LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Shuru kowa yayi ba abinda kakeji sai tashin kukanta.
Ahankali malam jauro ya kalli Iro yace.. “Kai jeka ka kiramin Ahmad..
Yawo tace.. “Daka fitta daga harkarta malam yarinyar nan bata da kai..
Murmushi yayi mata da cewa.. “Bazan d’aura mata aure da Wanda bata so ba. Dan tunda tazo duniya nake qaunarta kamar yanda nake qaunar y’ay’ana..
Jin abinda yace sai yasa hankalin Yawo kwanciya dan dama ita har ga Allah bata san Auran Iro da MUSLEEMA. Saboda Iro halinsa ya bambanta da sauran yaran malam jauro d’in… Shiyasa dawowar ADAMS gidanta sai taji tana San ya Auri MUSLEEMA. Saboda nutsuwarsa da kamewarsa..

Iro ko ransa ne yayi matuqar b’aci hankalinsa ya tashi matuqa. Gani yake in ba MUSLEEMA bazai iya rayuwa ba..
Haka da b’acin rai yaje ga Adams wanda yake wajen ciwo da qur’@ni a hannunsa yana tulawa yace dashi. “Kar kayi qoqarin ruguzamin rayuwata. Dan wallahi kayi min haka saina b’atar dakai duk daran dad’ewa. Sannan wai kaje Mahaifina nasan ganinka yanxu
Yana fad’in hakan ya juya abinsa ya tafi. Da kallan mamaki ADAMS ya bishi. Me kenan yake nufi da way’annan kalmomin nasa…
Tab’e baki yayi da tashi dan zuwa amsa kiran…

Yana zuwa yaga MUSLEEMAT na kuka sosai..
Ai baisan sanda yayi jifa da sandarsa gefe ba yaje gareta da kama hannunta yana goge nata hawaye fad’i yake.. “Waya tab’amin ke. Waya tab’amin qanwata. Meya sameki..
Ahankali cikin shagwab’a tace mai “Wallahi YAYA nikai nake so. Dakai nake san k’are rayuwata. Dan Allah karka bari a d’aura min aure da Iro nagaya musu gaskiya nikai nake so..
Shuru ADAMS yayi da sakin hannunta ya qarasa kusa da Malam jauro wanda yasaki baki yana kallansu yace.. “Gani Baba Iro yace min kana san ganina..
Jan numfashi Malam jauro yayi da cewa. “Eh haka ne. Dama ina san naji kaima kana san MUSLEEMA ne.
Kallansa Adams yayi da murmushi yace.. “Kayi hakuri Baba. A duk duniya bani da abin so kamarta. Ina san MUSLEEMA kiye da komai arayuwata.. Saidai karka daka ta shirmanta. Kaga ita yarinya ce. Ka duba Iro ka Aura mata shi. Dan shine ya dace da ita. Musamman idan kukayi duba da yanda naji mutane na fad’i cikin Rugar nan na wai ni ba’asan ko wanene ba. Bai dace ka duba zancenta ba. Ya dace ka bata wanda kasani ina ganin hakan shi zaifi alkairi..
Jan numfashi Malam jauro yayi cikin matuqar jin qaunar ADAMS d’in aransa. Yayi imani ko daga ina Adams ya fito shid’in ba mugun mutum bane. Kuma zai kasance d’an dangi ne. Haka zai kasance nutsattse ne..
Yana jin qaunar MUSLEEMA aransa kamar shine ya haifeta. Dan haka bazai tursasa Zuciyarta kan lalle saitayi rayuwa da d’ansa Iro dan san zuciya ba.
Dan haka cikin taushash shiyar murya irin tasu ta manya yace dashi. “Naji abinda nake sanji daga gareka. Kuma MUSLEEMA bata da wani miji bayan kai. Indai kakarta Yawo ta amince..
Da sauri Yawo tace.. “Ni kam duk yanda kayanke shawara kan auran MUSLEEMA na amince…

“Toh shi kenan. Zan d’aura mata aure da Ahmad ran jumma’an nan.
Sannan zan turo masu gini suzo su kewaye d’akin Ahmad d’in da fitar musu da bayan gida dan susamu inda zasu zauna. Dan nasan bazaki so suyi nisa dake ba.
Da murmushi Yawo tace “hakan yayi malam mungode Allah ya saka..
“Ba komai Allah shige mana gaba. Shi kuma Allah ya dawo mai da tunaninsa nan kusa
Liman yace “amiin.. Yanxu kai Iro sai kayi hakuri ko…
Murmushin yaqe Iro yayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo yace. “Ba komai Babba.
Haka sukayi addu’a suka tafi zuciyar Iro na gaya masa mezaima Adams wanda zaisa ya hucce kwacen matar da yayi masa.. Yayi alqawari saiya baqanta rayuwarsa. Ayi Auran komai daran dad’ewa saiyayi masa illah….

