LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Godiya sosai YAWO tama Hafsat. Kana Hafsat d'in ta fitta daga d'akin nasu cikin sand'a takoma nasu. Kasancewar tara har da rabi tayi:pm.
Su MUSLEEMA ko sam basu kwantar da haqarqarinsu ba. Dan tsoro ya cika zuciyarsu. Haka suka had’a kayansu gefe d’aya jira kawai suke dare yayi Hafsat tayi musu dagoran fitta.
Har qarfe biyu na daran idansu qir yake. Rahma na bayan yawo. Yayin da Khalil yake bayan MUSLEEMA. Haka d’auki Khalit ma tarungume duk da sun fara nauyi da wayo. ita dai awannan lokacin bataji nauyinsu ba.
Aiko Ahankali Hafsat tatuto ƙofar tasu tayi musu nuna da hannunta su biyota.
Cikin sanda haka Allah ya basu sa’a suka ficce ta k’ofar da Hafsat tagaya musu.
Sanda suka fitta. YAWO takama hannun Hafsat tace “Yanxu bazakizo mu gudu dake ba.
Murmushi Hafsat d’in tayi da cewa. “Kiyi hakuri YAWO nafiki san nabar gidan nan. Ina san iyayena araye wannan yasa nake har yanxu agidan. Indai addu’a na magani insha Allah zan fitta daga gidan.
“Tome yasa bazaku kai qararta gun hukuma ba. MUSLEEMA tace da Hafsan hakan
Murmushi Hafsan tayi da bata amsa da.. “Wata rana wani mutum ya tab’a zuwa da y’an sanda yace tasace miki d’a. Haka tarufe idanta tace ita bata sace mishi d’a ba.
In takaice muku tunda tamaka mutumin akotu wai yayi mata qage da sharri akan abinda bata jiba bata gani ba. Har yanxu yau kusan shekara biyu kenan ba’a sake mutumin ba. Yana can gidan yari ana ganamai azaba.
Kudai Allah ya temake ku sai kuyi Maza kuqara gaba. Dan yanzu lallabawa zanyi na mayar mata da kin k’ofar nan karta gane.
Ga number na wata nasan wata ranah zaku nemeni.
Karb’a MUSLEEMA tayi.
Sannan YAWO tayi mata godiya sosai suka d’auki hanya. Ita kuma Hafsan takulle ƙofar da komawa cikin gidan da sand’a
Sam su MUSLEEMA basu san inda suke jefa qafarsu ba. Sudai saibin titi suke suna tafiya da addu’a.
Ahaka sukaga wani layi suka Shiga. nan sukaga wani gu da alama wajen me saida balangu ne. To wajen yad’anyi duhu anan suka shinfid’a zaninsu suka zazzauna da rungumar yaran dansu bacci ne a idansu.
Har aka kira sallar asuba idansu YAWO garau yake.
Suna ganin mutane suna wuccewa zuwa masallaci har aka sauko akan idansu.
Haka sanda gari yayi haske har mutane sun fara yawa sannan suka tashi daci gaba da tafiya.
Rahma ce tasa musu kuka ita abata abinci.
Nan suka tsaya wajen wata mata me saida koko da k’osai. YAWO ta durqusa taroketa taba yaran kokon da k’osai d’in basu da kud’i idan tana buqatar sumata aikin kud’inta zasu mata.
Kallansu sosai matar tayi kana ta tab’e baki tace Nanawa zata basu
YAWO tafad’a mata sannan tabasu. Haka suka ibi ruwa a gun matar suka wanke musu baki da burushinsu da makilin Suma suka wanke nasu. sannan suka ba yaran koko da k’osan kana suka roketa dan Allah tanuna musu gidan da zasu Shiga suyi salla.. Daqer matar tanuna musu wani gida ba nata ba. Dan bataji aranta tayarda dasu ba.
Matar gidanku me kirki kuwa. haka tabasu ruwa sukayi sallar sannan suka fitto lokacin harsu Rahma sun gama cin k’osan da kunun.
Sai suka tambayi matar wane aiki zasu mata na kud’inta.
Tace ita kawai tabasu dan Allah ne. Dan haka su d’auki yaransu su qara gaba. Haka suka mata godiya suka tasa yaran agaba suka fara tafiya suna tambayar mutane LEEKITAN ZUCHIYA..
“Dan Allah malam katemaka idan kasanshi. Sunan damu muka rad’a mishi shine Ahmad. Amman sunanshi na Ainihi LEEKITAN ZUCHIYA. Ance mana likitocin zuciya sunfi yawa anan garin na kaduna ne shiyasa mukazo ko Allah zaisa adace. YAWO tafad’ama wani mutum hakan da suka taresa..
Kallansu yayi a nazarce kana yace.. “Gaskiya ban sanshi ba. Kuma garin kano yafi cikin garin nan likitocin zuciya. kawai wanda ya gaya muku ya fad’in muku hakan ne danya baku wahala.. Yana fad’a mata hakan ya wuccesu.
MUSLEEMA ta zauna kan wani d’an dandamali anan kan titi bakin wani layi tana me kallan YAWO tace da ita. “Wallahi nagaji YAWO. Yunwa nakeji. Gashi qirjina zafi yake min. Yana min wani abu kamar soya haka ga zafi kamar ZUCIYATA zata fitta….
