LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

YAWO taya MUSLEEMA ihun tayi. Amma sai taga kowa cikinsu ya sharesu.
Nan tanufi inda kayan aikin Yalwa suke ta rarumo muciya aiko tasauke masa a baya.
Lokacin bakinsa nakan san Shiga kan na fulaninta.
Aiko jin hakan afurgice ya saketa YAWO ta qara shinfid’a mai a kafad’a ainan ya taso da zafin nama ya mangare YAWON tazube qasa sannan ya taka hannunta da qarfin tsiya ya fuzze muciyar. Sannan ya qara nufar MUSLEEMA ganga ganga wacce tayi nasarar gyara rigarta. Aiko nan ya kwasheta abinka da ririya. Nan tazube qasa tim. yako bita ruf ya rufeta kamar matarsa yana kici kicin lalle saiya cinmma burinsa akanta.
Kuka wiwi MUSLEEMA take yi tana yimai ihu da yakushinsa da cizansa amma ina burinsa dai yacimma burinsa.

Daqer YAWO ta qara tashi kasan cewar ba qaramar mangare yayi mata ba. Haka tadaure taje ta qara rarumo farantin tangaras ta rutsa masa aka….
Wannan karan yayi qarya wajen cigaba da aiwatar da kudirin nasa Dan haka ba shiri ya tashi ganin yanda kansa yake fitar da jini.
Sanda ya qara mangare YAWO kana ya ficce daga shagwan..
Sai a lokacin almajiran suka gane ba d’aya daga cikinsu bane.

Matan ko mita suka dingama MUSLEEMA wai tashiga hakk’insu ta hanasu bacci miye danta barshi yayi amfani da ita. Ai wannan ba wani abu bane. Amma dan tsabar mugunta ta wani hanasu bacci bayan ba lokaci suke samu nayin baccin ba.
Dan wasu acikinsu da qarfe hud’u na asuba suke tashi d’ora abincin safe.
Tomiye danta barsa yayi abin aina d’an wani lokaci ne.
Ba kunyar YAWO ba jin tsoran Allah haka suka dingama MUSLEEMA Wannan masifar..

MUSLEEMA ko tattara kan y’ay’anta tayi ta rungumesu tana kuka suna tayata abin tausayi.
Itama Yawon hawaye takeyi
Wannan dare dai basu iya rintsawa ba.

Washe gari da kuka MUSLEEMA tace da YAWO.. “Dan Allah yawo mubar wajen nan. Dan suna shirin ketamin hakk’in aureta. Sun kulla aniyar cin mutuncin aurena. Zasu wulaqanta min igiyata.
Wallahi YAWO ina san mijina ina san ya ganni batare da wani yayi masa illa cikin Soyayyarsa ba.
Kimin rai ki amincemin mubar wajen.
“Toya zanyi MUSLEEMA. Ai barin wajen nan ya zamam mana dole dan zan iya jure wahala amma bazan iya jure aci mutuncinki ba.
Jin hakan yasa hankalin MUSLEEMA kwanciya.

Yalwa na fitowa qarfe takwas na safen wata qawarta Hajjiya batula tazo gareta karb’ar kud’inta da wata mata takawo mata jiya danta ajiye mata.
Nan Hajjiya Batula tayi ido hud’u dasu Khalit da Khalil & Rahma.
Nan tagigice ta kalli Yalwa daniyar cewa wani abu saiga MUSLEEMA da YAWO sun iso wajen.
MUSLEEMA ta durqusa da cewa. “Dan Allah Aunty Yalwa kimana hakuri zamubar aiki anan. Saboda abinda ya faru jiya damu… Nan YAWO takwashe komai tagaya mata. Ta qara da cewa “Kiyi hak’uri Yalwa ki yafe mana kud’in da kike binmu bashi wanda bamu qarasa aikin dan biyanki ba.
Nan hankalin Yalwa ya tashi. Danta gane kamar yanda tayi harsashe idan tamallaki MUSLEEMA zata qara samun kwastamomi. Toh haka abin ya kasance. Dan MUSLEEMA nafara bama munan nata abinci saita lura wasunsu jikin MUSLEEMAN ne yake sasu dawowa washe gari ko basuyi niyar dawowa ba. Tunaninsu ko zasu cimma burinsu.
To tayaya zatayi ta rabu dasu haka cikin sauqi. Dan haka cikin b’acin rai ta kalli yawo dakyau tace… “Ke tsohuwa ba inda zaku har sai kunyi min aikin kud’ina. Dan ba haka mukayi daku ba. Tayaya zan ciyar daku da way’ancan yaran naku masu cin tsiya sannan na baku aran kud’i yanxu kuzo kuce min wai inyi hak’uri zakubar aiki nayafe muku kud’ina. To wallahi baku isa ba. Dan sai kunbiyani kud’ina. Saboda lokacin dake kikazo kikamin y’ar murya akan na ranta miki kud’i zakiba MUSLEEMA taje can gari nemo mijinta ba wanda yasani dan haka babu batun hak’uri ko yafiya anan zaku zauna kuyimin aikin kud’ina iyeeee…

