LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

To gurinta Hajjiya ladi ta nunama su MUSLEEMA da suka tambayeta inda zasu sami abinci.
Kallan farko da Yalwa tama MUSLEEMA taji aranta dama tazama meyi mata aiki. Dan taga yarinyar tana da diri sosai zata qara ja mata Hankalin maza kwastamomi. Gashi ta mallaki duk wani abu da mazan suke so agun mace.
Dan haka da fara’a ta kalli MUSLEEMA tace.. “Daga ina kike yarinya.
Nuna mata gidan Hajjiya ladi MUSLEEMA tayi tace.. “Daga nan gidan nake..
“Ikwan Allah. Meya kawoku gidan.
Dake MUSLEEMA ahannu take burinta mutane su dinga sakewa da ita dan tadinga fad’in musu buqatarta na neman ADAMS ko Allah zaisa wani yace mata yasanshi. Nan tabata labarin abinda ya kawosu gidan.
Sosai Yalwa me abinci ta tausayama MUSLEEMA tace. “Aiko nayi mamaki danaji kince daga gidan Hajjiya Ladi kike. Ganin da nayi kamar kina da nutsuwa.
“A nazarce MUSLEEMA tace.. “Meyasa ki fad’in hakan.
“Eh gani nayi gidan karuwai ne.
Waro ido waje ???? MUSLEEMA tayi da cewa. “Gidan karuwai. Toh aimu ba karuwar bane. Meyasa wannan mutumin ya kawomu gidan.
“Nima mamakin danaji kenan. Karfa wani abu ya dameki dan zaman naku ai na wani d’an lokaci ne.
Murmushin yaqe MUSLEEMA tayi mata. Da miqa mata kud’i ta had’a musu abincin da MUSLEEMA tace mata tanaso..

Aiko MUSLEEMA na dawowa ta gayama YAWO agidan karuwai suke.
Ran YAWO baiyi mata dad’i ba. Amma data tuna zaman nasu na d’an wani lokaci ne sai Kawai ta share. Kula dai da yaran MUSLEEMA zatayi sosai dankarsu b’ata musu tarbiya.
Sosai yawo tayaba abincin Yalwa

Cikin dare da misalin qarfe goma sha biyu na dare wannan mutumin daya kawo su YAWO ya lallab’a ya tura d’akin dasu yawon suke yashige. Dake sun kashe kwan wuta da d’an hasken wayarsa ya dinga lalubar inda zaiga inda yawo tasa sauran kud’in nan. Aiko yaci sa’a. ???? nan cikin kayan su Khalit yagani. Ahankali kamar yanda yake tafiyar da motsin nasa ya d’auke kud’in gabaki d’aya. Har zai fitta saiya dawo ya sakama musu d’ari biyar a inda dai ya d’auki kud’in.
Kana ya ficce daga d’akin ahankali cikin jin dad’in yanda basu sakama ƙofar sakata ba kamar yanda yayi zato.

Washe gari da safe YAWO ta tambayi Hajjiya ladi kan inda zasu samu ruwan wanka. Hajjiya ladi ta cokaro d’an kwali gaba tace da ita Hita zaku sayo da d’an bokati da soso dakomai na buqata. Harda furko da gawayi kudinga yin abinda kukeso. Kamar yanda kukaga kowa nayi. Dake ku baqi ne kikawo kud’in naba almajirin gidan nan yaje ya suyo muku

Toh YAWO tace mata da dawowa d’akinsu. Anan tahau neman kud’in nasu tanema sama ko qasa babu ko sisi sai d’ari biyar.
Hankalin YAWO dana MUSLEEMA ya tashi nan suka fara hargitsa kayansu waiko zasu gani. Amma babu kud’in nan nasu ba dalilinsa.
Hawaye ya zuboma MUSLEEMA ta d’ora hannu aka tace “YAWO mun shiga uku. Yanxu waye zai bamu kud’i. Can y’an fashi sun amshe manyan kud’ad’an. Nan kuma gashi an yashe mana Sauran.
Sam YAWO bata iya ba MUSLEEMA amsa ba. Dan hankalinta ya tashi matuqa.
Da muguwar damuwa taje tana gayama Hajjiya Ladi sufa basuga kud’insu ba.
Dariya Hajjiya Ladi tasheqe musu dashi tace. “Ban gane bakuga kud’inku ba. Kun bar ƙofar taku a bud’e ne.
“Eh abud’e muka barta saboda nayi nayi na kulle na kasa.. YAWO tabata amsa da damuwa.
Qara dariya Hajjiya Ladi tayi tace.. “Shege d’an malam. Ai gaya muku ne banyi ba na sha’afa. Wannan mutumin daya kawoku jiya ai tantagaryar b’arawo ne.
Idan ya kawamin mutane irinku way’anda basu san gari ba. Zuwa yake daga baya yayi musu sane wato sata.
Dan haka sai kuyi hakuri.

