LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Safe da ranah MUSLEEMA neman ADAMS tasaka agaba. Kullum cikin kuka take musamman idan tatambayi wasu mutanan suka sakata a gaba da dariya.
Duk sallar da zatayi addu’a take tana kuka kan Allah ya had’ata da LEEKITAN ZUCHIYA.

Ayanxu dai satinsu d’aya kenan
Yau tun asuba kan MUSLEEMA yake mata ciwo. Lokaci lokaci kuma takanji qirjinta nayi mata zafi musamman wajen da ZUCIYA take amsar sak’o. Haka daddafa tashirya qarfe tara ta fitta kamar yanda tasaba ita da almajirin dake mata rakiyar dan neman LEEKITAN ZUCHIYA.

Sunyi tambayoyin da dama bataci karo da wanda yace ya gane kwatancen nata ba.
Sai kawai tazauna kan wani dakali tad’ora hannu aka tarushe da kuka.
Fad’i take a bayyane. “Meyasa kamin haka Abban Khalit. Meyasa kamin haka baban Khalil. Meyasa kamin haka YAYANA. Meyasa kamin haka LEEKITAN ZUCHIYA.
Kamanta cewar ka b’ata tunanina. Kamanta cewa kadasamin qaunarka azuciyata. Kamanta cewa bana ji bani gani akan sanka da qaunarka.
Meyasa kake wahalar da ruhina. Meyasa kake wahalar da tunanina. Meyasa kake wahalar da zuciyata. Harshena. Gangar jikina. Kafafuna. Ya dace kaji aranka kayi rayuwa dani. Ya dace kaji aranka ina nemanka. Ya dace kaji aranka kana da yara dani. Ya dace kaji aranka akwai wata meyi maka wani SO wanda yafi qarfin akirashi da MASIFAR SO.
Haka tadinga sambatu tana kuka wiwi mutane na kallanta wasu suji tausayinta su tsaya tambayarta idan tayi musu shuru su qara gaba. Wasunsu ko koda sunji tausayin nata basa mata magana suke wuccewa.
Wani tsoho ne ya nace saiyaji abinda yasata kuka haka. Nan tagaya masa. Ya tausaya mata nan ya bata shawara tunda sunan ya had’a dangantaka da likita mezaisa bazataje asibitoci taga ko zata ganshi acan ba.
Aiko taji dad’in shawarar daya bata.
Haka suka dawo gida tagayama YAWO.
Washe gari yawo tabata d’ari biyar irin d’ari d’arin da Yalwa take basu. Haka suka tari kekenafaf zuwa asibitin Aminu kano.
Taci sa’a wata doctor salma taji tausayinta dataji labarinta. Dan haka nan tasadata da hotunan doctors Amman bataga ko me kama da idan Adams ba.
Tunkan tabar asibitin tafara kuka.

Washe gari haka Yalwa ta ranta musu dari biyar ta nufi asibitin murtala. Nan kam tad’an sha wahala kafin wani Dr Ahmad ya fahimceta.
Shima ya nuna mata manyan doctors nanma ko me irin qeyar Adams MUSLEEMA bata gani ba.
Still haka tabaro asibitin da kuka.

Haka akwanakin nan tadinga ziyartar asibitoci amma shuru kake ji.

Haka ta tabari tadena bin asibitocin badan ta hak’ura ba. Saidan babu kud’in zuwa gunsu.
Dan Yalwa tace bazata qara ara musu ko sisi ba. Tunda kud’inta yakai duba biyu da d’ari biyar akansu.
Gashi MUSLEEMAN ba dawowa take da wuri ba. Sai kusan bayan isha. Dan haka idan zata tsaya tayi mata aiki tatsaya tayi mata aiki. Sannan tasan inda zataje ta biyata kud’inta.
Yawo ce tace tayi hak’uri zata dinga dawowa akan lokaci batun kud’i kuma tadinga cirewa aduk rana cikin d’arin da take basu.
Wannan yasa Hankalin Yalwa kwanciya..

Toh MUSLEEMA tadena dadewa wajen yawan neman ADAMS saboda dukar Yalwa.
Saidai yanxu tafara fuskantar wata matsala kamar haka wajen aikin nata.

Idan tazo kawowa Mazajen abinci saisuta kallan qirjinta da qugunta.
Suna janta da hira.
Sam bata san hakan b’cos tana ganin ita matar aure ce.
Duk da cewar hijab take sawa amman hakan baya hanasu qin kallan way’annan abubuwan biyun ba.

Gashi duk da saida dare take dawowa hakan baya hana mazan dake suwa wajen karuwan gidan Hajjiya Ladin binta da mayataccen kallo
Itadai jifansu take da addu’a dan tasan itace makaminta

Dan akwai ranar da wani ya tab’a fad’o musu d’akin nasu yana me san fad’ama MUSLEEMAN haka dai Allah ya kare
Saidai daga ranar suka koyi iya rufe d’akin nasu..


