LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ai ba shiri Yusuf ya fito daga ɗakinsa direct ga motarsa ya nufa bai tsaya ako ina ba sai’a gidan ADAMS. Anan ko falansa ya gansa ya rungumesa suna masu jin daɗin ganin juna.
Sanda ADAMS ya bashi labarin komai. Sannan shima Yusuf yace. “Wallahi na shiga damuwa daban ganka a garin gwambe ba. Haka nashiga tashin hankali da Ibrahim yake bayanin wai shine wannan maqiyin naka me neman rayuwarka.
Wato ADAMS wallahi yanxu mutum tsoro yake ban. Shiyasa naqi yarda da kowa tun bayan ɓatanka bani da aboki. Yanxu naji mafificin Farin ciki sosai dana tsinci muryarka cikin wayata. Dole na qara Alwala nayi salla danna godema Allah daya qara haska fuskokinmu gani gaka…
Qara rungumarsa ADAMS yayi dan ga zahiri nan na damuwar rashin nasa ta bayyana ajikin Yusuf ɗin danya rame sosai gashi bashi da kuzarin da yake dashi kamar yanda ya sanshi.
Ahankali yace dashi. “Har abada bazan samu abokin gaskiya kamarka ba Yusuf. Wallahi ina sanka ina qaunarka kaci gaba da suna da amana nima zanci gaba dasanka da amana.
“Baka da matsala da hakan ADAMS. Yanxu dai ina muka nufa. Sannan banga su Dady ba.
“Eh su Dady sunyi gida. Yanxu dai rakani wajen matana zakayi naga awane yanayi suke. Duk da na samu labari agun Dady kana kulamin dasu sosai. Wannan ma yasa nake san qara gode maka..
“karka damu da wannan ma. Dan Idan baka waje komai naka abin dubawa nane. Haka nasan idan nima bana waje komai nawa abin dubawarka ne. Yanxu muje Kagansu hankalinka ya kwanta. Dan naga har wani rawar kai kake…
Murmushi ADAMS yayi da dakar kafaɗar Yusuf d’in Suka ficce daga falan…
Da sauri masu tsaransa sukazo dan bud’e musu mota sukaisu inda zasu.
Dakatar dasu ADAMS yayi da cewa.. “Yanxu na gane maqiyin nawa me neman rayuwata. Zanyi zama daku ran lahadi in sallameku dan dama nifa ba wani san yawo daku nake ba.
Cikin sanyin jiki suka kallesa da cewa. “Bamu fatan barinka oga. Saboda kai mutum ne. Kasan darajar ɗan Adam. Gashi abinda kake bamu yana wadatamu da iyalanmu. Idan har kace baka san kulawar da muke baka bazamu tab’a samun wanda zai dinga biyanmu yanda ya dace ba..
Jan numfashi ADAMS yayi da cewa… “Toh naji. Kudai had’a kanku ranar lahadi kusameni. Sannan yanxu dai bani buqatar kuyimin rakiya.
Toh suka cemai saiya shige motar Yusuf ya jasu..

Suna zuwa unguwar sukaga TAUDHAT ta fitto taci kwalliya ita da yarinyarta Haneepha.
Waro ido ADAMS yayi ganin yanda tayi ƙiba komai na jikinta ya cika tam tam. Ta qara wayewa da ganinta kasan tana jin daɗin rayuwa..
ADAMS yace. “Wow Hankalinta akwance.

“Kuma fa kwanan nan tafara qibar nan. Cewar Yusuf.
Tsaki Adams yaja da cewa. “Karka wani kareta malam. Yana faɗin hakan ya fitto daga motar sosai jikinsa yake fudda qamshin turaransa..
ƙamshinne ya bugi hancin TAUDHAT ta ɗago da saurinta dan jin wane mahalukin ne ya mallaki ƙamshin ADAMS…
Ai tana haɗa ido dashi tawancakalar da jakarta da wayarta kobi takan ƴarta Haneepha batayi ba ta daka wani tsalle saigata a ƙofar gidasu. Da sauri tashige cikin gidan nasu tana maida numfashi. Tunaninta gamo tayi. Dan yanxu tagama tunanin ADAMS d’in shiyasata tunanin ko wannan aljani ne.

