LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ibrahim abokin Adams da Yusuf ne..
Sam halinsu yasha bambam da nashi. Wannan dalilin yasa ba kowa bane yake yarda ma abokinsu ne. Saboda yanda suke guje masa sam basu san wuld’a dashi tunda suka dawo daga karatu daga waje..
Katsam acikin satin nan saiya kirasu yake gaya musu ya bud’e wani asibiti nashi na qashin kansa a garin da mahaifiyarsa take jahar Gwambe.
Amman dan Allah kar suce mai basu suzo ba dan yana san yayi walimar bud’e asibitin tare dasu.. Walimar biyu ce. Data ranar jumma’a data ranar lahadi.. Kuma yana san dukka ayi dasu.
Sunji kunyarsa sosai hakan ne yasa suka amsa masa dato zasuzo kuma za’ayi komai dasu…
Tunran alhamis Yusuf ya tafi dan lokacin jikin Dadyn Adams bai gama warwarewa ba kasancewar yayi zazzab’i kwana biyu da suka wucce..
Hakan yasa Adams yace yaje shi yaxo ran asabar yasamu walimar ta ranar lahadin
Haka ko akayi nan Yusuf ya tafi..
Kuma har ya tabbatar mishi da cewa ya sauka lafiya dake tafiyar jirgi ne.
Toshi haka kawai Adams ya tsinci kansa dasan tafiyar mota..
Danya ankawo masa wata fitacciyar mota me inganci wacce tazarce kowace mota cikin motocinsa a kud’i… Dan haka sai yaji yana san tafiya da motar..
Kuma baya san tafiya da maso tsaran lafiyansa.
Dayake gayama su Dadynsa da Amminsa sai hankalinsu ya tashi sukace basu yarda ba
Dan basu manta yanda aka mishi lokacin baya da yake yawo shi kad’ai ba
Murmushi yayi dace musu haba dai. Yanxu koma waye maqiyin nasa ai yaci ace ya haqura ya dena bibiyarsa tunda yanxu rabansa dashi kusan shekaru takwas kenan.
Jin hakan yasa hankalin nasu kwanciya.. Amma yanxu ganin da gaske tafiyan zaiyi sai kuma sukaji tashin hankalin ya dawo musu…
Murmushi ADAMS yayi dan ganinsu cikin damuwa. Haka ya kalli Dadyn nasa yace.. “Dama Dady nazo muku sallamar ne..
Murmushin yaqe Dadyn yayi masa dacewa.. “Anya bazan hanaka tafiyan nan bako ADAMU
Da sauri Adams ya qara tsaida idanta akan na Dadyn nasa yace… “Dan Allah karka hanani Dady.. Bafa wani abun dazai faru. Kawai addu’arku nake nema nasan idan har kukamin bazata fad’i qasa banza ba..
Jan numfashi Amminsa tayi da cewa toh Allah ya saukeka lafiya ya dawo mana dakai lafiya.. Sannan ka kula da hanya kasan ba sanin wajen kayi ba..
“Insha Allah Ammina
Kuma ai kinga tare da Sunusi zamu dan yaje gwamben kusan sau biyar tunda acen Mahaifinsa yanxu yake da zama.
Dan haka baza mu sami wata matsala ba
Jin hakan yasa hankalinsu kwanciya amman duk da hakan sunso da ace girgi yabi. Da hankalinsu yafi kwanciya…
Haka yayi musu sallama duk da baqin hali irin na Hajjiya Rukayyat sanda itama taji aranta kamar karya tafi..
Salim mah jiyayi kamar yayan nasa yayi tafiyar shi..
Haka lokacin da yakema matsaransa sallama akan su kwantar da hankalinsu ba abinda zai samesa yaudai ranah d’aya ai ba wani abu bane. Fatansa dai suba matansa kulawa dan baya san yaji wani abu ya faru dasu… Da sanyin jiki suka bashi mukullin motar da zaiyi tafiyar da ita.
Haka yaba Sunusi ya shige bayan motar Sunusin ya zauna wajen mazaunin direba yajasu sukabar harabar gidan zuciyar Adams cike da qaunar iyayen nasa….
Biyan Sunusi akayi wato d’aya daga cikin direbobin Adams d’in..
Kasancewar direbobin nasa uku ne..
Kuma shima kansa Sunusin sanda yayarda zaiyi abinda suke so sai daga baya kuma yazo yana na damar yanda yake qoqarin cin amanar ogan nasa wanda yayi masa dukkanin gata..
Wannan dai maqiyin nasa ne har yau yake san neman rayuwarsa.. Dan dad’ewar da yayi wajen lamfo kamar ya rabu da Adams d’in shekara da shekaru. Ashe dad’ewar shirye shiryen yanda za’ayi ya cimma burin nasa akansa ne..
Toh yau yana neman cin sa’a da nasara akansa…
Dake ADAMS bai san yanyar garin Gwamben ba shiyasa sam baisan inda Sunusi yake jefa k’afar motar tasu ba…
Hasalima shi karatun jaridarsa yake yi idan yaji Sunusin ya tsaya awani
waje yakan kalli wajen idan yaga da mabarata ko gajiyayyu sai yaba Sunusin kud’i ya basu….
