LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin ikwan Allah sun iso garin kaduna lafiya basu zarce ako Ina ba sai’a wani asibiti wanda ya amsa sunansa new yan hospital.. Anan masana sirrin lafiya suka shiga caje ADAMS. Nanko suka gano yana da matsala babba. Suna tunanin tunaninsa ya tab’a d’aukewa a baya. Yanxu suna fatan idan ya tashi farfad’owar tunanin nasa ya daidaita..

Jin hakan da alhajin yayi sai kawai ya kira Dadyn ADAMS a waya dake amininsa ne yace mai dan Allah yazo nan asibitin yaga wani mutum me kama da ADAMS nasu. Shifa yana ginin kamar Adams ne mah.
Ai Dady najin batun abokin nasa ya tashi zunb’ur daga falansa ya saka takalmi ko bin kan d’aya daga cikin matan nasa baiyi ba ya ficce daga gidan sai asibitin…
Dady Suma yayi dayaga ADAMS. Dan babu wani canji da ADAMS zai samu a rayuwarsa wanda zaisa Dady ya kasa gane shi..

Bayan ya farfad’o kuka ya sake yana me hangen ADAMS ta jikin window saboda likitocin sunqi yarda ya qara zuwa ga ADAMS a karo na biyu dan karya qara sumewa..
Dady yasha kuka dan yacire tsammanin qara ganin ADAMS d’insa…

Dady ya tabbatar ma da abokin nasa Adams ne ba wani ba..
Anan abokin nasa yake basa labarin yanda akayi yaga ADAMS d’in. Da bayanan da likitoci suka fad’a akansa..
Jan numfashi Dady yayi. Ya tabbatar Allah shine me iko.
Dama saidai idan ADAMS baya cikin tunanin shine zai iya d’aukar way’annan shekaru batare da yayi waiwayen gida ba…
Anan Dady yakira su Ammi ya gaya musu Amman Yace karsu gayama su NUFAISAT har saiya farfad’o.. Ammin Adams bata tab’a jin labari me dad’i irin nayau ba…
Jin dad’in nata yaqara tabbatuwa ne lokacin data hangi ADAMS d’in tajikin window ita da Hajjiya Rukayyat….

????????????????????????????????????????????????????????
Me karatu idan kayi tunani ya kamata kasan koda ADAMS ya farfad’o bazai iya tuna wata rayuwa yayi da wata MUSLEEMA ba..
Koda zai tuna wani abu tunanin zai dinga masa wasa ne kamar yayi mafarki ne ya tashi. Kuma mafarkin bazai nuna mishi komai yanda zai ankare ba.

Sannan kunsan ambar baya da q'ura tafannin su MUSLEEMA..

Kuci gaba da bina a LEEKITAN ZUCHIYA inda zamuga wacece cikin matan Adams take da mallakin wannan sunan abakinta na LEEKITAN ZUCHIYA ina zata ganshi ya gyara tunaninta..????
[7/17, 3:49 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 21☆

Zama Amminsa tayi tana me godema Allah daya bayyana mata d’an nata..

Hajjiya Rukayyat ko haka kawai sai taji bataji daɗin bayyanar ADAMS ba.

Dady ko sallar godiya ga Allah yake tayi dan ba qarya yaji mafificin Farin ciki sosai da yanda ADAMS ɗin ya bayyana.

ADAMS bai samu kansa ba sanda yakai kwana uku kana ya samu kansa.
Lokacin daya bud’e idansa qarema ɗakin dayake kallo ya fara yi. Yana tunanin meya kawosa asibiti haka…
Dake shigowar doctor Suleiman kenan wanda yafi bashi kulawa sai yayi murmushi dace mai. “Masha Allah. Allah abin godiya. Wlcm da tashi.
Murmushi ADAMS yayi masa da faɗin. “Yauwa. meya kawoni asibiti haka.
Murmushi doctor Suleiman ya qarayi yace.. “Bara dai na kira maka iyayenka sai kaji daga garesu. Amman kafin nan ɗan bani dama na qara tabbatar da lafiyarka..
Murmushi ADAMS d’in yayi mai kawai.
Ganin hakan saiya fara dubasa dakyau ya tabbatar yanxu bashi da wata matsala sai ɗan ciwan kai dayace mai yana damunsa.
Magani ya basa da ficcewa ya gayama su Dady ya farfad’o. Ainan take sukayi ciki da murnarsu. Dady ya kama hannunsa yana nuna masa zahirin Farin cikin da yake ciki.
Yace dashi. “Yanxu Ina ne yake kama ciwo my son.
ɗan ɓata fuska ADAMS yayi da cewa. “Kai na ne dai kawai.. Wai Dady meya faru dani ne aka kawoni asibiti.
Shuru Dady yamasa. Sai Amminsa ce ta amshi zancen da cewa. “kai zamu tambaya meya faru dakai. Amma ba yanzu ba sai mun koma gida.

