LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL


Kasancewar mahaifin TAUDHAT ya rasu tun tana shekara goma.. Hakan yasa abubuwa dadama suka canja na rayuwa acikin gidan nasu
Ya zama talauci yayi musu qatutu..
Hakan yasa mahaifin NUFAISAT da mahaifiyarta suke temaka musu kasan cewarsu makwaftan juna
Toh ZUCIYA da buri
Hakan yasa TAUDHAT taga bata mallakan komai na rayuwa kamar yanda NUFAISAT take mallaka
Saboda mahaifin NUFAISAT Babban mutum ne.
Yana da arziqi
Toh ance Idan har da hassada azuciyar Wanda kake kyautatama baizai tab’a ganin abunda kakemai ba
Da TAUDHAT nake.. Dan NUFAISAT ta kasance me tausayinta.. Idan za’a dinka mata kaya daru take sawa sai’an d’inka mata Ita da TAUDHAT
Tun mahaifiyarta najin haushi. Har taxo tadena. Jin haushin
Saiya kasance komai da zakasan NUFAISAT dashi. To katabbatar zakaga TAUDHAT dashi
Dan komai biyu iyayan NUFAISAT sukeyi
D’aya na NUFAISAT d’aya na TAUDHAT
Amman hakan bai hana TAUDHAT lalacewa ba
Dan bataso komai ace iyayan NUFAISAT ne suke musu
Wannan dalili yasa tafara bin maza
Tun ana amfani da ita abata kud’i kad’an hardai tazo ta kile tafara karb’ar manyan kud’ad’e
Saiya kasance rabin kud’in zata dinga kawowa gidansu tana amfanin yau da kullum dukda ba abinda iyayan NUFAISAT suka ragesu dashi
Tun mahaifiyar TAUDHAT bata ganewa hardai tazo tagane me y’arta takeyi take samun kud’i haka
Hankalinta ba qaramin tashi yayi ba data san me Y’ar tata takeyi
Saidai kash… lokacin data sani ya qure dan ba qaramin bokaye da malamai TAUDHAT tasani ba..
Wancan rabin kud’in da take b’oyewa a wajen bokaye da malamai yake qarewa da maganin mata. dan kawia tasamu maza yanda takeso..
Wannan dalilin yasa data ankare mahaifiyar tata tagane me takeyi sai kawai takaima wani boka sunan mahaifiyar tata tace ya rufe mata bakinta sai yanda tayi da Ita
Aiko haka akayi.. Koda mahaifiyar tata tanufeta da batun mekaita aikata karuwanci. Tashi tayi tahau mahaifiyan da fad’a tana nuna mata bazata iya rayuwar saidai wasu su basu ba
Shuru mahaifiyar tata tayi mata..
Ganin hakan yasa TAUDHAT d’in tasan aikin boka yaci mahaifiyar tata..
Saiya kasance tafara tsola tsiyarta yanda take so agaban mahaifiyar tata…
Dan tasan ba abinda uwar ta’isa tayi mata
Saidai duk abinda takema mahaifiyar tata bata tab’a yarda tayi mata agaban NUFAISAT.
Ta hakan ne mahaifiyar tata tagane duk abinda TAUDHAT d’in takeyi NUFAISAT bata da sani akai…

[29/04 12:05 pm] ????◾◼▪????: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 04☆

Abin na damun Maman TAUDHAT d’in yanda lokaci d’aya tafara jin tsoran TAUDHAT d’in

Ana haka ADAMSY ya fitoh Auran NUFAISAT
Saboda ganinta da yayi a bikin Yayarta Zainab
Kallo d’aya tamai ta amince dashi
Har akayi bikin NUFAISAT da ADAMSY TAUDHAT bata da nutsuwa
Dan tun ranar da NUFAISAT tazo mata da batun ADAMSY yace yana santa… Tun daga lokacin take shirye shiryen yanda zatayi tajuyo da hankalinsa izuwa gareta

Tak’i samun nasara danshi me ibada ne. Shi me nema agun Allah ne.
Wannan yasa har akayi bikin NUFAISAT dashi bata samu yanda takeso ba
Dukko da irin bin bokayen da takeyi da malaman…
Wannan dalilin shiyasa tacusa kanta ga yimasa abinci tunda tasan ba abinda NUFAISAT bata iyaba sai girki… Shima dan batayi agidansu ne..

