LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Gashi Mahaifiyarta fara mahaifinta fari danginta farare amman ita tazo baqa..

Ranar suna yarinya taci suna Faɗima.
Dake malam jauro ne ya rad’a mata sunan haka kawai yaji yana qaunar yarinyar. Dan yarinya ce me shiga rai tun zuwanta duniya haka mutanan wajen suke tururuwa wajen san ganinta.
Dan da wiya kamata kallan farko bakaji tashiga ranka ba..
Hakan yasa Malam Jauro yake kiranta da Musulma.. Shine Yawo take kiranta da MUSLEEMA.

San duniyar nan haka Yawo da mahaifan Hasiya suka d’auka suke nunama MUSLEEMA

Kaf cikin Rugar nan babu black beauty Sai MUSLEEMA
Hakan yasa kowa yasan da zaman MUSLEEMA awannan Ruga..

Ayanxu shekarunta goma sha biyu.
Kuma a qa’idar Rugar malam jauro yara y’an mata suna kaiwa shekaru goma sha uku ake Aurar dasu..

Wani d’an malam jauro ne yake san MUSLEEMA. Ayanxu haka har an saka musu ranah..

MUSLEEMA yarinyace me sanyi haka. Tana da d’an surutu tsiwa idan tasanka kuka saba..
Tana da manyan ido shanyayyu irin na me jin bacci d’innan. Ga dinful d’inta me sata kyau idan tayi murmushi ko dariya. Ga jiki na d’aukar hankali..
Zara zaran yatsunta abin kallo ne. Sannan tana da Gashi me tsawo me santsi da sheqi irin na ainiyin fulani.
Alamu sun nuna MUSLEEMA bazatayi irin wannan tsawan nan me yawa ba. sannan bazatayi qajarta irin me munin nan ba
Sannan baza’a kirata siririya ba. Haka baza’ace mata lukuta ba.
Idan me karatu yana san ya hango yanda jikin MUSLEEMA yake. Toh yayi amfani da jikin wannan jurumar Y’ar film d’in wasan hausan nan wato MARYAM BOOTH…
Abu uku kawai MUSLEEMA zata nunama Maryam booth shine tafita mazaunu HP. Zata fita breast idan taqara girma. Haka kaza lika zata fita diri na jiki na d’aukar hankali idan taqara girma still..
Sannan ita bata da hanci can. Hacinta gajere ne????
Sam idan Mazaje masu san mata kyawawa sukaci garo da MUSLEEMA baza su d’auketa ba. Dan ko kusa baza su sata a sawun mata masu kyau ba..
Cewa zasuyi gata baqa gata da gajeran hanci sam bazasu kirata da kyakkyawar mace ba

Amman ga mutumin dayasan ailihin kyau ga y’a mace yana ganin MUSLEEMA zaiyi gudu dan saceta ya b’oyeta inda babu Wanda zaina kallanta bare ya gane masa sirrin dake tare da ita..

Mahaifiyarta tayi wani aure saidai itama bata wani dad’e ba tarasu dan haihuwanta d’aya cikin rashin sani tana jan ruwa a rijiya tana magana santsi ya kwasheta tafad’i Sai jinta akayi acikin rijiyar tafad’a tsumdum. Tayi mutuwar shahada Dan ba’a kaiga I cirota ba tace ga garinku nan…
Iya tashin hankali iyayanta da Yawo sun shiga. Dan Hasiya mutum ce..
Haka iyayenta suka roqi alfarma kan iyayen mijinta subar musu d’an data bari Suleiman..
Dake mijin yayarda haka suma suka yarda…

Shine fa ya kasance Yawo take riqe da MUSLEEMA su Kuma iyayan Hasiya suka riqe da Suleiman..

Wannan shine labarin MUSLEEMA da yanda tazo duniya…


Abinda ya faru awashe garin ranar da Y’an iskan nan sukama ADAMS wannan duka suka yadashi Rugar malam Jauro shine..
Ita dai MUSLEEMA bayan tayi sallar asuba makarantar malam jauro ta nufa kamar yanda tasaba. Yana karantar dasu karatun bayan sallar asuba zuwa qarfe takwas na safe..
Qawarta Aisha ce me biyo mata to jiya a gidan kusa dana malam jauro ta kwana gidan yayarta data haihu..
Hakan yasa take tafe ita kad’ai yau..

Taga Adams akwance Sai tsoro ya hanata kulawa dashi..

Dake makarantar tana da d’an nisa da gidansu haka ta dinga tafiya tana waige dan ganin Adams ya tsaya mata arai..
Duk da ba ganin fuskarsa tayi ba.. Amman ya tsaya mata arai matuqa

Har aka tashi daga makarantar hankalin MUSLEEMA nakan ADAMS..
Dama malam jauro na lura da ita Dan haka da’aka tashi saiya kirata yana tambayarta me yake damunta ne yau. Yaga kamar hankalinta baya kan karatu..
Cikin nutsuwa ta gayamai taga wani mutum ne a can kusa da gidansu. Kuma da alama mutuwa yayi..

