LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan dare MUSLEEMA tattara kayanta tahauyi anufinta gobe idan Allah yakaisu zata cale zuwa garin na kano dan neman mijin nata…
Kallanta YAWO take kawai dan tausayinta ne ya kama zuciyarta.
Washe gari YAWO tasa aka kira mata Malam jauro ta gayamai zasu garin kano neman Ahmad.
Nan yahau cemata tayi hakuri zaisa mutane suje su bincika mata shi.
Tace bazai yuhuba. Tana san farin cikin jikarta. Dan ita kad’ai tarage mata arayuwa dan haka ita yanxu so take yasiye shanunsu sutafi da kuɗinsu danzai temaka musu sosai wajen nemansa. Saboda talura ma tunda suka rasa Ahmed d’in shanun sai mutuwa suke..????
Nan Yace mata shi bashi da kud’in dazai iya siye shanunsu kaf
Dake Hankalin yawo ya tashi ita buqatarta subar rugar dan kwata kwata tunda taga MUSLEEMA tayi yimma ita kano take san zuwa. Sai taji duk rugar tafitan mata arai. Dan haka cemai tayi yabata muliyan d’aya kawai ita tabar mishi shanun.
Murmushi Malam jauro yayi dan ganin hankalinta baya jikinta.
Tabbas yasan shununta sunfi karfin kud’in data fad’a. Dan haka kallanta yayi cikin tausayawa Yace.. Zai bata muliyan d’ayan Amman badan iya kud’inta kenan ba..
Dan haka tabashi kwana uku ya had’a mata kan kud’in
Haka YAWO taba MUSLEEMA hak’uri sujirasa zuwa nan da kwana ukun.
Haka ko akayi dan malam jauro ya had’a mata kud’in.
Yace idan tadawo saiya ware nasa yabar mata sauran shanun dan tasan shanunta sunfi qarfin kud’innan daya bata..
Nan YAWO tamai godiya shi kuma ya musu fatan alkairi akan Allah ya had’asu Ahmad wato ADAMS cikin sauri idan kuma sun rasasa su dawo karsu zauna ako ina..
Toh YAWO tace mai
Dake da yamma ya kawo musu kud’in hakan ne yasa suka bari sai gobe sabar rugar
Nan YAWO tama makwaftanta sallama da iyayan Hasiya mahaifan uwar MUSLEEMA
Sannan ta qara had’a kayan su a gana masgo tabama makwaftan nata sadakar kayan aikinta. Washe gari ko dake Dr Usman yazo ajiyan anan yaji komai daya faru. Shine ya fitar dasu daga rugar zuwa kan titi da motarsa.
Haka yabarsu zuciyarsa da jin takaicin yanda bai Adana hotan ADAMS ba lokacin da yake tare dasu. Daya d’auka ya Adana da yanzu yayi musu amfani dan baza susha wahala wajen nemansa ba.
Toh koma dai miye yana musu fatan alkairi.
Saidai me????
Bayan sun samu motar dazata kaisu garin na kano. Kafin su fitta daga garin gwamben Y’an fashi suka taresu. Anan suka samu nasarar amshe mak’udan kud’in nan da malam jauro yabasu.
Sauqinta d’aya dama YAWO taware dubu d’ari dansu fara amfani da ita.
To Allah cikin ikwansa da wannan d’arin suka tsira.
Sauran dubu d’ari taranko y’an fashin sun amshe.
Kuma sun sami nasarar amshe kud’in ne sakamakwan harbe wani da sukayi a qafa dayace bashi da kud’i. Toh Hankalin YAWO ya tashi shiyasa tabasu dubu d’ari taran tunanin d’arin data warene tabasu.
Sanda suka samo nasarar tafiya lafiya sannan tagane me yawan tabasu.
Sam YAWO bata wani damu ba dan tafi buqatar rayuwarsu akan kud’in…
Suna shiguwa garin na kano sai suka fara raba ido ta’ina zasu fara neman ADAMS wanda suka laqabawa Ahmad.
Tun a tasha MUSLEEMA tafara yima y’an tashan kwatancen ADAMS.. Wani ya kalleta cikin raini Yace… “Ke kin ishemu da kwatance. Idan zaki fad’a mana sunansa kifad’a kozamu iya ganewa..
Cikin sauri YAWO tace “Sunansa Ahmad..
MUSLEEMA ta girgiza mata kai da rungume Y’ay’anta tace. “Yawo wannan sunan da kuka rad’a masa ne. Kuma kinji abinda Dr Usman yake cewa. Zai iya yuhuwa dukan da Iro yayi masa ya iya sawa tunaninsa na ainihi ya dawo. Kuma idan hakan tafaru ba shakka nufar inda ya fito zaiyi. Bazai waniyi tunaninmu ba. Idanko haka ne dole muyi amfani da sunan da Iro ya gaya mana wanda yace matan nan sun fad’i wato LEEKITAN ZUCHIYA. MUSLEEMA takai qarshen zancenta da kallan mutumin tacigaba da cewa. Sunansa LEEKITAN ZUCHIYA dan Allah ka temaka min mijina ne shi. Yana nan wani fari kyakkyawa haka me yawan murmushi dasan tsafta…
Sheqe mata da dariya mutumin yayi tare da way’anda suke wajen. Nan ran YAWO ya b’aci ta kallesu da takaici tace.. “Haba yaran nan daga tambayarku sai kuhau yima mutane dariya.
