LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai jami’an tsaran suka jinjina hassada da baqin hali irin na Ibrahim.
Sun buqaci daya gaya musu inda yaran suke. Way’anda yasa su kashe Adams d’in
Ya gaya musu inda suke. Amman anyi duban duniya suma ba’a gansu ba
Wannan yasa hankalin jami’an tsaran ya tashi dan Ibrahim ya tabbatar musu da cewar wallahi bayan inda ya gaya musu baisan inda kuma suke ba…

Ayanxu dai Ibrahim yana hannun jami’an tsaro dayi musu aiki me tsanani.. Dan sunce bazasu sakesa ba har sai ranar da akaga ADAMS. dan ba zama zasuyi ba zasu dinga nemansa ne har Allah yasa adace..

Ammin Adams tana cikin wani hali. Kullum tunaninta ADAMS ne
Ba dare babu rana rokwan Allah take kan ya fito mata da d’anta cike da lafiya..

Haka NUFAISAT itama tunaninta ADAMS d’in ne kuka take cikin dare tana rokwan Allah ya bayyana mata mijinta..

TAUDHAT mah tana cikin damuwa dan har tafara tunanin yanxu idan ba’aga ADAMS ba. Ya zatayi wajen rayuwa da wani namijin..

Yusuf ma ba’a barshi abaya ba. Dan kullum addu’a yakema Adams babu dare babu ranah. Haka indai zai fita saiyaje gurare da dama wai kozaiga Adams d’in..

Dady kam jiki babu sauqi dan likita yace saiya cire damuwar Adams aransa sannan zai samu lafiya..

Lokaci na tafiya amman har yanxu shuru kakeji babu labarin Adams.
Yau kusan watanni tara kenan babu amo babu labari…
TAUDHAT da NUFAISAT sunsa aransu bazasu tab’a barin Auran Adams ba suna nan suna jiran dawowarsa dan sunji aransu da gaske bai mutu ba….

Wannan kenan me karatu????????‍♀

Kuci gaba da bibiyata ni Rahma Nalele ina tare daku y’an hannuna????????????????????????.. Jiya naso turo muku Allah bai yarda ba

[7/11, 2:55 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 19☆

Sannan way’anda sukama ADAMS dukan nan suna nan cikin garin Kaduna suna jinyar kansu cikin b’oyayyan guri…
Dan nagaya muku shima Adams bawai kallansu kawai ya tsaya yi ba. Yayi musu b’ar me yawa. Dan dai kawai suna jin tsoran karsu kasheshi ne ogansu yad’au hukunci akansu banda haka da tun fara artabun nasu zasu sakar mai bindiga.
Dan duk da suna tare makamai ahannunsu sanda ya nuna masu iyakarsu.
Ya fasama d’aya daga cikinsu gefan ido d’aya Wanda nake kyautata zatun yama rasa idan..
Haka ya karya wani ma acinya.
Yama wani duka a gabansa. Inda kunsan da wiya mutum yake tsallake duka awannan waje batare daya shiga ukunsa ba.
Sannan ya kaima Wanda ya kashe Sunusi mugun bugu a hanci Wanda nan take kamanninsa suka canja. Dan hancin ya samu mugun rauni. Ga baki hak’ura sun zube..
Wannan tunda yayi masa haka yar iyanxu kansa yaqi dawowa daidai..
Ogansu yayi mamakin hakan sosai. Dan bai tab’a kawowa masu jin dad’in rayuwa suna tare da qarfi haka

Wannan kenan me karatu


Rugar malam jauro wata hatsabibiyar ruga ce da take nan cikin d’aya daga qauyukan garin gwambe. Saidai tayi daji da yawa kasancewar malam jauro yana da arziqin shanu masu yawan gaske..
Wannan dalilin yasa mutane suke zagawa suke mai sata san ransu. Lokacin daya ankare da hakan shine yayi wani abu Wanda duk Wanda ya shigo rugarsa da niyar sata to ba makawa mutuwa zaiyi..
Abin da yayi yana amfani da haline da abinda kazoyi.
Wannan yasa jama’a da dama suke ganin rugar ba wajen zuwa bace saboda yanda suke ganin kawarwaken mutane da sun shiga wajen.. Duk Wanda ko sukaga yaje rugar lafiya ya fitto lafiya cewa suke akwai abinda ya taka..

Babbar Ruga ce sosai danta tara ainiyin fulani masu wayan gaske.
Way’anda basu san hayaniya. Dan kallo d’aya zaka musu ka kirasu da fulanin daji.
Basu san komai na rayuwa ba sai kiwo…
Saidai sun bambanta da jahilan mutane saboda malam jauro shahararran malami ne.
Yana da sani akan ilimi na addinin musulinci.
Wannan yasa duk inda suka fito idan zasu aiwatar da al’amuransu gabanka bazaka kirasu da jahilal ba.
Dan sunsan ilimi na addinin musulinci
Malam jauro ya koyar dasu Qur’ani me girma su fiqhu ahalari qawaqidi da sauran littattafai na addina..