Murmushi malam jauro yayi Dan tunaninsa ko masu zuwayi masa sata ne sukazo rai yayi halinsa..
Dan haka saiya kira liman da yaransa biyu ciki harda Wanda zai Auri MUSLEEMAN yace suzo akwai wani Wanda ya mace can kusa da gidansu MUSLEEMA..

Aiko cikin sauri suka rangad’o zuwa ganin wanene kuma wannan..
MUSLEEMA tana gaba suna binta a baya har takaisu inda taga ADAMS.
Aiko yana nan kamar yanda ta gansa…

Hankalin me gari da liman yayi matuqar tashi ganin Adams haka. Sun gane mugun duka aka masa Wanda duk Wany’anda suka masa wannan duka sun ilmantu da dukan mutane a inda suke da tabbacin zai zamame mutum illa arayuwa..
Duk wani gu Wanda ido yake tsoran a tab’a mai ajiki Sanda suka tab’amai

Malam jauro yaga sab’anin abinda yake tunani..
Nan take tausayin ADAMS ya kamashi yace maza su kinkimesa su kaishi gida.
Wajen d’aukar nasa ne liman yake tabbatarma da malam jauro karaya bakwai ce a jikin ADAMS.
Malam jauro yaqara jinjina wannan rashin tausayi irin na mutane..

MUSLEEMA ko tunda taga fuskar ADAMS hankalinta ya tashi. Tausayinsa ya cika zuciyarta.. Nan take tafara kuka tana me qarajin tausayinsa aranta.
Daqar malam jauro da liman suka iya shawo kan kukan nata tatafi gida.
Sun tabbatar da lalle yarinyar me tausayi ce..

Da kuka tashiga gidan nasu lokacin Yawo na dama kokon safe..
Aiko da sauri tatashi ta tareta tana tambayarta… “Meya faru dake yanxu kuma da sassafe.
“Wani mutum nagani kusa da gidanmu d’azu zani makaranta. Shine da aka tashi malam dasu Iro da liman suka biyoni na nuna musu shi. Yawo bakiga yanda akamai duka ba. Wasu ne suka jimai ciwo sosai ajikinsa. koma ya mutu ne oho

Shuru Yawo tayi dan tayi tunanin ko masu zuwa yima malam jauro d’in sata ne. Amman dataji batun duka Sai tunaninta ya canja..
“Kinga ba komai zauna kiyi kalacen ki.
“Ni bazan iya cin komai ba. “Toh yanxu me kika san ayi. “Nidai kizo muje gidan malam kiga mutumin kinga saimu dinga zuwa dubasa ko☹
“Ohni Yawo.???? zamuje amman Sai munyi kalace..
Jin hakan yasa MUSLEEMA d’auko tabarma ta shinfid’a a tsakar gidan nasu wanda yasa sumunti ta d’auko kokon nasu da kosai suka zauna ita da Yawon suka cika cikinsu..

A al’adar MUSLEEMA idan tawowa daga makaranta bayan taci abinci shara takeyi da wanke wanke saitayi wanka saita zaga wajen ciwansu ta duba lafiyar dabbobin da taga zata iya dubawa. Idan da matsala tazo ta gayama Yawo idan babu matsala haka zata zauna cikinsu tana me kula dasu na lokaci me tsawo. Sallah ce take tadata. Idan tayi takan fitta su had’u da qawarta Aisha suta wasansu da hirace hiracensu..
Toh yau ko sharan da wanke wanken batayi ba tatashi ta azalzalama Yawo wai saidai tatashi suje gidan malam taga wannan mutumin…
Yawo tace bazata ba saitayi mata wanke wanke da shara tukunna
Haka MUSLEEMA tayi tana turo baki. Wai adole ranta ya b’aci…
Tana gamako suka kullo gidan da nufar gidan malam jauro.

Kallo d’aya Yawo tama Adams gabanta yayanke ya fad’i.. Hankalinta kuma ya tashi.. Saboda ganin da tayi yayi mata kama da y’arta Rahma.
Ga irin idansa nan irin na Rahma ne. Irin na MUSLEEMA.
Ga hancinsa mah irin na Rahma Y’arta ne..
A dibibice ta kalli malam jauro tace… “Malam a ina Kaga wannan bawan Allahn..
” aa MUSLEEMA bata gaya miki bane. Ai itace taban labarin yanda tagansa.
“Eh nima taban labarin na dai d’auka ko a kid’ime take ne.
“aa gaskiyar kenan tagaya miki… “Ammako ko suwaye ne suka mishi haka suncika azzalimai.
“Wallahi yanxu ni da liman zancen da muke kenan. Ko daga ina yake. Wayaxo ya yayada shi Allahu ya’alamu.
Amman nasa su Iro suje kewayenmu su bincika ko wani nasu ya b’ace. Dan ga wani cikin rugata yana jin jiki..
“Eh hakan yayi. Allah yasa anan kusa yake..
“Amiin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button