Murmushi ADAMS yayi danya lura ta tsorata dashi ne.
Ahankali yaje ya kama hannun Haneepha tare da rage tsawansa yace da ita. “Haneepha kin gane ni. Shuru tamai tana me qarema fuskarsa kallo. Can tace. “Na ganeka kana kama da Dadyna na photo. Sai dai Dadyna ya fika fari.
Murmushi ADAMS yayi da manna mata kiss a goshi. Yace. “Nine Dadynki kawai nayi rashin lafiya ne yasa nayi baqin. Amman Farin nawa zai dawo nan kusa kinji..
“Toh Amma me yasa ka gudu ka barni baka zuwa guna. Kullum mamana ce take kaini skull kai baka kaini.
“Ba guduwa nayi ba. Nace miki bani da lafiya ne amma yanxu na samu sauqi kullum zaki dinga ganina kinji.
ɗaga masa kai tayi. Alamar taji..
D’auko jakar TAUDHAT d’in yayi da wayarta yaba Haneephan yana cigaba dace mata
Yanxu jeki gayama mamanki tafito..
Ai da gudu tayi cikin gidan tana cewa mamah mamah kifito ga Dadyna..

Kama hannunta TAUDHAT tayi da cewa. “Ya kama hannunki. “Har kiss yamin Dadyn. “Toh jeki gun mamah zanje ni gunsan.
Toh Haneepha tace mata tanufi gun mama dake zaune kan taburma tana cin burabisko..

Da qarfin hali TAUDHAT ta fitto tana qara had’a ido da ADAMS ya galla mata harara.
Sanda ta iso garesa yace mata. “Wai da ɗazu ina zaki kikaci wanka haka.
Kallansa da sauri tayi yanxu ta tabbatar da cewar shine. Cikin matuqar Farin ciki sosai tace.. “Wayyo Allahna wai da gaske Kaine agabana. Harfa na cire tsammanin ganinka.
Wayyo Allah abin godiya. Gaskiya naji mafificin daɗi da sanyi sosai. Kamar na rungumeka saidai gamu akan titi????.
Murmushi yayi da cewa “baki dai so hakan ba. Yanxu kaimu muga Mamah idan naganta anjima idan Aka dawomin dake kyayimin yanda kikeso tunda yanxu kin kasa.

Murmushi tayi da shigewa gaba tana cewa. “Muje kawai..
Haka tana gaba suna binta abaya har zuwa cikin gidan nasu.
Mama murmushi tayi mai da nuna mishi Farin cikinta Sosai na ganinsan da akayi. Har take qaramai ai bata dad’e dayin waya da Dadynsa ba yake gaya mata bayyanarsa.
Tana kyautata zatan anjima ma zaiso kan batun komawar TAUDHAT..
Murmushi ADAMS yayi suka tashi dayi mata sallama kan zasu shiga cikin gidansu NUFAISAT..
Nan taqara sakin fara’a dayi musu fatan alkairi.

Bayan sunfita ne TAUDHAT taja tsaki dacema Maman nata.. “Ke dai mamah bazaki dena munafunci ba. In banda munafunci Ashe d’azu da Dadyn ADAMS d’in kike waya shine kika kasa sanar dani angansan sanda yazo sannan nake sani…
Kallanta maman tayi kawai dan yanzu lamarin TAUDHAT d’in ya dena bata mamaki Sam…

