LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Kankace me???? nan gidan Yawo yacika maqel da y’an barka….
Kowa fad’in albarkacin bakinsa yake kan yanda yaran sukaxo dakyau..
Sun had’une iyakar had’uwa. Saikace yaran larabawa..
Anan wasu yaran suka ruga daji da gudu suka gayama ADAMS MUSLEEMA ta haihu ta haifo y’an uku????????????????????
Da mamaki ADAMS ya nufi gidan nasu cikin sauri yana atunanin anya kuwa zancen da yaran suka gayamai gaskiya ne..
Aiko ya tabbatar. Jiyayi kamar yasa ransa ame dan Farin ciki.
Yawo ta kalli ADAMS tace.. “Kaga ikwan Allah ko. Dama na gaya muku kudena biyema y’an asibitin nan wajen haihuwa. A kwai sinadarai namu na gargajiya irinsu ganyayyaki itacuwa ingantattu da muke zuwa daji muke iboma me ciki take sha.
haka zakaga ta haihu sumul da ita. Bata tare da wani ciwo ko kad’an.. Yaranta suzo duniya jikinsu luwai luwai gwanin ban sha’awa dashi.
Murmushi ADAMS yayi baice mata komai ba. Dan yasan Yawo wajen musu idan akan ciki ne. Shi kuma gani yake kamar ya dace idan Mace nada ciki taje doctors su dubata. Saidai yanxu ya qara tabbatarwa Allah ne kawai me karewa.
Har kwana hud’u da haihuwan amma sam yaran basu da kuka basu da wani matsala.
Sai shan nonon uwarsu suke me gard’i da lafiya. Saboda sinadaran da Yawo take bata dan qarama nonon inganci..
Ranar suna raguna uku da shunuwa d’aya aka yankama yaran.
Yawo tace idan bamma Y’ay’an MUSLEEMA ba banga y’ay’an wanda zamma ba.
Dan haka ko d’ari ne ayanka dabbobin arziqinsu ne.
Jin hakan yasa ADAMS murmushi yace mata aa raguna uku shanuwa d’aya sun isa..
Tace to badamuwa.
Y’an tattun suna aka sama yaran kamar… Musu da Aliyu sai qaramarsu Rahma…
Wannan suna ya tara mutane ba d’an kad’an ba.
Saboda bajintar da Yawo tayi asunan bad’an kad’an bane.
Haka shima Adams ana saura kwana biyu suna sanda ya saida saniyarsa irin way’anda Yawo take basa yaba usman kud’in yace dan Allah yaba matarsa tashiga kasuwa takwaso masa rugunan yara da atamfofi masu kyau irin na mejego..
Wannan yasa sunan MUSLEEMA ya zarce dukkan wani sunan yara da akeyi a rugar..
Sunan dai kam ya zama sunan kwatance…
Dan kowa yaci shinkafa da nama san ransa.
Wannan shine kawai abinda akayi asunan kuma ya qayatar ya gamsar da al’umar rugar…
Matar Usman kasance warta doctor itama kamar mijinta data zo sunan sanda takeb’ance da MUSLEEMA ta duba gabanta tatabbatar bata samu qari ba sannan hankalinta ya kwanta..
Saidai tayi mamakin yanda bataje asibiti ko sau d’aya ba Amma cikinta ya rayu da lafiya. Gashi itama da lafiya ga yaranta gwanin ban sha’awa.
Duk da haka sanda tabama yaran kulawa irin tasu ta likitoci.
San duniyar nan haka ADAMS ya d’auka ya d’ora kan MUSLEEMA da yaranta..
Yara suna rayuwarsu rayuwa me inganci.
Usman da matarsa yaran sun shiga ransu hakan yasa suke zuwa suke ba yaran kulawa irin tasu ta likitoci acewarsu bai dace su zauna haka ba kulawar likitoci ba…
Ayanxu shekarar yaran biyu da wata d’aya..
Yaran sun taso gwanin ban sha’awa abinsu.
Ga surutu ga wayo..
Idan kagansu Sai kace sunkai shekara uku.
Saboda girmansu da lafiyar da suke tare da ita….
Da kanta MUSLEEMA take kaisu wajen malam jauro d’aukar karatun Alqur’ani me girma.
Zanso gaji yanda suke d’auke komai akansu idan an biya musu..
Yau take Asabar tun safe
MUSLEEMA taji gabanta na fad’uwa haka kawai..
ADAMS na lura da canjin yanayinta dan haka bayan sun idar da karyawa ya kalleta da cewa.. “Na lura yau tunda kika tashi baki da kuzari..
Jan numfashi tayi da kallansa shima tace.. “Eh wallahi. Haka kawai naji gabana na fad’uwa kamar zan rasa wani abu me mahimmanci arayuwata.
“Niko kinga bani jin komai. Dan haka kishare dan ba mamaki ko alkairi ne yake san zuwa gareki.