YAWO ta waro ido tace. “Muyi hakuri muci me kenan. Yanxu tunda kin sanshi nezai hana ki had’amu dashi yabamu kud’inmu
Kallan raini Hajjiya ladi tayi mata da cewa. “Tabd’ijan. Ai sai dai kuyi hakuri dan Wallahi tunda d’an malam ya sace muku kud’in ban yatafi kenan har abada. Toni yanzu ma a ina zanga d’an malam. Dama idan ya aikata irin wannan nemansa ake a rasa sai ya daidaici mutanan sun tafi yake dawowa yaban labarin yanda yayi satar.
Kinga tsohuwa kibar batun d’an malam yanxu kikama abinda zai fishsheku
“Innalillahi-wa’inna’ilaihirraji’un. Shine abinda YAWO ta fad’i.
MUSLEEMA ko sai hawaye take tana hararo mezai faru dasu gaba yanzu tunda ba kud’i.

Da d’ari biyar d’in MUSLEEMA taje tasiyo musu hitar d’ari da hamsin da buredin d’ari biyu. Da Lipton na ishirin da sikarin arba’in dake da sauran canji ahannunta na jiya data siya musu abinci saita had’a tasiya musu soso da sabulu harda man shafawa tadawo gidan lokacin akwai wuta. Hajjiya Ladin ce dai tanuna musu yanda ake amfani da hitar har tabasu aran bokatin ta da kofuna. Kafin almajirin data aika ya kawo musu nasun. Dan MUSLEEMA tabata sauran kud’in dan taba almajirin yasai musu bukati d’aya da kofuna uku harda lokali d’aya da buta. Shine taba almajirin yasiyo musu.

Haka YAWO tayi wanka MUSLEEMA ma tayi tayima yaranta. Sannan suka sha ruwan Lipton d’in da buredin.

Suna gama sha ko MUSLEEMA tasaka yaranta agaba YAWO na binsu dama Hajjiya ladi ta had’asu da wani almajiri dan haka nan suka Shiga gari neman ADAMS.
Duk inda sukaje sai ammusu dariya. Wasu su tausaya musu Wasu kuma suga ganganci irin na Yawo data ba ADAMS MUSLEEMA bayan tasan bata san kowa nasa ba bata san waye shi ba.

Haka suka dawo gidan lilis da gajiya. Gajin yunwa gashi basu da ko sisi. Abin gwanin ban tausayi.
Suna gani Hajjiya Ladi tasaka abincinta agaba ta zauna a tsakar gidan tacinye ko kwad’an batayi musu tayi ba. Dan tasan idan tayi musu tayin wallahi ci zasuyi dan tasan sarai yunwa sukeji.
Khalil ya kalli MUSLEEMA yace. “Mama yunwa nake ji. Khalit ma yace “nima yunwa nakeji mama.
Hawaye ya zuboma MUSLEEMA tace.. “Kuyi hakuri Yanxu zan nemo muku abinci.
YAWO ta share hawayan da itama ya zubo mata tace. “Gwara musan yanda zamuyi mu basu abinci MUSLEEMA. Tunkan wannan acicin tatashi kinga dai yanda tayi baccin da kukan yunwar.
“To yanzu YAWO ya zamuyi.
“Muje wajen me abincin nan na roketa tabamu bashi mubasu daga baya masan yanda zamuyi.

Haka ko suka nufi gun Yalwa me saida abinci suka gaya mata buqatarsu har suka qara mata da cewa sace musu kud’insu wani yayi.
Yalwa tayi murmushi tace. “Hmm yanxu idan na baku ya zakuyi anjima.
Kawai dai ga shawara idan kunga zaku iya.
“YAWO tace idan tayi mezai hanamu iyawa
“Yauwa tsohuwa temakwanku zanyi. Kinga ke saiki dinga min wanke wanke da shara. Ke kuma MUSLEEMA saiki dinga zuwa kina bama mazage abinci. Amma cikin nutsuwa yanda zakina jan ra’ayinsu kamar yanda akeyi.
YAWO tace.. “Yanxu idan muka yarda da hakan yaushe zamu samu lokacin dubawa shi LEEKITAN ZUCHIYAN.
Yalwa taja numfashi tace. “Sai MUSLEEMA tadinga zuwa da safe nemansan har zuwa ranah. Daga lokacin da yamma tayi saitazo tajimin da kwastomumina har zuwa sha d’aya na dare.
Idan kun yarda to zan dinga baku abinci safe da ranah da dare sannan zan dinga baku naira d’ari. ammafa ba batun biyanku albashi kamar yanda nake bama y’an aikina duk sati.. Danku nayi muku babban temako ne..
Saidai idan zaman namu ya d’ore nan da wata uku zan iya baku kud’in da zaku koma garin na gwambe
Da sauri sukace mata sun yarda.
Aiko nan tacika musu abinci suka dawo gidan sukaba Khalil da Khalit sukaci Suma sukaci sannan suka ragema Rahma kan tatashi..


Sai rayuwar tasu ta kansance haka. Kullum idan sun tashi wanka sukeyi YAWO tana tasa Khalit da Khalil zuwa gun Yalwa me abinci su hau yimata aiki kamar sauran ma’aikatan nata. MUSLEEMA Kuma tashiga gari neman (ADAMS) LEEKITAN ZUCHIYA..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button