Sai hakan yaba TAUDHAT damar yimai barbad'e cikin abincin da takemai. Dan kawai karya gaji dacin girkin nata. 

Wannan dalilin yasa kobaiyi dad’i ba. Baya ganewa.. Dan yarigada ya saba da girkin nata

Kuma iyawar tata ba wani can bane
Saidai tafidai NUFAISAT d’in dabata iya ba.
Wani malaminta ya tabbatar mata da cewar saita dage sosai wajen d’auke hankalinsa akan kowane abincin da zaici inba nata ba. Sannan zata shiga ransa har tasamu damar shiga gidansa matsayin matarsa ta biyu…
Wannan shine dalilin dayake sawa qarfe goma Sha d’aya na safe nayi take zuwa gidan NUFAISAT tayi mata girkin rana akai masa. Sannan tayi mata na dare tajirasa ya sauketa agida..
Tayi wani saban boka. Wanda yace mata tasan yanda zatayi takawo NUFAISAT ya ganta. Kawai ganinta Idan yayi azahiri shi zaisa ADAMSY ya Aureta ko aranar ne…

   Kullun tunani takeyi. Ya zatayi takai NUFAISAT gunsa 

Dan tasha cusama NUFAISAT d’in ra’ayin bin kalamai akan matsalar haihuwan datake fama dashi
Yau shekarunta da ADAMSY shidda kenan amman bata tab’a samun ciki ba
suna karb’ar magani sosai
Saidai komai sai Allah yayarda
A binciken da ADAMSY yasa kwararrun likitoci sukama NUFAISAT d’in sun gano bazata tab’a aihuwa ba!!! Ita bata da kwan haihuwa….
ADAMSY yaqi gaya mata
Dan baqaramin so yake mata ba
Kasancewar tatara duk abinda yakeso agun mace
Ta iya duk wani abu da yake so agun mace
Matsalarta biyu ce agaresa
Shine bata iya girki ba
Kuma bata damu ta’iya ba
Yana San mace me shagwaɓa. Amman baya samun hakan agunta
Saidai yanaji aransa zai rayu da Ita a hakan

Yana matuƙar San yara
Hakan yasa yajema iyayansa da batun zai d’auko yaran marayu biyu ya rainesu..
Dake mahaifiyarsa itace amarya agidan mahaifin nasa.
Kuma bata isa tayanke wani hukunci akansa ba
Saboda uwar gidan mahaifinsa tagama da mahaifin nasa. Watoh Hajjiya Salma
Kuma itama haihuwanta d’aya da mahaifin nasa… Saida mah mahaifiyarsa hajjiya Rahma ta haifesa bayan wasu shekaru uwar gidan hajjiya Rukayyat ta haihu..
Dan har tacire rai da haihuwan..
Shine take haifan Salim Wanda yanxu shima ya girma yake kula da supermarket d’in ADAMSIN…

Wannan abu yana b'ata ma Hajjiya Rukayyat rai... Yanda ADAMSY yake juya nera.

Hannunsa me albarka ne
Dan duk abinda yasa agaba zaiyi kasuwanci akansa tosaiya samu albarka…
Gashi doctor.. Ga kasuwanci.. Gashi duk fad’in garin KADUNA bawanda baisan ADAMSY ba
Kowa fatan alkairi yake masa.
Saboda kyautatawarsa ga al’uma
Ga qaninsa Salim d’in yana San d’an uwan nasa ADAMSY… dan baya nuna masa komai
Shiyake masa komai na rayuwa..
Dake shi Salim d’in kasuwanci ya karanta. Shiyasa ADAMSY ya barsa a supermarket d’in nasa…

Burin hajjiya Rukayyat ADAMSY ya mutu. Salim ya zama kamarsa.. Su gaje dukiyarsa..
Wannan dalilin yasa dataji zaije ya d’auko yaran marayu tayi tsalle ta dira tace bata amince ya ibi yaran marayu ya rainesu ba
Ganin hakan yasa mahaifinsa shima yace bai yarda ya d’aukosu ba.