Galla mata harara MUSLEEMA tayi da cewa. “Lallema matar nan baki da imani. Kina gani za’aci mutuncin aure. Za’aci mutuncin soyayyata. za’aci mutuncin shinfid’ar mijina amma kike magana akan wai saimun zauna hakan tafaru dan kawai munci kud’inki wanda bai taka kara ya karya ba..
Kallemu sama daga qasa muba matsiyata bane. Qaddara qaddara qaddara ce tasa kika gammu nan cikin garinku gabanki muna sunkuyar dakai dan muyi miki aiki kibamu abin zamuci. Banda haka ba abinda zaisa muyima wata mata kamarki aikatau.
Dan haka kwantar da hankalinki ina dai dubu d’aya ce Yanxu saura kud’in da kike binmu. Zan biyaki kafin fad’uwar rana kwana ne dai bazamu qarayi cikin wannan akurkin naki ba…

Ba Yalwa ba hatta YAWO sanda tayi mamakin maganar da MUSLEEMA tagayama Yalwan. Dan aqalla Yalwa ta haifi MUSLEEMA.

Yalwa gyad’a kai tayi tace.. “Hmm d’an Adam butulu. Tokije duk inda zaki kije ki nemomin kud’ina sannan kizo ki kwashi y’ay’anki da kakarki kubarmin akurkin nawa tunda ke matsiyaciya ce.

Girgiza kai Hajjiya batula tayi cikin jin dad’in faruwar yanayin. Yanxu take da damar dazata cuka maganarta ko zatayi tasiri.
Dan haka salta kalli MUSLEEMA tace “Y’ata zonan ba haka za’ayi ba.
Zo nan kigayamin wacece ke…
Da kuka MUSLEEMA ta qarasa gareta takwashe komai tagaya mata.
Duk da cewar Hajjiya Batula shed’aniya ce sanda ta tausayama MUSLEEMA. Saidai duk da haka zataso burinta ya cika akan yaran MUSLEEMAN dan haka saita kalli YAWO tace…
“Ayya ai mutanan kirki sun mutu a garin Kano. Dakin sani daba nan kike nufo ba.
Sannan gaskiya Baba kinyi kuskuran bama shi LEEKITAN ZUCHIYAN jikarki MUSLEEMA.
Yanxu shawarar dazan baku d’ayace. Shine zai iya yuhuwa shi direban ba garin kano ya kawosa ba.
Dan haka ku canja gari ko Allah zaisa ku dace.
Amma idan kunga zaku iya bina ni ina garin KADUNA ne da zama. Kuma kunga zai iya yuhuwa direban garin kaduna yayi dashi ba nan garin kano ba.
Tunda kunga duk hanyar d’aya ce.
Idan kun yarda dama ni nazo nan Kano siyan kaya ne jiya. Idan kunga ba damuwa kuzo muje garin Kadunan kuyi sati d’aya a gidan nawa lokacin kun huta. daga nan saiku fara neman LEEKITAN ZUCHIYAN. Tunda kunga likitocin zuciya sunfi yawa a garin Kaduna. Ina kyautata zatan zaku samesa acan d’in
Kunga shikenan saina bama Yalwa kud’inta wannan na bata fisabidillahi ne na temakeku.
Saidai zaku dinga min aikin gidana har lokacin daza kuga LEEKITAN ZUCHIYAN shikenan fa idan kun amince. Danni nayi niyar temakwanku ne tsakani da Allah ganin likitocin zuciya sunfi yawa a garin na Kaduna…
Ai dajin hakan MUSLEEMA tace. “Na amince Aunty Allah yasaka. Haka YAWO mah tace ta amince.
Jan numfashi Hajjiya Batula tayi da cewa. “To kuje ku had’a kayanku da kan yaran ga motata can kusaka kayanku kafin na gama da Yalwan.
Aiko kicin jin dad’i suka koma ciki dan aiwatar da abinda tace musu.

Yalwa takalli Hajjiya Batula tace “Nasan dai badan Allah kike san zuwa dasu garin na Kaduna ba.
Tace “Eh magana ta gaskiya naga yaran MUSLEEMAN zasuyi daraja da yawa ne.
Sannan daga ganinsu basu da hankali.
Banda haka me zaisa kakar tata tabama wanda bata san daga Inda ya fitoba jikarta. Sannan dan rashin dabara sukama suzo garin kano batare da sunsan inda zasu dosa ba.
Kawai magana ta gaskiya anan naga zanyi kud’i sosai da yaran nan idan na siyarma da Ahaji bala su.
Murmushin mugunta Yalwa tayi da cewa.. “Dan Allah albarkacin rashin kunyar da MUSLEEMAN tamin ina rokwanki da ALLAH kuna zuwa kisa a fiffille musu kai????
Dariya Hajjiya Batula tayi da fad’in.. “Kai Yalwa baki da mutunci. Ai ki kwantar da hankalinki tunda sukacemin su fulani ne naji na tsanesu. Kin manta kishiyata bafulatanace ta kwacemin miji. Aitun daga lokacin natsani duk wani bafulatan mutum dan babu mugu kamarsa.
Yanxu dai ga dubu ishirin kiyi harkar gabanki da ita.
Idan mun had’u na qara miki wani abun koda yake kema ai kin kusa fad’owa hannu adinga damawa dake.
Yalwa tace. “Eh duk da haka wallahi baki isa ba. Koki bani duba hamshin ko yanxu na tona miki asiri agunsu.
Sanin halinta shiyasa Hajjiya Batula qara mata sukayi sallama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button