LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Motar tata kad’al idan ka kalla ta’isheka tabbatarwa Hajjiyan me kud’ice.
Cewa tayi MUSLEEMA takoma gaba tabar YAWO da yaran a baya zasufi sakewa.
Aiko hakan MUSLEEMA tayi.
Hajjiya Batulan tashiga mazaunin direba tajasu da gaske garin na kaduna tanufa dan acan d’in gidan nata yake…
By AUNTYN LUV????????????
[7/26, 1:00 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R ®
http://hausafulaniwriters.blogspot.com
” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 24☆
Sun d’an sha tafiya sannan suka iso wani katafaran gida.
Tun daga bakin get YAWO da MUSLEEMA sukasan hajjiyan tajik’u da naira.
Nan ma’akatanta biyu mata suka hau zube mata suna masu yimata Barka da dawowa.
Tunda MUSLEEMA da YAWO suke aduniya basu tab’a zatan zasu Shiga gida irin wannan ba. Duk da cewa bawai gidan ya taka kara ya karya bane. aa gida ne dai me kyau amma ko kwatan kwatan kyau baiyiba a irin jerin gidajen masu kud’i.
Yanxu dai gasu afalan gidan sai raba ido suke inda ɗaya daga cikin masu aikin takawo musu abinci me rai da lafiya.
Shinkaface da miya da had’in salat da nama manya manya. Ga drink da ruwa susha duk wanda sukaga dama.
Haka sukayi nak Hajjiya Batula takallesu da murmushi tace bara tayi musu jagora I zuwa inda zasu dinga kwana.
Da murmushin godiya sukabi bayanta har takaisu wani d’aki me kyau da tsari.
Gadone lafiyayye ad’akin da durowarsa sai toilet. d’akin dai ba lefi yayi kama dana saukar baqi.
Haka su MUSLEEMA sukayi sallah tayima yaranta wanka da canja musu kaya suka d’an kwanta saboda gajiya.
Basu suka tashi ba saican kusan magrib. Haka sukayi salati da godema Allah daya kawosu hannun wannan mata me kirki. Dan tunda suka baro Rugar malam jauro basu tab’a baccin kwanciyar hankali cikin lokaci kad’an haka ba.
Haka da sukayi sallar isha haka me aikin nan taqara basu abinci har cikin d’akin da suke.
Sukaci suka qoshi kamar d’azu suka qara meqewa suka kwanta.
Sam Hajjiya Batula Bata bi takan su cikin daran da udirinta ba. Saboda tana so susake da ita tayanda zata aiwatar da udirin nata da hikima.
Haka yasa tadinga kyautata musu. Ba dare ba ranah harna tsawan sati d’aya kamar yanda tagaya musu saisun huta saboda jikin YAWO da bata jin daɗinsa kana saisu fara fitta neman ADAMS dan idan suka fitta ne take da damar cimma burinta akan yaran.
Ayau d’inne kwanansu bakwai dan haka sai murna Hajjiyan take tana Allah Allah gobe tayi dan agoben ne su MUSLEEMA da YAWO zasu fara fitta neman ADAMS LEEKITAN ZUCHIYAN nasu.
Hafsat sunan d’aya daga cikin y’an aikin Hajjiya Batula itace taji tausayin su MUSLEEMA data nemi yau subata labarinsu sukako bata.
Taji tausayinsu matuqa musamman ma datasan k’udirin Hajjiya Batula akansu.
Saboda itace idan hakan tafaru ma’ana idan Hajjiyan tazo da mutane irinsu irin hakan. itace take jan hankalin yaran takaisu can bayan gidan Hajjiyan wajen wata k’ofa da aka fitar da yaran da Hajjiya Batulan take siyarwa. Sai wani alhaji bala yasa yaran amota yayi gaba dasu. Shikenan duk bala’in duniya da za’ayi yaranka sun tafi kenan. Dan ita Hajjiya Batula zata nuna ai tana tare daku masu y’ay’an. Kawai dai yaran sun fitta waje ne wasu suka sacesu. Dama garin Kaduna ai garin mayune.???? yanxu ne dai abin yayi sauqi.
Ahankali Hafsat ta kalli YAWO da MUSLEEMA tace dasu.. “Zan gaya muku wata gaskiya saboda yanda naji tausayinku araina. Hak’ik’a da kunsan wajen wacce kuke hannunta ayanzu. da baku yarda kun biyota ba.