Yau tun safe Hajjiya Ladi tabasu notis kan kud’insu ya qare wata d’ayan da sukayi da ita ya qare dan haka su tashi mata daga d’aki zatasa wata budurwa aciki. Dan gashi tabata kud’inta cif cif dan haka su tattara inasu inasu su qara gaba

Kuka MUSLEEMA tasama Hajjiya Ladi tace.. “Dan Allah ki temaka mana kiqara mana lokaci zamu biyaki kud’inki.
Tace.. “Bazai yuhu ina ganin kud’i ahannu nabar budurwar nan ta tafi da kud’inta bayan ku babani zakuyi yanxu ba
Wallahi Saidai kuyi hakuri inda ace d’akunan basu cika ba dana qara muku lokacin.

Ba irin magiyar dasu MUSLEEMA basuma Hajjiya ladi ba kan ta barsu tace basu isa ba.
Haka suka d’an kwashe kayansu sukaje gun Yalwa me saidai abinci.
Anan Yalwa tace idan sunga zaku iya kwana cikin y’an aikin da suke mata aikatau a shagwan abincin nata to ga waje nan su ajiye kayansu.
Idanko sunga bazasu iya ba. To ita bata da wani waje da zata sasu.
Dan gidanta d’aki d’aya ne tayimai rufi daga shi sai bayan gida ai gashi nan dai sunga gidan ajikin shagwan nata.
Shuru sukayi mata dan a y’an aikin nata harda maza almajirai.
Kuma duk balagaggu ne.
Amma da sukaga gefan matan daban na mazan daban dansu mazan a barandar waje suke kwana. Matan ne aciki Suma irin yaran nan ne way’anda iyayansu suke koransu kai da duhun jahilci ko yaran da basu da yanda zasuyi.

Haka dai YAWO tacema MUSLEEMA su yarda.
Haka suka yarda tunda ba yanda zasuyi.
Sunyi kwana d’aya lafiya lau dai.
Ayau na biyun ne MUSLEEMA tazo kawoma wani alhaji abinci kamar yanda yasaba zuwa kullum ci qarfe tara na dare.. Yana d’aya daga cikin mutanan da suke bin qirjinta da kallo.
Hakan ne yasa ta tsane shi. Harta juya zata tafi ganin ta shirya mishi duk abinda yake buqata dancin.
Sai ya kirata yana tambayarta a ina take kwana.
Kallansa tayi dakyau tana nazarinsa can tace mai miye had’insa da inda taje kwana
Murmushi yayi mata idansa qir akan qirjinta yake bata da cewa. Kawai yana san sani ne. Idan bazata gaya masa ba yaje gun Yalwa tagayamai.
Sanda ta galla masa wata muguwar harara kana tace mai ashagwan taje kwana.
Yaji dad’in hakan sosai dan b’aro b’aro taga ya saki dariya yace mata zai dawo wajenta anjima.
Bata gane me yake nufi dazai dawo d’inba haka tashige abinta ta barsa.

YAWO jikinta kwana biyu babu lafiya komai daurewa kawai takeyi saboda aikin datake bana wasa bane
Hakan yasa yau qarfe goma:pm ta kwanta.
MUSLEEMA ko sai sha d’aya da rabi tasamu kanta.

Qarfe d’aya na dare kowa yayi bacci cikinsu.
Almajiran suna tacan waje suna baccinsu Ammanfa ahakan gadi sukema Yalwa na kaya.
Su Yawo ko suna tacan ciki.
Amma dan tabar shed’ananci haka shegen mutumin nan ya ratsa kowa yaje har inda MUSLEEMA take yahau shafata.
Dake baccin ya fara cin qarfinta sam bata fara jin wani abu ajikinta ba.
Motsinsa ne ya Rahma tashi dake tana kusa da MUSLEEMAN ganin mutumin saita hau jan rigarsa tana mama kitashi ga wani yana tab’aki
Sam MUSLEEMA bataji ba.
Sanda shegen yayi nasarar damke na fulaninta ya fara cirosu tare da daneta iyakar qarfinsa sannan MUSLEEMA tafarka da wata shegiyar qara.
Ai sanda dukkansu suka farka.
Ganin abinda yake faruwa sai Matan sukaja tsaki kowaccensu takoma baccinta dan Wannan su aganinsu ba bakwan lamari bane.
Mazan dake wajen ko tunaninsu d’aya daga cikinsu ne ya afkawa MUSLEEMAN kamar yanda idan wani cikinsu yaji lalurarsa yake afkawa duk wacce yaso amatan kuma komin ihunki saiya biya buqatarsa sannan zai barki.
Toh tunaninsu ko hakan ne. Duk da kowa acikinsu idansa akanta yake. Ganin Yanxu tafara bunqarowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button