Bayan wannan basu da sani akan komai sai kiwo..

Gwaggwa Yawo wacce suke kira da Yawo tana d’aya daga cikin mutanan da suke zama cikin wannan Ruga..
Saidai ba’a wajen ainihi tayi rayuwa ba aa zama ne dai ya kawo ta cikin dajin ita da d’anta Musa..

Dan ita asalinsu y’an qauyen Jos ne BASA.

Yawo yaranta biyu ne aduniya. Rahma da Musa qaninta..
Mahaifinsu ya mutu ne bayan sati uku da Aurar da Rahma da yayi ga wani d’an garin Kano. Wanda bai sanshi ba haka kawai dan ya ganta yace yana Santa Sai kawai ya bashi ita wai ya yaba da hankalinsa..
Dan kawai ya d’auki wata d’aya yana zuwa tad’i wajenta.. Dake kunsan Bafulatan mutum dasan kud’i nan take shiko saurayin ya dinga masa kyauta kala kala. Hakan yasa yace wai yayarda da hankalinsa. Amman ya masa alqawari idan ya aura masa y’arsa Rahma zai dinga zuwa duk wata biyu yana kawo musu ita suna ganinta..
Shiko saurayi yayarda da hakan.
Ita dai yawo hankalinta bai wani kwanta ba. Gani take saurayin d’an yankan kaine. Yana aure mata y’a zai yanke mata kai.
Dan haka tanuna ita bata amince da auran ba. Shi kuma mijin nata yace ya amince. Haka tanaji tana gani ya d’aura ma Rahma aure da wannan saurayi ya kuma saka Rahman gaban motar saurayin yace tama mijinta biyayya dan yayarda dashi????????????
Yowa tafi kwana uku tana kukan rabuwa da Rahma
Lamarin d’aurin Auran ya faru da kwana uku tayi mafarkin saurayin ya yanka mata y’a..
Aiko wayewar wannan safiya data tashi ba abinda take Sai kuka..
Shiko mijin nata ce mata yayi Dan tasa hakan aranta ne shiyasa tayi mafarkin hakan..
Jinsa kawai tayi Amman tasa aranta da gaske sirikin nasu ya kashe mata Y’a…
Tana cikin jimamamin hakan ne kuma da sati biyu mijin nata ya rasu..
Wannan yasa tsoro ya kama zuciyarta..
Ana yin Arba’in d’in rasuwan mijin nata sai tace da Musa ya saida shanunsu kaf zasu tashi daga basa nan qauyen Jos su koma qauyen yola ko gwambe..
Haka musa ya yarda da zancenta ya sayar dasu kamar yanda ta buqata shine fa basu zame ako ina ba sai’a garin gwambe
Ahankali suka fara gane kan garin. Kasancewar Yawo tafi san zaman daji saita dinga neman sani akan dajikan da suke qauyen gwambe. Anan taji ta gamsu tayarda da zama a Rugar malam jauro..
Sai Musa yasai musu shanu agun Malam Jauro ya fara ciwansu. Aiko cikin iko na Allah nan shanun nan suka dinga haihaifafa ya tarasu da yawan gaske.
Anan yaga wata wacce yake so ya Aura sunanta Hasiya.. Hasiya macece me hankali da nutsuwa tunda Musu ya furta mata yana santa da aure taji tana sanshi da qaunarsa..
Hasiya y’a d’ayace agun iyayenta. Wanda makwaftan junane su dasu Musan
Suma iyayenta basu da wasu danji dan suma zuwa rugar sukayi kamar yanda su Yawo d’in sukazo..
Sun yarda da auran Musa da Hasiya iyayenta nan aka d’aura musu aure.
Saidai watansu takwas da auran Musa ya rasu ya bar Hasiya da ciki..
Anan hankalin Yawo ya tashi matuqa dan dama su biyu gareta. Gashi bata san inda Rahma take ba. Da gaske saurayin nan ya kasheta kobai kasheta ba oho..???? Shid’in kuma da take kallansa taji dad’i Gashi ya tafi..
Wannan dalilin yasa tad’auki san duniya ta d’ora akan cikin da Hasiya take dashi…
Hasiya na tashi haihuwa tahaifi mace santaleliya me kama da ita sak.
Saidai ita baqa ce. Irin baqin nan da bature ke cewa black beauty..
Kallo d’aya zaka mata kasan kayi gamo da baqar bafulatana..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button