Hajjiya Batula wata shahararriyar shed’aniya ce. Bata da aiki saina sato yaran mutane tana saidama manyan mutane suna kud’i dasu.
Ta gayamin gobe zaku fara fitta neman LEEKITAN ZUCHIYA dan haka agoben naja hankalin yaranki ke MUSLEEMA nakaisu wajen Alhaji bala.
Idan kuka dawo sai nace muku ai kuna fitta yaran suka saka kuka shine na bud’e musu get suka biyo bayanku dan atunanina tunda naga bakuyi nisa ba nasan zakuji motsinsu a bayanku. Kai batama yanda za’ayi kuna fitta na bud’e musu get kuce baku gansu ba..
Idan kunqi gamsuwa da wannan hujjar Hajjiya Batula tasan abubuwan da zata gaya muku dole sai kun yarda kun gamsu yaranku b’ata sukayi. Sannan zata b’ata muku tunani wajen yad’awa gidajen rediyo da talabijin wajen cikiya sam bazaku kawo cewar itace tasace muku yara ba.
Idanfa kuncire zoton ba itace tasace muku y’ay’aba. Idanko kunsaka mata gaba kan itace tasace muku y’ay’a Wallahi makaku zatayi agun bokanta ya rufe muku baki.
Waro ido waje???? MUSLEEMA tayi jin abinda Hafsat ke faɗi.
Ai ba shiri tararumo yaranta ta rungumesu cikin matuqar tsoro kamar ance mata yanxu ne za’a rabata da yaran.
Cikin kuka ta kalli Hafsat d’in tace.. “Yanxu ya za’ayi mu ficce daga gidan nan. Wallahi ina san yara na ina san yaruwa dasu ina san ubansu ya gansu ina san rayuwa dasu da ubansu.????
Jan numfashi Hafsat tayi da cewa. “Agaskiya yanxu kuna cikin bala’i. Saboda yanxu kuna tashi kuna cewa zaku fitta daga gidan nan da yaran nan wannan saurayin me bama fulawa ruwa bazai tab’a barinku kufitta ba. Dan yasan nufin Hajjiya akanku.
Nan zaiyi babakere a get yace saiya kira Hajjiya idan tace abarku ku ficce toh. Idan yaji sab’anin hakan bazai barku ba.
Kuma Hajjiyan na zuwa farko tambayarku zata farayi mezaisaku tafiya batare dakun gaya mata ba.
Daga lokacin da kuka fara mata kame kame daga wannan lokacin kunjefamu nida abokiyar aikina a bala’a.
Saboda zatace mungaya muku wani abu Wallahi daga yau mumbar numfashi aduniya. Dan kashemu zatasa ayi.
Saboda da mu uku ne masuyi mata aikin. Sai d’aya data gane me take aikatawa saita gudu garinsu dan acewarta a imani irin nata babban kuskure ne dasa hannunta adinga kashe yaran mutane.
Wallahi ina gaya muku har garinsu Hajjiya Batula tasa wasu sukaje suka kashe Balkisu bazamu tab’a mantawa ba dan agabanmu tayi waya tana jinjinama way’anda sukayi kisan. Sannan taja kunnanmu wai muma idan muka fad’ama wani abun da takeyi bama muba har iyayenmu saitaga bayansu..
Wallahi nima raina basan wannan aikin yake ba. Lokuta da dama idan ina aikatawa kuka nakeyi cikin dare kan Allah ya fitar dani daga gidan nan lafiya????
Dan ni aikin su wanke wanke nazo mata kuma haka iyayena suka turoni nayi. Saidai basu san abinda nake aikatawa ba. Hafsat takai qarshen zancenta da zubda hawaye
Goge gumi YAWO tayi da tashi arikice take cewa. “Bar kuka y’arnan yanxu ba lokacin kuka bane. Innalillahiwainna’ilaihirraji’un.
Wannan ba gidan zama bane. Keko yarinya meyasa baki fad’in mana hakan tuntuni ba.
Goge hawayenta Hafsat tayi da cewa.. “Kwantar da hankalinki YAWO zan fitar daku daga gidan nan ta k’ofar da ake fitta da yaran da take satowa. Amman sai cikin dare yayin da qafa ta d’auke.
Dafatan kingane.
“Nagane y’ar nan.
“Toh yanxu kusake karku nuna kunsan wani abu bare tagane.
“Insha Allah bazamu nuna wani abu wanda zaisa ta ankare damu ba. MUSLEEMA tagaya mata hakan da qara qanqame yaranta.