LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Da Farin ciki sosai ADAMS yake d’aukarsu. Idan ya sauke Wannan saiya d’auki wancan.
Suko sai murna suke dan baqaramin San uban nasu suke ba..
Sanda ya koma gidan ya zaunar dasu sannan yama Yawo sallama yana cewa gwara yaje dai ya duba tabbobin yaga ya suke idan yaso ya dawo ya kwantar…. Jin hakan yasa tamai fatan dawowa lafiya….
Saidai ADAMS baiyi nisa a tafiyarsa ba Iro da wasu abokansa uku suka taresa wai yaje inji malam jauro..
Har ADAMS yayi haryar gidan Malam jauro d’in sai Iron ya dakatar dashi wajen cewa ai baya gida kadaixo muje daji acan yake yaje sassaq’o wani magani ne.
Jin hakan yasa ADAMS binsu da zuciya d’aya
Sai tafiya suke cikin daji can Adams yace “Wai har ina malam d’in yake ne.
Shuru sukamai. Ganin hakan saiyaja bakinsa yayi shuru sukaci gaba da tafiya..
Dake Iro tashin wajen ne. Yasan lungu da sak’o na dajin. Dan haka nan kusa suka kusa b’ollowa titi.
Ahankali Iro ya fara dawowa baya da baya dayima d’aya daga cikin abokan nasa nuni da ido wai ya wuccesa. Aiko cikin sauri abokin nasa ya wuccesa saiya kasance yana gabansu su suna bayansa..
Da haka da haka Iro ya koma baya can ya kasance shine a qarshensu suna gaba yana binsu a baya..
Aiko ganin ADAMS ya tattara hankalinsa kawai a gabansa. Sai ko Iro ya d’aga sandarsa sama ???? ya sauketa a ƙeyar ADAMS. Saiji kake gubbb????…..
Ai nan take ADAMS yaji kansa nayi masa hajijiya. Bai samo nutsuwarsa ba Iro ya qara sakar masa wata sandar awajen.. Aiko wannan karan sai zubewa qasa ADAMS yayi warwar alamar sumewa.. Dan bugu ne na shammata. Kuma na mugunta. Sannan nasan illatarwa..
Dariya Iro yayi da cewa.. “Dama nayi ma ZUCIYATA Alqawari bazan tab’a garinka kaci gaba da rayuwa da MUSLEEMA ina gani ba.
Nayi alqawarin saina maka illah. To gashi ka gani…
Sanda ya gama duk iskancinsa sannan suka kinkimesa sukayi titin dashi… Basu qarasa titin ba suka ajiyesa dan hutawa
Suna cikin hutawar ne zai sukaga wata mota tatsaya wani na miji ya fitto daga motar da mata biyu suna masu duba motar…
Can sai sukaga matan sun fara nufo inda suke da gorar swan water a hannunsu.
Kan suyi wani qoqari na b’oye ADAMS kar matan su gansa saiya kasance har sun iso wajen nasu. Lokacin Yayi daidai da rungume Adams da Iro Yayi
D’aya daga cikin matan tace dan Allah ku temaka mana da ruwa musama motarmu..
Kan subata amsa d’ayar tabigi kafad’ar wacce tayi maganar tace.. “Kinga salma wannan mutumin baya miki kama da LEEKITAN da yake duba momy wanda take gaya mana ya b’ata shekarun baya…
Qura ma ADAMS ido wacce aka kira da salma tayi. Can tace. Kuma fa suna kama. Saidai wannan yad’anyi baqi da rama.
“Nima abinda magani kenan. Waccan yafi wannan fari da gogaggiyar fata Wannan kuma Yayi baqi da siranta.. D’ayar tafad’i hakan danuna tabbaci
Salman tace… “Niko mema sunan wancan d’in…
“Ni dai nafi saninsa da LEEKITAN ZUCHIYA kamar yanda momy take fad’a yafi duba ZUCIYATA akan kowa b’angare na jiki. Bacin hakan bansan ainiyin sunansa ba. Kinga munemi abinda zamu nema gunsu lokaci na tafiya.
Jan numfashi salman tayi da qara kallansu tace.. “Dan Allah kuna da ruwa..
Girgiza mata kai iro yayi alamar basu dashi.
“Toh yanxu a ina kuke ganin zamu samu
“Gaskiya bamu sani ba. D’aya daga cikin abokan Iro yace da ita hakan
Ganin hakan sai suka tafi dan su gayama saurayin da suka fitto tare dashi daga cikin motar wanda ya bud’e murfin gaban motar yana dubawa.
Ahankali ya kallesu yace dasu aina samu ruwan. Sukace a’ina ya samu. Nan yake gaya musu Ashe yana dashi a bayan but na ledar pure water. Sukace toh yanxu gyaran me yakeyi. Yace kawai yana dad’a duba motar ne bawai badan tana da wata matsala ba. Jin hakan sai yasa suka shige cikin motar shima ya rufe murfin gaban motar yashiga ciki sukayi gaba abinsu..
