LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiko ADAMSY shuru yayi yana jinsu..
Da farko yaji fad’uwan gaba dayaji furucin mahaifin nasa nasan ya ƙara Auran
Dan ko’a mafarki baiji aransa yana San qara Aure ba..
Saidai kuma yaji mamaki sosai yanda hajjiya Rukayyat ta nuna damuwarta akan batasan ya ƙara Auran
Hakan yasa kwakwalwarsa tashiga tunani dan tagano dalilinta..
Yadai fahimci koma menene dalilin nata bame kyau bane
Ya gane da daɗewa ba sanshi take da haihuwa ba
Toh me take nufi da hakan..
Shuru yayi na wani d’an lokaci… Danya raasa gane manufarta..

Dan haka Ahankali ya kalli Dadyn nasa yace mai… “Nasan kana San yara Dady.. Kuma dama nima ina San gaya maka Inasan ƙara Aure….
Kawai jira nake mugama dai dai tawa da Ita yarinyar nazo maka da batun…
Ai da sauri Dadyn nasa ya tashi daga shigingiɗan da yake cikin farin ciki da murna yace… “Masha Allah.. Allah abin godiya.
Gaskiya naji dad’in hakan
Ku dai dai ta Inasan ganin yaranka ADAM.. Allah yasa nagansu da raina
Da Murmushi ADAMSY ya kama hannun Dadyn nasa yace… “Insha Allah Dady zaka gansu kana raye.. Har suxo kan cinyarka suja maka gemu..????
Dariya sosai Dadyn nasa yayi yana shimai albarka….

Afusace hajjiya Rukayyat ta gallama ADAMSY harara tace… “Ka kalleni ADAM. Kasan bana magana biyu anan gidan.
Dan haka bazaka ƙara Aure yanxu ba..
Sai nan da wasu shekaru..
Har yaushe kayi Auran dazakace zaka ƙara.
In banda zalama irin taku ta yaran zamani meye matarsa NUFAISAT bata had’aba
Yarinya me hankali da nutsuwa ga ladabi da biyayya
Kai yanxu baza kaji kunyar idanta Idan taji zaka ƙara Aure ba!!!

Yanxu ADAMSY ya ƙara tabbatarwa tana da manufa me qarfi kan bata San ya ƙara Aure

Dan haka da Murmushi cikin sanyin murya yace da Ita… “Momy ina San ƙara Aure ne badan matsalar haihuwa ba.
Saidan karna fad’a ga halaka.
Azahirin gaskiya ina da ra’ayin yin mata hud’u..
Wannan shine dalilin dayasa zan ƙara Aure badan NUFAISAT tarageni da komai ba
Dake mun fahimci juna da Ita na gaya mata dalilina nasan na ƙara Aure
Kuma tafahimta har ta’amince dana nema mata abokiyar zaman tagari…
Ki kwantar da hankalinki momyna.. Insha Allah mata bazu wahalar miki dani ba… Dan nasan matsalarki kenan…. Ya ƙarashe furucin da tashi yana mah Dadynsa sallma da Murmushi akan fuskarsa yake cemai daga gun Amminsa zai wucce gida basai yadawo ba
Fatan alkairi mahaifin nasa yayi masa shiko ya ficce da sauri dan bayasan hajjiya Rukayyat d’in tace mai wani abu…

Aiko yana ficcewa itama taficce zuwa shashinta dan kiran aminiyarta Susan yanda zasuyi????

Shiko Dady da kallo yabita… Kana ya tab’e irin zakiji dashi d’innan…
[29/04 12:05 pm] ????◾◼▪????: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 05☆

Shiko ADAMSY can a bed yaga Ammeen nasa tana qoqarin kwantawa..
Aiko da Murmushi ta kallesa tace… “Yanxu nake tunaninka d’an albarka…
Fad’i nake araina kodai yau bazan ganka bane nayi baccina
Zama yayi kan kujerar dake kusa da bed d’inta yana cewa.. “Wane ni da qin zuwa ganin iyayena.
Koda ace NUFAISAT shed’aniyace. Bata isa hidimarta tasani mantawa da iyayena ba.
Ina sanki Ammeena..
Zanyi komai gareki dan kiji dad’i
Jan numfashi tayi dajin daddad’an kalamansa. Kana ta zauna gefan gadan nata tana me qara cigaba da kallansa tace.. “Abu d’aya yanxu zai qara faranta raina agunka ADAM.. Shine naga y’ay’anka..
Duk da cewar ina qaunar NUFAISAT.. Bazan so ka had’ata da wata mace ba. Danta tara duk abinda yadace asamesa agun Y’a mace..
Saidai zuciyata na gayamin.. Kodai zaka qara Aure ne..
Wallahi ADAM ba abinda nake buri ayanxu kamar naga y’ay’anka..

