogan nasu da yake san rayuwarshi ba..
Haka kazalika bai tab’a ganin fuskokin masu mai dukan ba. Dan idansu arufe yake ba wata alama da suka bari yanda zai ganesu…

Wannan yasa hankalin Dadynsa ya tashi yace dole ya dinga yawo da masu tsoro..
Da Adams yama Dadyn nasa musu akan me zaisa ko’ina zashi sai yayi yawo da masu tsoro. Shi baya sha’awar hakan sam. ALLAHn daya yisa shizai karesa.. Ba qaramin yaqi Dadyn yayi dashi ba kafin ya yarda ya samu matsaron lafiyar tashi. Sai Allah ya had’asa da nagari wanda sam basu da niyar cin amanarsa. Saboda yanda suke tunanin zai kyautata musu sai sukaga aihar ya zarce hakan wajen kyautata musun.. Dan haka sukaqi bama wanda yake san ganin bayan nasa had’in kai. Dansu sun sanshi sarai sundai k’i gayama ADAMS d’in ne saboda sun gaya masa yanda suke da ilimi wajen saran lafiyar mutum zasuyi amfani da wannan ilimin nasu wajen gujema duk wani hari dazai kawo ma Adams..
Dan haba bazasu gayama ADAMS ba. Dan sunsan zai d’auki mataki ne. Kuma kunga su shikenan fa sun rasa wannan garab’asan da suke samu agunsa ba..
Sannan sunyi ilimi da Allah zasu tsare lafiyarsa dayakar qarfinsu da aiki da iliminsu…

Wannan yasa mekaratu yake ganin Adams da masu tsaro tun farkwan fara karatunshi….


Yana breakfast a falan NUFAISAT Yayinda Haneepha take kan cinyarsa sai zubamai surutu takeyi irin na yara..
Sam hankalinsa baya kanta yana kan NUFAISAT da tayi tagumi kawai saboda maganar daya gaya mata tun shekaran jiya na wai zaiyi tafiya…
D’an shafan gefan fusakarta yayi cikin so da qauna yace.. “Haba my luv. Wai miye ne haka. Ke dazaki bani qarfin gwiwar zuwa amma saiki jefa kanki cikin tunani dan kisa ZUCIYATA rawa ko..
Kallansa tayi cikin damuwa tace.. “Wallahi ba haka bane mijina. Kawai dai kasan baka tab’ayin tafiya bane kabarni haka
Murmushi yayi da cewa.. “Kwana hud’u nefa kawai zanyi. Kuma ya kamata kibani qarfin gwiwa dan nagaya miki waye Ibrahim agaremu.
Ibrahim shine wanda mukayi skull kaf dashi. Kawai bamu cika shiga harkarsa bane nida Yusuf saboda halinmu ya bambanta da nashi..
Ko yaushe yana san jammu cikin al’amuransa mune dai muke kauce masa. Amman yanxu ya dace mununa masa bama qinsa mununa masa farin cikinmu akan abinda ya samesa na alkairin nan.
“Toh shi kenan dama haka kawai ne naji gabana na fad’uwa akan tafiyar sam bana san kayita Wallahi. Bana so. amma tunda ka kafe Allah yakaika lafiya ya dawo min dakai lafiya..
“Yauwa matata dama hakan nake sanji daga gareki.

Yana gamawa ya sauke Haneepha da rungumar NUFAISAT d’in ya b’ata lokaci sosai yana kissing d’inta kamar bazai barta ba. Can dai ya barta da nufar part d’in TAUDHAT itama dai tanuna mai bata san tafiyar amman tunda yana so itama tanai mishi Fatan alkairi…

Tabbas shima yaji wani iri lokacin daya shiga motar tashi dan ganin yanda jikin NUFAISAT yayi sanyi.. Haka ya sakar mata murmushi yace direban nashi yaja motar..
Haka sufa ficce dashi daga gidan yana me d’agama Haneepha hannu alamun bye bye…

Direct gidansu yayi.. Nanko yagasu Dady da Amminsa cikin damuwa. alama tanuna suma hankalinsu bai kwanta da tafiyar tashi ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button