Itama Yawo zuwa tayi gefanta tazauna yaran suka tsaya gabansu tace. “Hak’uri zakiyi MUSLEEMA mu qara gaba ko Allah zai had’amu dame saida abinci kici ko yunwace
Shuru MUSLEEMAT tayi. jin yanda yanxu gabanta ya shiga bugawa fat fat fat… Aiko dai dai lokacin ADAMS ya faka motarsa agefan titin. Amman tatsallakensu MUSLEEMAT d’inne. Yana tare da Yusuf ne Wanda yaje har office d’insa ya d’aukosa dan ya duba masa kakarsa Hajjiyansu. Yusuf d’in yayi yayi da ita Hajjiyan nasu kan tayarda yakaita asibitin kamar yanda ya saba kaita tace ita sam yau batasan yakaita yaje dai ya d’auko mata ADAMS d’in tasan zaibar duk abinda yake yazo ya dubata ai.
Shine fa Yusuf yanxu yaje yasa ADAMS d’in agaba kan suje ya dubata.
Ahankali ADAMS ya kalli Yusuf yace.. “Kayi hak’uri d’an uwa. Yau dai d’aya na tsaya gefan titi dan amsa waya.
Murmushi Yusuf yayi da cewa.. “Haka tsarin yake ai. Dama ai ganganci kakeyi da kake d’aga waya kana tuqin. Fatana dai Allah yasa ba maiyarka bace takiraka taja mana lokaci.
Murmushi ADAMS yayi da cewa “kamarko kasan Ita d’ince. Yafad’a yana me d’aga wayar daci gaba da cewa… Ina cikin k’oshin lafiya my luv.
NUFAISAT dake tsaye a kitchen d’inta tana yanka kub’ewa dan yau ADAMS d’in yace mata tuwo yake san ci da ranah. kasancewar yau itace dashi ma’ana tashiga girkinta.
Ajiye wuqar dake hannunta tayi tare da tab’e baki tace.. “Nasan kana cikin k’oshin lafiya mijina. Tunda tunkan kafita nake binka da addu’a. Kuma nasan bazata fad’i qasa banza ba. Kawai haka kawai naji gabana yana fad’uwa yanxu. Shine na kira ka dan naji lafiyar zuciyarka. babu mamaki ko zuciyar taka tana dab da karb’ar wani saqo ne shine nake san jan kunnanka dan Allah karka bari ta amshi sakwan soyayyar wata y’a mace…
Hak’ik’a ADAMS yana jin NUFAISAT da kalamanta amma idansa nakan MUSLEEMA yana me qare mata kallo from up down. Kallo na qurilla. Tunda idansa yakai kanta wasu jijiyoyi acikin kansa sukaso fara aiki. Saidai dake yana jin muryar NUFAISAT d’in sai hakan yaqi ba jijiyoyin damar aikin yanda ya dace.
"Kamar nasanta.
Ya faɗi hakan a bayyane batare da yasan ya fad’i ba
Cikin nutsuwa NUFAISAT tace.. “Ita wah????..
Ahankali yacire wayar tashi daga kunnansa yamaida kallansa kan wayar.. Shi sai yanxuma ya tuna Ashe waya suke da NUFAISAT. Dan haka cikin sauri ya maida wayar kunnasa da cigaba da cewa. “Kiyi hak’uri my LUV na Shiga wani yanayi ne.
Waro ido???? NUFAISAT tayi da cewa. “Na Shiga uku ni NUFAISAT. Kardai har zuciyar taka ta karb’i sakwan.
Murmushi ADAMS yayi da faɗin. “Kwantar da hankalinki matata. Dan ba wani sak’o da zuciyata zata karb’a imba naki ba.
“Naqi yarda da abinda kace min a wannan lokacin. B’cos baka tab’amin qarya ba.
“Haka ne my LUV. Kuma bazan fara miki yau ba. Zan gaya miki idan nadawo gida.
“Yanxu bazaka gayamin ba.
“Muna kan hanya ne nida Yusuf zanje duba Hajjiyansu. Pls ki barni kar kisa kaina ya kulle na kasa komai dan Allah.
Murmushi tayi da cewa “Kanka bazai kulle ba mijina bare yasaka kasa komai. Na Barka saika dawo luv u.????
Murmushi kawai yayi da ajiye wayar ya qara maida kallansa ga MUSLEEMAT tare da tab’a Yusuf wanda yaketa danne dannan waya yace dashi… “Kaga wata Baby mekyau????????. Nutsu dakyau ka qare mata kallo tatara duk wani abu damu maza muke buk’ata agun mace..
Murmushi Yusuf yayi idansa nakan MUSLEEMAT d’in yace. Saidai hannunta na dafe da zuciya.
“Eh nanma na lura kamar tana da matsala da zuciyartata. dan idan kaqara kallan gefan wiyanta dakyau zakaga alamar tashin wata jijiya wacce nake kyautata zatan akowane lokaci ciwan zuciya zai iya kamata. Dan wannan jijiyar alamace tafara bayyanar ciwan