Murmushi Yawo tayi da cewa.. “Eh nima fa haka nake ji araina haka kamar wani abu zai faru damu..
“Haba Yawo kema da tsufanki zakina fad’in hakan danki tsurar min da mata. Kunga nima fa shuru nayi. Dan Wallahi yanda kukeji haka nima nakeji..
Da marairaicewa cikin shagwab’a MUSLEEMA tace.. “Bana san nayi rashin koma wane irin abu ne haka arayuwata.
Dan Allah mijina katayani da addu’a.
Kama hannunta yayi cikin so da qauna yace. “Baki da matsala da hakan matata.
Fatana yanxu ki kwantar da hankalinki dan ba abinda zaki rasa..
Murmushi kawai tasakar mai.
Yawo ta girgiza kai. Tana tuna wane irin so ADAMS yakema MUSLEEMA ne..
Ahankali tatashi daqer tabar musu wajen. Saboda ciwan da yake damunta na duk jiki. Wanda yake haka ga kowane mutum idan ya d’auko hanyar tsufa.
Ganin hakan yasa ADAMS jan matarsa d’aki dama yaran nasu suna makarantar malam jauro..
Acan uwar d’aga ya ritsata yana cewa.. “Ban tab’a jin muguwar sha’awa irin tayau ba..
Kallansa dayi da muradi tace.. “Nima haka YAYANA..
Sun faranta ran juna kamar bazasu bar juna ba.
Tana qirjinsa yake cewa.. “Maganar gaskiya qanwata ina jin wani iri araina yau kamar yanda kika fad’a d’azu.
Kallansa tayi da Qara shige masa tana me fad’in. “Nidai koma dai miye Allah kabarni da mijina da yarana da kuma kakata..
Shafata yahau yi da yana amsa mata da “amiin..
Lokacin da suka fitto Yawo bata nan da alama ta fitta ne..
Suna jin dad’in yanda suke wanka a tare.
Kuma sun lura kamar idan suka keb’e da juna da ranah Yawo shiga makwafta take..
Hakan ne yake basu damar yin wankan tare da ranar ma
Da gaske Yawo bar musu gidan take..
Saboda tana jin kukan MUSLEEMA idan suka keb’e da juna.
Ta tabbatar ADAMS ya gama samun MUSLEEMAN ne shiyasa koyaushe cikin yimai ihu take.. Ba dare ba ranah..
Toh abin naba Yawo kunya???? shiyasa take barin musu gidan. Gwara da daddare tayi bacci wani lokacin bata jinta. Dan idan kaji tajita da daddaran to dama ciwan qafarta ne ya dameta ya hanata bacci shiyasa take jinta. Allah yasa yaran a d’akin Yawon suke kwana ba’a d’akinsu ADAMS d’in ba. Dan inda ace a d’akin su Adams d’in suke kwana ba makawa tashinsu MUSLEEMA zata dingayi da ihun nata idan abin ya ciyota.????
Shiko ADAMS tun abin nata na bashi kunya kar Yawo tajiyota har ya cire kunyar ya ajeta gefe tunda ya fuskanci kamar halittartace haka.????
Ga ita MUSLEEMAN ko
bata san Ashe Yawo tana jin kukanta da ihunta haka ba. Shiyasa bata tab’a tunanin denawa ba.
Haka suka saka ruwa sukayi wankansu. Wannan ranah duk jikinsu a sanyaye yake. Haka ADAMS ya shafi gefan faskar MUSLEEMA yace.. “Bara naje wajen shanu na duba lafiyarsu na dawo ko.
Kallansa tayi cikin so da qauna tace.. “Ka kula da kanka YAYANA karka bari wani abu yasamar min kai.
“Zan kula miki da kaina qanwata fatan kema kijimin da kanki.
Ahankali tamatsa jikinsa tasakar mai kisa a baki tace.. “Zan kula ma da kaina..
“Kinyi alqawari..
“Nayi maka mijina..
Qara shafar fuskarta yayi da sakar mata murmushi ya fitto daga d’akin..
Yazo zai fitta waje kenan sukaci karo da Yawo. Tace. “Har kafito zaka daji ne.
“Eh amman ina jin yanxu zan dawo dan ina jin kamar zazzab’i ne yake san kamani.
“Toh kadawo kawai ka kwanta mana. Idan kaji dama dama ka fitta anjima…..
Kan ADAMS yayi mata magana saigasu Khalit da Khalil da Rahma sunshigo (dake haka ake kiransu. Wannan ma malam jauro ne yake kirasu da hakan. Wato Musa shine Khalit. Aliyu Kuma Khalil. Shekenan sai Yawo tafara kiransu da hakan shine ya bisu dan Rahma ita ba’a mata wani inkiya ba.)
Wata Rabi ce a makwaftansu take dawowa dasu idan MUSLEEMA takaisu.