Sun ɗan jima suna hira. Can dai ADAMS ya kasa haƙuri yace. “Ammi ina NUFAISAT da TAUDHAT ne & my daughter Haneepha..
“ADAMS kayi haƙuri mu koma gida mana. Yanzufa ka tashi ya dace kabama kanka lokaci ko kaɗan ne. Ta gayamai hakan da damuwa
Shuru ADAMS yayi. Yanxu jikinsa ya fara basa akwai wani abu da ya faru wanda basu san su gaya masa..

Haka zuwa can yamma bayan likitocin sun tabbatar da bashi da wata matsalar daza tasa su riƙesa sai kawai suka bashi sallama.
Adams yayi mamakin yanda ba asibitinsu aka kaishi ba.

Mamakinsa ya qara tabbatuwa ne lokacin da suka isa gidansa. Yaga canji dadama agidan. Dan Dady tun randa yaga ADAMS ɗin yasa aka fara gyaran gidan nasa. Anyi saban fanti anyi gyaran sauri dai gaskiya ba lafe gidan ya qara kyau. Anan yake sanar da masu tsaran Adams ɗin cewar anga Adams ɗin
Shiyasa yanxu da sukazo gidan sai shigowa suke suna masa barka da dawowa.
Shi dai amsawa kawai yake yi amma azahiri bai san meyasa suke mai barkan ba..

Lokacin daya shiga toilet wanka matsama kansa yayi da tunani yana san tuno wani abu. Amma sam bai tuno komai ba.

Bayan ya fitto yana shafa mai da alamama kayan shafe shafen nasa sabbine ne aka saka mai awajen. Murmushi kawai yayi yana tuna NUFAISAT dan itace ta fad’omai. “Wai suna ina ne.. Yayi furucin abayyane.
Sauri sauri gudu gudu haka ya gama kintsa kansa ya dawo falan nashi inda su Dady suke jiransa..
Anan sukace ya gaya musu bayan tafiyarsa garin gwambe meya faru dashi…
Ai dajin haka nan take ya fara tuno abin daya faru..
Sanda ya gaya musu komai wanda y’an iskan yaran nan suka masa.
Sannan yaqara da cewa.. “Wallahi Dady bayan hakan bansan kuma meya faru dani ba. Sai yanxu dana tsinci kaina a asibitin da muka dawo yanzu..

Jan numfashi Dady yayi sannan shima ya kwashe duk yanda al’amuran suka faru dasu anan..
Sosai ADAMS yayi mamakin abokin nasu Ibrahim. Ya tabbatar da lalle mutum abin tsoro ne. Amma banda haka hujjar dashi Ibrahim ɗin ya bayar wai akanta yake neman rayuwarsa sam ba abar dubawa bace awajensa shi.
Dan gani yayi ai ɗaukaka awajen Allah take kuma mutum baya tsallakema arziƙinsa

Hankalin ADAMS ya tashi sosai dajin yanda ya ibi shekaru masu tsawo haka. Gashi shi ya kasa tuno komai bare ya gaya musu gashi gashi ga rayuwar da yayi.. Saidai ya dace ya koma inda aminin Dadyn nasa ya tsinceshi yaga ko akwai wanda ya sanshi agun…

Nan dai yaci abinci me rai da lafiya wanda Amminsa tasa laraba me aikinta tayi masa tun sa’adda ya farfad’o.
Sanda ya gama ci take gayamai yau yaci girkin ƴar aiki. Da mamaki yake kallan Ammin tasa da cewa dama ba ita ce tayi mai ba. Hajjiya Rukayyat tace yi shuru dai kawai dan yau kaci girkin ƴar aiki..
Murmushi shida Dady da Salim sukayi.
Anan Dady yake cemai bara yaje gida ya kira iyayan matan nasa NUFAISAT da TAUDHAT dan agyara musu auran nasu..

Komai yayi daidai inji ADAMS.
Karb’ar wayarsa yayi gun Amminsa ya kira Yusuf awayar yake cemai… “Kai gauro ban mutu ba. Dena nemana nadawo gida cikin hankalina????..
Yusuf dake kan gadansa damuwar kakarsa ta ishesa kan saiya nemo matar aure sai ganin kiran ADAMS ɗin kawai yayi awayarsa. Da matuqar mamaki ya amsa kiran yana addu’ar Allah yasa yaji muryar ADAMS d’in.. Aiko yana jin muryar tashi ya tatashi zumbur dace mai.. “Alhamdulillah.. Allah na gode maka daka dawomin da aminina ɗan uwa na. ALLAH kabarni dashi ko’a gidan ALJANNAH NE…
Dariya ADAMS yayi da faɗin. “Wato saida na ɓace kasan mahimmanci na agareka ko.
Yace “kamarko kasani ɗan uwa. Yanxu dai kana ina ne wallahi na zaƙu najika na ganka ko Farin cikin nawa yayi low.
“Saidai yayi hai✋????. Dan daga lahira nake magana dakai..????
Dariya sukayi gabaki ɗaya.. Adams yana meci gaba da cemai yazo gidansa ya samesa yana so yaje yaga ƴan matansa wato NUFAISAT da TAUDHAT

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button