“Mutumin ya kalle da cewa. “Kema tsohuwa da girmanki zaki tsaya biyema shirman jikarki. Fisabidillahi a’ina zamusan wani waishi LEEKITAN ZUCHIYA. Kuma gashi wai kyakkyawa me san tsafta da murmushi.
Yanxu idan ke mukama wannan tambayar fisabidillahi zaki bamu amsa.
“Me zaisa bazan baku amsa ba yaran nan. Idan nasan shi gaya muku zanyi idanko ban sanshi ba banga dalilin da zaisa na tsaya yi muku dariya ba.
Dariyar suka qara bushe musu da ita. Kana ya bata amsa da.. “Tomu bamu san wani waishi LEEKITAN ZUCHIYA ba. Kuje can gaba wala’Allah zakuci karo da Wanda ya sanshi..
Hawaye ne ya zuboma MUSLEEMA. Nan YAWO tatab’ata tana meyi mata nuni dasu qara gaba..
Afuwan masoyana LEEKITAN ZUCHIYA naku ne.. ????kuci gaba da bibiyata akansa
[7/23, 10:30 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 23☆
Haka suka qara gaba inda suka had’u da wani masifaffan tsoho ya kalli Yawo kallan wani iri haka yace. “LEEKITAN ZUCHIYA kowa kuke cewa. Yanxu ni a’ina zan sanshi. Da Allah ku qara can gaba qila kwa gansa.
Haka YAWO da MUSLEEMA suka dinga yawo suna neman ADAMS da bashi suna LEEKITAN ZUCHIYA amma basuci karo da wanda yace ya sanshi ba.
Duk sunsha ranah. Musamman kunsan garin kano da zafin ranah. Haka suka zauna bakin shagwan wani mutum me saida kayan provision dan ganin akwai wani me soya indomie da kwai. Haka suka bashi kud’i ya had’a musu yanda zai ishesu.
Bayan sun gamaci ne suka fara tunanin inda zasuyi sallah. Bama wannan ba a’ina zasu samu wajen kwana.
Wani saurayi ne yazo wuccewa Yawo takirasa take tambayarsa dan Allah a’ina zasu samu d’akin haya na sati biyu. Su baqi ne suna neman wajen kwana ne.
Kallan tsaf saurayin yayi musu kana yace suna da kud’i ne.
Nan YAWO tace mishi eh suna da shi.
Ai dajin hakan saurayin yace suzo zai kaisu wajen Hajjiya ladi tana da d’akuna acikin gidanta sannan tana bada haya yana tabbatar musu sun sami gidan haya me kyau dan ko’ina a gidan me kyau ne sosai
Haka YAWO da MUSLEEMA da yaranta sukabi bayan mutumin nan yakaisu gidan Hajjiya ladi dake unguwar bacirawa.
Hajjiya ladi shahararriyar shed’aniya ce. Kaf way’anda suke haya a gidanta gogaggun y’an iska ne karuwai. Shi dai wannan mutumin shiyake kawoma Hajjiya ladi mutane musamman way’anda idan ya lura basusan kan gari ba. To idan ya kai mata su yakan dawo da daddare yayima mutunan dai daya kawo mata sane wato sata. Sam bashi da wani aiki sai hakan.
Dan haka da suka isa gidan Hajjiya ladi kallansu tayi da kyau taga dai basu da fuskar mugayan mutane sai tace subata dubu talatin..
Ai nan YAWO ta zaro ido tace. “Haba keko baiwar Allah kiji tausayinmu mu baki dubu goma saboda muma bada hakan mukazo ba. Munzo da kud’i da yawa saidai munci karo da y’an fashi sun yashe mana me yawan. Nan YAWO takwashe komai tagayama Hajjiya ladi.
Azahirin Gaskiya Hajjiya ladi ta tausayama MUSLEEMA dan ganinta qaramar yarinya.
Saidai taji haushin YAWO over dan inda itace bazata tab’a Aurama ADAMS jikarta ba. Saboda bata san waye shi ba. Bata san daga inda ya fito ba. Haka kawai dan gwaninta saita kama ta bashi jikarta dan toshewar basira..
“Toh ai shikenan. Allah ya rufa asiri. Kidai bada dubu Ishirin kiyi wata d’aya. Idan wata d’aya yayi saiku fitta kubani d’akina idan kuma zaku qara biya saiku qara zama har Allah yasa kusami shi LEEKITAN ZUCHIYAR naku.. Hajjiya Ladi tafad’i hakan da wani tab’e baki.
Godiya YAWO tamata ta fito da kud’in ta qirga tabata. Sannan tamaida kud’in cikin y’ar lalitarta cikin wani d’an qaramin buhu duk wannan mutumin yana kallanta.
Haka Hajjiya ladi tayi musu jagora zuwa wani d’aki haka. Eh dai bashi da wani matsala. Dan akwai ledar d’aki cikinsa da wata yololuwar katifa da fillo..
Haka MUSLEEMA ta share d’akin tas tasaka musu kayansu a gefe sukayi sallah kana suka fara tunanin me zasuci na dare.
Anan kusa da gidan Hajjiya ladi akwai wata mata Yalwa me saida abinci safe da rana da dare tana da ma’aikata da dama. Matar ta’iya abinci sosai shiyasa mazaje masu aji daji da kansu da mata masu aji suke zuwa wajenta cin abincin nata.