Sunsha uwar tafiya wanda sai yanxu nadamar qin shiga jirki tazoma Adams.. Danshi arayuwarsa bai tab’a tafiya irin wannan ba..
Cak ADAMS yaji Sunusi ya tsaya da tuqin mota. Duk da bacci ya fara fuzgarsa. Jin tsayuwar motar shiyasa shi bud’e idansa..
D’ago kansa da zaiyi kawai saiya gansu kan titi gashi gabas da yamma cikin daji suke.. Dajin dabazai iya cewa ga inda suke ba.. Gashi abin mamaki wasu mutane ya gani su goma.. Murd’add’u da alama ma kad’an daga cikinsu sune way’anda suke kawo mai hari shekarun baya dan yaga hakan atattare dasu..
Uku bindiga ne ahannunsu sauran kuma qarfuna ne da sandina a nasu hannayen..
Fitowa Adams yayi kamar yanda Sunusi ya fitto..
Cikin Dariyar mugunta suka d’aga bindigarsu sama suka setata akan Adams..
Cikin sauri Sunusi ya fashe da kuka yace dasu. “Dan Allah karku cutarmin da oga na. Karku kashesa.
Nayi muku abinda nayi muku amman ina cikin nadama. Saboda naci amanar wanda ya yarda dani. Na munafurcesa bayan yayi min dukkan gata.. Wallahi me gida nayi maka abinda bai dace ba. Dan Allah ka yafemin.. Sunusi ya qarashe maganar da kallan Adams ya kama qafarsa alama ban hak’uri..
Cikin mamaki Adams ya kalli Sunusi yace.. “Wai me yake faruwa ne..
“Oga way’annan mutanan ne suka bani kud’i me yawan gaske sukace duk yanda za’ayi nayi dan kayo tafiyar nan dani. Dan sun samu labarin zuwanka gwamben kuma a mota. Shine sukace nakawo musu kai cikin dajin nan da zaran tafiya tayi nisa. Oga ban san manufarsu ba. Kawai na duba yawan kud’in da suka ban ne.. Sunusi ya fad’i hakan daci gaba da kuka..
Nan ADAMS ya rintse idansa yana tuna yanda yabar matansa iyayensa. Ya tabbatar tunda ya had’u da way’an nan mutanan wannan karan ba barinsa zasuyi ba.
Dan haka da wani hali ya kalli Sunusin da cemai. “Karka damu Sunusi nayafe maka.
Aiko kan Sunusin yace wani abu wani daga cikin masu d’auke da bindigar ya harbe kan Sunusin da bindigar hannunsa…????
Jikake fasss..
Ai arikice Adams ya tashe yaje ya rungumesa yana me kiran sunansa.. “Sunusi Sunusi Sunusi katashi katashi dan Allah.. Amma ina ko alamar motsawa Sunusi baiyi ba.. Saboda rai yayi halinsa…
Gabaki d’aya Adams ya rikice fad’in musu yake.. Kun kashesa fah. Ya mutu. Wallahi kun kashesa.. Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un… Haka Adams yaketa fad’a hankalinsa tashe..
“ADAMCY kenan.. Mun gayama kabar garin Kaduna idan kana san ganinka da lafiya kuma a raye..
Sai kaqi. Ka zauna abinka baka tare da wani tashin hankali. Saboda kayima kanka gata kana da masu tsaro..
Sai gashi yau tunaninka ya toshe ka fito inda baka tab’a zuwa ba batare dasu ba..
Oganmu ya gaya mana bokan Wanda yasa shi wannan aikin akanka ya gaya masa idan har kana garin Kaduna sunansa da azziqinsa bazasu tab’a suna ba. Bazai tab’a zama wani ba. Shi kuma yana san ya fika tako ta’ina….
Wannan dalilin yasa yace mu kashe masa kai.
Saidai mu bamu san muyi maka hakan saboda katab’a temakwan oganmu. Shine yasa muke maka dukkan tsiya dan mu hanaka tashi bare kaci gaba da aiwatar da harkokinka.
Saiya kasance katashi. Muka dad’a maka wani dukan dace maka kabar garin Kaduna idan kana san zama da rayuwaka. Amman kaqi.
Yanxu ma ba kasheka zamuyi ba. Saboda mu ba butulu bane munsan wanda yayi mana. Zamu qara maka wani dukkan ne wanda bazaka moru ba bare kaci gaba da aiwatar da ayyukanka ka hana wancan maqiyin naka cika burinsa…
Kan ADAMS yace wani abu sun fara kai masa duka a inda suke da tabbacin idan suka dakai bazai iya muruwa ba.. Da qarfuna da sandinansu suka fara kai mishi wannan duka
Duk da cewar bawai kallansu yake ba. aa yana qoqarin kare kansa. Dan sosai suma yayi musu b’arna. Wajen rama abin da suke masa. Toh kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin qarfi.. Hakan ne yasa yaqi cin galaba akansu.. Dan d’aya daga cikin su yana d’aga sandarsa saiko ya sauke ta a qeyarsa wanda nan take ADAMS ya jirkice ya zube awajen tamkar wanda ya mutu. Dan babu alamar rai atare dashi