Na gaida y’an hannuna????????????????????????
[7/14, 1:49 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 20☆

Bayan su Adams sun koma gida Yawo barinsu tayi a tsakar gidan nasu ta shige kicin dan kama aiki.
ADAMS ya kalli MUSLEEMA cikin tsokana yace. “Wallahi YAYA ni kai nake so. Dakai kad’ai nake san k’are rayuwata..
Murmushi MUSLEEMA tayi da galla mishi hararar wasa.
Shima murmushi Yayi daciba da cewa. Toh nima wallahi qanwata nake so. Kuma ke kad’ai nake san qarashe rayuwata.
“Toh dan Allah yaya karka barni. Duk wiya duk matsi duk tashin hankali kada ka gujemin.
“Ko’a mafarki bazan tab’a iya guje miki ba. Bare azahiri ina ganinki ido da ido na gujemiki. Bazan iya hakan ba. Dan nasan idan na aikata hakan na aikata babban zunubi.. Saboda na gujema tauraruwa me haskake hasken taurari…
Ba qaramin jin dad’in furucinsa MUSLEEMA tayi ba hakan yasa ta rungumesa tana cewa. Zan girka maka abinci me dad’in gaske anjima.
Shafa kanta yayi dabata amsa.. “Tona gode qanwata ki kula min da kanki sosai dan bani san naji ance wuta ta qona min ke..
“Zan kiyaye YAYANA..
“Yauwa qanwata bara naje dan nabar shanunmu can cikin daji.
Janye jikinta tayi daga nasa tana sakar mai murmushi. Shima murmushin ya sakar mata kana ya ficce daga gidan..

Aranar malam jauro ya aiko da masu gyara suke kewayema Adams da MUSLEEMA inda zasu zauna

Itama Yawo daga ranar tafara damama MUSLEEMA wata gamba da madarar shanu tana bata tana sha.
Sannan dama ita MUSLEEMA ba’abinda tafi so kamar shan madarar shanu farar tasa wacce ba’a dafa ba.
Babban sirri ne ga Y’a mace tadinga sha dan yana wanke mara da sakama mace wata ni’ima me tsayawa aran miji. sannan ko baki shan maganin mata ked’in tada bance acikin matan…
Sannan tana bata rubutun suratul Yusuf wacce ake wankewa da ruwan kankana..
Haka akwai wasu suna darai na sirrin bafulatanin mutum wanda shima duk sanda ta bata..

Sannan ana sauran kwana biyu d’aurin Aure ta siyar da Saniya biyu tasiya musu gado da katifa harda ladar d’aki da abubuwan buqata.

Yau takasance ranar jumma’a kuma an d’aura auran ADAMS wanda suke kira da Ahmad shi da MUSLEEMA..

Jama’ar rugar sai qananun maganganu suke akan yanda Yawo ta amince taba ADAMS Auran jikarta tilo d’aya bayan ba’asan daga inda ya fitto ba. Ai yanxu kai ya waye andena irin wannan kwad’an…
Tajisu Amman ta toshe kunnnata dan ita alkairin hakan kawai take hangowa bata hango wani sharri ko faruwar wata matsala..

Da misalin qarfe takwas da rabi Yawo takira Adams ta danqa masa amanar MUSLEEMA tace.. “Gata nan qanwarka ce ka riqeta amana kamar yanda na baka ita amana..
“Insha allah Yawo bazaki tab’a nadama da bani ita da kikayi ba.
“Masha Allah. Saiku tashi kuyi shashin naku.
Haka suka tashi sukayi shashin nasu wanda ya kasance ciki ne da falo sai d’an fili idan suka fitto daga falan nasu. Bayangida kuma dama had’e yake dana Yawo..
Haka Adams yace da MUSLEEMA taje tayo alwala suyi sallah..
Aiko nan tatashi ba musu dan dama ita bata mishi musu akan komai. Bare kuma yanxu da Yawo taja kunnanta sosai akan hakan..
Bayan tadawo nan suka gabatar da sallah raka’a biyu Adams yace da ita.. “Qanwata kin fara wannan al’adar ne irin ta mata.
Sunkuyar da kanta qasa tayi batare da tabasa amsa ba.
Sanda ya qara maimaita mata tambayar sannan cikin jin kunya tace dashi.. “Na fara wancan watan.
“Toh gayamin kwana nawa kikayi ya d’auke miki. Tace kwana hud’u.. Yace “Yaya kika aiwatar da wankan… Kallansa tayi da sauri.. Yako gyad’a mata kai alamar yana san sani.
Tunani tashiga yi Ashe dama yaya Ahmad d’an iska ne..
Kamar yasan tunanin da takeyi yaci gaba da cewa. Qanwata karfa zuciyarki tagaya miki cewa ni d’an iska ne. aa haka aure yake dole ki gayamin yanda kike aiwatar da ibadarki dan nasani nasan daidai kikeyi koko akwai matsala.
Jin hakan yasata sakewa tagaya masa kanta a sunkuye.
Yaji dad’in yanda ta’iya dai dai da yanda ake so dan haka saiya qara mata tambaya akan yanda take ibadunta. Namma bata bashi kunya ba tagaya masa.
Nanya kama kanta yayi mata addu’o’eh. Kana ya jawota jikinsa ya shiga bata kazar da Aliyu abokinsa ya gasa masa da madarar shunu me d’umi da Yawo tabashi….
MUSLEEMA kad’an ta rage. Hakama madarar. Dama shi ba wata yunwa yake jiba. Hakan yaci sauran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button