Iro ya kalli abokansa yace “Yanxu ya zamuyi dashi ne.
“Kawai mubarshi anan.. Inji wani daga cikinsu.
Iro yace.. “Kai baka da kai. Idan muka barshi anan wani na temaka masa ya farfad’o zai iya gaya masa inda yake. Kaga shikenan ya qara dawo mana ruga kenan. Kawai mu jira wata motar Lodi wacce zata gari me nisa saimu biya direban yakaishi can. Idan ya tashi duk wanda zai gayama daga Rugar malam jauro yake baza’a kallesa ba. Dan ba wanda ya Santa a garin. Kunga shikenan zaiyi hakuri ya kama wata rayuwa. Ni kuma na aure MUSLEEMA..
Sun yarda da shawarar tasa..
Dan haka suka zauna awajen sunata hirarrakinsu. Suna kallan motoci na wuccewa daga nesa. Tunda su motar Lodi suke nema tazo..????
Suna nan a haka saiga wani me motar Lodi zai wucce.. Ai da sauri Iro yaje ya taresa.
Direban ya zaci kayansa ne wani ya kunce ya fad’i. Saida ya tsaya yaga tsab’anin hakan
D’an tsohu ne direban. Irin tsofaffin y’an iskan nan. Dan kana masa kallo d’aya zaka san d’an bariki ne.
Gashi ya bugu alamar yasha kwaya tamai karo kamar yanda suka saba sha.
Da wani yanayi ya kalli Iro yace.. “Kai Yaro menene dalikinka na tareni..
Iro ya kalli bayan motarsa da take abud’e hanhai kamar ta d’aukar gawa. Sai kullun kayayyaki da suke cikin buhu burjik alamar lodi. Saiya dawo da kallansa garesa Yace.. “Dan Allah wane gari zaka.
Direban yace.. “KANO na nufa…
Da sauri iro yace.. “Dama ko wani d’an uwanmu ne zashi KANON gashi can. Dan Allah sai musamaka shi abaya cikin kayanka. Kana zuwa saika saukesa..
Direban ya kalli Iro a wulaqance yace. “Ban gane kusamin shi cikin kayana kamar wani kayan wanke ba. Shi bashi da rai ne daba zai hau da kansa ba sai kun sashi…
“aa ba wai haka bane yana da ciwan bacci ne. Yanxu baccin yayi.. Ga wannan dan Allah katemakemu musa maka shi.. Iro ya fad’i hakan da miqara masa kud’i har naira dubu uku..
Kunsan direbobin nan da san kud’i. Bare wannan dayake a make. Ainan da nan ya amsha kud’in yana cewa kusashi.
Nan take Iro yakira abokansa dasu tawo da ADAMS d’in.
Cikin sauri ko suka kinkimosa suka kawosa nan.
Haka suka temaka ma iro suka sashi cikin kayan lodin nan cikin hikima wanda kana gani zaka zaci bacci ne ya d’aukesa. Dan sun ajiyesa da tsari..
Suna gama sashi suka cema direban sun sashi. Nan ko yaja motar shi abinsa.
Iro da abokansa suka sheqe da dariya suka koma cikin dajin dan nufar Rugarsu…
Lokaci lokaci sojoji masu tsaran hanya suka cema direban daya d’auki ADAMS d’in.. Shiko wannan baccinsa yake abinsa.. Direban ya kan basu amsa da cewa. Eh yayi bacci..
Lokacin dayaga yafara nufo kano tsayawa yayi anan d’an wani daji ya fitto ya karema Adams kallo yadai tabbatar babu numfashi atare dashi. Aiko saiya saukesa ya barsa nan bakin titi yana cewa “Y’an iska qilama matacce suka samin dan nashiga uku.
Haka direban nan yayi gaba abinsa yabar Adams anan yashe…
Minto goma tsakani wani Alhaji yazo wucce da motarsa me d’an kyau haka shi da yaransa da alama suna kan hanyarsu ta nufar wani gari ne. Sai kawai yaga ADAMS a yashe kan titi.
Nan ya yatsaida motar tashi suka fito shi da d’ansa dan ganin abin mamakin waye haka akan titi..
Suna zuwa alhajin nan ya qarema ADAMS kallo ya tabbatar lalle wannan idan ba doctor ADAMS bane LEEKITAN ZUCHIYA ya tabbatar d’an uwansa ne.
Dan haka yasa d’ansa ya temaka mishi su sashi cikin motarsu. Suna mamakin ya akayi yake kwance haka a gefan titi inda babu kowa agun haka. da alamama ko rai yayi halinsa.
Fatansu dai yanxu su isa garin nasu na kaduna su kaishi asibiti suji yana da rai koko baya dashi dan sunji jikinsa bai sake irin na mamaci ba ..