Koda ADAMSY ya kalli mahaifiyarsa a lokacin nunamai tayi dole yabi umarninsu
Dan yasan bata da y’anci agidan
Kuma mahaifinsa yana da zafi.. Idan ya yanke hukunci akan abinda hajjiya Rukayyat tayanke shikenan ya zauna..
Wannan rayuwar da mahaifiyarsa takeyi agidan tana baqanta ran ADAMSY
Saidai ba yanda zaiyi. Amman zuciyarsa cike take da tsanar uwar gidan Dadyn nasa hajjiya Rukayyat

Sannan hajjiya Rukayyat bata san ADAMSY ya haihu  dan bokanta yace mata duk randa ADAMSY ya haihu toh aranar duk wani asirce asircen da takema mahaifin nasa aranar zai fara warwarewa... 
Ita kuma irin nata salan qaddarar asirce asircen nata kenan

Wannan shine labarin TAUDHAT da dangantakar dake tsakaninta da NUFAISAT. Da kuma d’an rayuwar ADAMSY dana d’auki muku….


Ba abinda Maman TAUDHAT ta iya cema TAUDHAT d’in sai tashi da tayi tabar mata falan…
Aiko wani matsiyacin tsaki TAUDHAT d’in taja wai adole ranta ya b’aci. (Allah ka shirya mana zuri’a Amiin)

Toilet ta shiga tayi wanka da fad’awa bed nata. tana tsaka yanda zatayi taja hankalin NUFAISAT suje wajen saban bokan nata
Duk ta k’osa tazama Matar ADAMSY
Itama yadinga damawa da ita cikin soyayyarsa

ADAMSY ko yana kaiwa gidansu duk da cewar dare ne Amman hakan bai hana ma’aikatan gidan rugowa da gudu suka zube agabansa suna masu kwasar gaisuwa ba..
Suna San ADAMSY kasancewar yana kyautata musu da basu kulawa…
Da Murmushi yake amsa gaisuwarsu ahaka har ya shige falan Dadynsa
Dake yau hajjiya Rukayyat ce da Dadyn nasa tare ya gansu suna hira..
Dan haka yana gama gaishesu saiya nemi daya tashi yaje shashin mahaifiyarsa….
Da sauri Dadyn nasa yace dashi… “Dakata ADAM.. Dama ina San magana dakai
Cikin ladabi ADAMSY ya koma ya zauna yana cewa.. “Ina jinka Dady
Jan numfashi Dadyn nasa yayi da cewa.. “Dama ina San.. ka ƙara Aure ne….
Cikin sauri da rikicewa tsakanin ADAMSY da hajjiya Rukayyat suka had’a baki wajen cewa.. “Aure????.. Suna masu kallansa
Da wani hali Dadyn ya maida kallansa ga hajjiya Rukayyat yace.. “Eh Aure..
Aure nakesan ya qara ko za’a samu rabo daga matar dazai Aura..
Yanxu fa shekarun auransa kusan Bakwai..
Ina San yara da yawa Rukayyat.. kinfi kowa sanin hakan
Daga shi sai d’an uwansa Salim nake dasu..
Hakan yasa nake kwad’ayin samun jikoki
Gaskiya ina san ganin jikokina nan kusa
Da wani hali hajjiya Rukayyat tace… “Amman Alhaji ai ADAM baiyi dad’ewar daza’ace ya ƙara Aure dan rashin haihuwa ba..
Murmushi Dadyn nasa yayi da cewa… “Haba Rukayyat. Kiyi aiki da hankali mana. Yaran nan ya haure shekaru talatin.. Idan bai haihu yanxu ba. Saiya tsufa kikesan ya haihu..
Gaskiya Ina San naga y’ay’ansa yanxu.. Nagansu kan cinyata suna jamun gemuna…. Ya ƙarashe furucin da Murmushi????
Aiko nan take ta murtuƙe fuska.. Ta nuna ƙarara bataji dad’in furucinsa ba..
Dan haka da ɓacin rai tace.. “Toni gaskiya ban amince ADAM ya ƙara Aure yanxu ba..
Dan haka aƙaramai wasu shekaru Idan anji shuru abarsa ya ƙara Auran
Shuru Dadyn nasa yayi.. Can yace. “Toh shikenan an qara masa lokacin. Allah ya dubesa ya basa nan kusa..
Da Murmushi tace.. “Amiin Amiin..????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button