“Ammee kenan.. Insha Allah zakiga y’ay’ana. Yanxu ma maganar da muka gama kenan da Dady
Yana San na qara Aure amman kamar momyn Salim bata San na qara Auran
Saidai na tabbatar mata da cewar zan qara dan ina da burin Auran mace hud’u

Murmushi Ammeen tasa tayi da cewa. “Masha Allah.. Saika gaggauta neman wacce zata dace dakai… Dan Idan ka d’auki lokaci ba makawa zatayi wani abu akai.. Tunda kaga kamar bata so ka qara..
“Insha Allah kuwa Ammee

Sun d’an jima suna shirarrakinsu irin na d’a da uwa..
Sai daga bisani ya numfasa yace.. “Yanxu ni zan tafi.. Naga dare nayi.. Ko akwai wani abinda kike buqata.
“aa nidai gareni babu komai..
Saidai gobe baqin da zaka gana dasu da safe suna da yawa..
Murmushi yayi da tashi yana cewa.. “Ba damuwa. Allah ya qara shige mana gaba..
“Amiin. Tace dashi tana me Murmushi
Shima da Murmushin ya fitta daga d’akin..

Direct wajen shiyan kayan sanyi ya nufa.. Inda ya siyama Matar tashi ice-cream. Dasu mittifai da sauransu.. Kana ya nufi gida

Tun daga farfajiyar gidan yake jiyo ƙamshin turaran da Matar tasa tasaka a falan nata..
Murmushi yayi da girgiza kai. Yana tuna tsafta da kwalliya irin na Matar tasa..
Da cikakken nishad’i ya shiga falan yana cewa.. “Inafa jin daɗin turaran nan…
Ahankali tafitoh daga wani d’an sak’o tana Murmushi tace… “Har sai yaushe zaka dena wannan furucin da zaran kajiyo wannan ƙamshin..
Da wani salo. Da wani yanayi yake qare mata kallo tun daga sama har qasa..
Tayi mai kyau irin sosai ɗinnan????????
Danji yayi kamar ya saceta ya gudu..
Wani mini siket ne tasaka da wata riga wacce tatsaya mata a dai-dai na fulaninta..
Nan wajen kawai ta iya sitircewa a jikinta..
Haka kazanika shi mini ɗinma ba wai ya saukan mata bane.. dan Idan tayi kyakkyawan juyi zaka iya gano gabanta nan kusa basai kasha wahala ba..
Yafa kwaɗaitu fa sosai da yanayin.. Dan taga yanda yayi saurin haɗiyan yawo..
Shi dai yana San matarsa. Dan yana samun farin ciki daga gareta….
Rungumarta yayi yana kissing ɗinta tako ta ina yana cewa.. “Kinyi kyau sosai matata…
Ina sanki..
Ina ƙaunarki
Ina fatan kasancewa dake har ƙarshen RAYUWANA…

Tafi kowa sanin mijinta…
Bai iya ganinta ya barta haka kawai ba
Saidai Idan da baqi yayi musu alkunya
Ji take aranta tafi kowa Sanshi da ƙaunarsa

Taƙyer takwaci kanta tana cewa.. “Nakasa banbancewa
Shin awane yanayi kafisan kaganni..
Na saka ƙananun kayane ko nasaka kayanmu na hausawa..
Idanshi ya kaɗa yayi jah yace da ita.. “Me kika gani..
“Gani nayi a kowane yanayi kaganni rikicewa kakeyi..
Murmushi yayi da cewa.. “My luv bazaki gane qaunar da nake miki bane..
Yanxu dai muje ki bani nasamu nutsuwa.. Amman dan Allah ki barni nayi yanda nakeso..
Hararar wasa tasakar mai da cewa.. “Yaushe zaka dena wannan futunar taka…
Cikin sauri ya katseta da cewa.. “Randa namiki Kishiya ranar zan dena damunki da yawa…
Aiko nan take ta zumɓuro baki tace… “Zanfa babbakaku daga kai har kishiyar..
Dariya yayi sosai yana kallanta da bata amsa.. “Toh Idan kuma ya kasance Y’ar uwarki ce fah
“Wake nan..???? Wai kana nufin TAUDHAT…
ɗaga mata kai yayi yana kunshe muguwar dariyar dataxo masa..

Aiko turmuƙe fuska tayi kamar zatayi kuka tace… “Dan Allah kabari… Kaima kasan abune bame yuhuwa ba..
Nasan ko’a mafarki TAUDHAT baza tataɓa zama kishiyata ba..
“Ko….. Ya katseta da faɗin hakan yana me cigaba da cewa… Amman kinsan da cewa TAUDHAT tana matuƙar sona..
Jan numfashi NUFAISAT tayi da cewa. “Na lura yau sokake ka zautar dani da zolaya…
Kaga zomuje na shayar dakai dannaga a kwaɗaice kake dasu… Ta ƙarashe furucin nata tana me karɓar ledar dake hannunsa da kama hannun nasa tajashi bedroom ɗinsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button