Su Adams ko gidansu NUFAISAT suka shiga… NUFAISAT ɗin na barandarsu ta sama da wani littafin AUNTYN LUV tana karantawa me suna ABU KAMAR WASA FAH jaruman cikin labarin suna burgeta hakan yasa take tare da nishaɗi..
Ji tayi ajikinta kamar ana kallanta. Saita maida kallanta inda tafi tunanin daga nan ake kallan nata… Aiko sai ganin masoyin nata tayi shida Yusuf jikin motar mummy ɗinta….
Nan tatashi da yar da littafin tana me murza idanta danta tabbatar da gaske mijin nata ne abin alfaharinta..
Murmushi ya sakar mata da dafa Yusuf dan ta tabbatar dashi ɗin ne..
Aifa ƙafa me naci ban baki ba. Nan tasheqo da gudun gaske ta sauko qasa mummy dake falo tana yankan farce fad’i take “ke lafiyarki kike gudu haka.. Sam batabi ta akanta ba sanda tayi waje lokacin yayi daidai da ware mata hannunsa da yayi alamar ta rungumesa. Dama itama niyarta kenan. Ai zafin nama taje ta rungumesa.. Fad’i take. “Mijina ka dawo gareni. Mijina ne wallahi. Mijina ne Yusuf ba kowa ba. Mijina ne na tabbatar. Mijina ne naji ɗuminsa. Mijina ne shine wallahi… Saka mata hannunsa yayi a bakinta alamar tayi shuru danin yanda take a rikice .. Aiko shurun tayi idanta cikin nasa. Cikin sanyayyiyar murya yace.. “Bazan iya rayuwa babu ke ba! dan ina tabbatar miki ko mutuwa ce tazo d’aukata rokwanta zanyi ta had’a dake. Saboda ina san kabarinmu suyi makwaftaka da juna…
Tunda nadawo haiyacina farkwan tunanina kece my LUV.
Dan haka ki nutsu da kyau matata danki qara gaya min naji sanyi araina. Madallah. Yanzu gaya min ya kikaji da kika ganni…

Jan numfashi tayi
“Komai ma naji mijina. Na rikice matuqa da ganinka. Dan Allah kayima zuciyata gata kada ka qara aikata wannan babban lefi agareta.
Na shiga tashin hankali. Na shiga ɗimuwa sosai dana rasaka. Ashe da gaske kaine ganina. Dana rasa ganinka kowa haushin kallansa nake ji.. Ashe da gaske kaine jina. Dana rasa muryarka. Kowa jin muryarsa nake kamar maɗaci. Ashe da gaske kaine gangar jikina. Dana rasa ɗuminka rashin lafiya baibarni ba sai yanxu dana jini jikinka. Nayi missing abubuwa uku arayuwata. Wanda tunda ka ɓace har yau mummy da Dady wany’anda suka isa dani fama suke dani akansu.
Sun kaini asibiti yafi sau nawa akan hakan.
1 Bana cin abinci yanda ya dace. B’cos idan nasaka agabana kai nake tunani. 2 Bana bacci yanda ya dace. B’cos idan na kwanta kai nake tunani. Bana cika magana da kowa. B’cos daikai kaɗai na iya hira..
Meyasa hakan ta faru dani. Saboda karigada ka ɓata masu tarbiyar ƴa…
B’cos daka baka auranta kacanja musu duk wani abu da suka raineta dashi.
ADAMS kaine rayuwata. Nayi alqawarin bazan tab’a bari wani namiji ya raɓar maka jikina ba idan har na rasaka arayuwa saidai na mutu babu aure… NUFAISAT takai ƙarshen zancenta da zubo da hawaye..
Ahankali yahau lashe mata su. Cikin matuƙar so da ƙauna
“Ina sanki matata. Ina qaunarki matata. Ina fatan zarce kasancewa dake har agidan ALJANNAH….
Kai bakinta tayi cikin nasa ta aika masa da wani shu’umin kiss…. Cikin matuƙar buƙata yaso gyara mata mazauni a qirkinta wajen san su kasance da jin ɗumin bakin junansu. sai dai Yusuf ya katse musu jin dad’in nasu wajen cewa…. “Na farko agidan surukai kuke. Bacin nan saiku ɗan jin kirta agyara muku auranku…
Denawa NUFAISAT tayi cikin jin kunyarsa. Sai dai duk da haka sanda ts qara bajewa a qirjinsa tana lumshe ido da kallan Yusuf tace.. “Dole surukan su mana uziri..
Murmushi yayi da cewa.. “Kimana iso wajen momy kawai mu gaisheta idan yaso kwaci gaba..
ɗago da kanta ADAMS yayi da cewa.. “Kiyi haƙuri matata ganin yanda ya katse mana qauna…
“Da wani hali tace mai.. “Ba batun haƙuri kawai ka hukunta shine abun da zaifi.
Murmushi yayi da faɗin “Yusuf ne fa..
Itama murmushin tayi da bashi amsa da. “Tona nayi hak’uri.
“Yauwa masoyiya maza rakamu gun mummy itama taganni ta tabbatar.
Murmushi ta qara mai…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button