LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Jan numfashi Yousuf yayi da cewa “Wai dama waya kakeyi d’azu ko kallan yarinyar mutane. Dan naga kayi saurin gane komai atare da ita cikin lokaci k’ank’ani..
Murmushi ADAMS yayi da bashi amsa. “Kasan ko’a skull nafika gane abubuwa cikin sauri. Kuma karkace na shagala da yawa. Dan kasan san mata ba d’abi’ata bace.

Juyowa Yusuf yayi yana harararsa da cewa. “Wato magana zaka gayamin.
ADAMS ya qara yin murmushi da cewa. “Harma na gaya maka mai ai. In banda iskanci kasan dai neman mata baya gabana
Kaine dai wahalalle daka dami zuciyarka saika had’u da wacce tacika sharid’anka..
“Naji dan Allah. Wannan d’inma dan tayi yarinya ne. Bazata isheni watayawa da yaw ba. Da Wallahi yau saina baka kunya na nemeta da aure in kashe bakin gorin da kakemin akoda yaushe.

Tada motar ADAMS yayi yana cewa. “Dako ka huta wallahi..
Daidai nan kamar ance MUSLEEMA tad’ago kanta saiko tasauke akan gefan fuskar ADAMS…

Azarane tatashi har tana mangare Khalit dake gabanta ta kwalla ihu tana nunama Yawo ADAMS faɗi take “Wallahi shine. Shine YAWO. Shine acikin motar can.
Wani saurayi ne yazo wucce yaji abinda take fad’i. Sai ya kalli motar ADAMS dake tafiya ya dawo da kallansa kan MUSLEEMA da galla mata harara yace.. “Shine wah.
Da sauri MUSLEEMA ta qarasa gun saurayin tace. “Shine mijina Wallahi mujina ne dan Allah kasan shi ne.

Kallan raini yayi mata da qare mata kallo daga sama har qasa yace. “Gaskiya ke y’ar rainin hankali ce. ADAMS LEEKITAN ZUCHIYA ne mijinki. Ke kinsan waye shi afad’in garin nan kuwa. Wani babban mutum ne me arziqi. Gashi Doctor gashi d’an kasuwa. Kafin ki gansama kuzanta sai kina da hanya. Dan yau baki gansa da masu tsoro ba shine zaki wani ce mijinki ne. Mijinki a ina kina kicaka dake haka. Dubeki fa kamar wata almajira. Ke idan kikaci karo da Matansama kikace ke matarsa ce wallahi sai sun sa and’aureki d’aurewar dahar ki mutu bame kunceki. Shashasha wawiya almajira kawai…
Ai MUSLEEMA bataji qarshen zancensa ba hannunta dafe da k’irji tafad’i sumammiya sakamakwan qara ganin motar ADAMS da tayi tana nufosu..
Dama zagawa ADAMS yayi da motar tashi dan cikin layin dasu MUSLEEMA suke zaune zai Shiga kasancewar nan ne layinsu Hajjiyansu Yusuf d’in da suke san zuwa dubata.

Jan tsaki saurayin yayi da wuccewarsa abinsa yana tafiya yana sambatu daga ganinsa kasan akwai abinda yake damunsa kamarma dai abuge yake.

Hankalin YAWO ya bala’in tashi. Nanta jawo MUSLEEMA jikinta tana mata fifita da fad’in. “Ki tashi MUSLEEMA kinga halin da muke ciki dan Allah ki tashi.
Dai dai nan ADAMS ya qaraso da motarsa dan yin kwana ya Shiga layin. Ahankali ya tsaya da motar tare da zuge gilashin b’angaransa ya kalli YAWO da cewa.. “Sannu Baba meyasameta.
Ai da sauri YAWO takallesa tana had’a ido dashi tunaninta ya tsaya cak….
San da ADAMS ya qara maimaita tambayarsa Sannan tunaninta ya dawo. Hawaye ya zubo mata tace dashi. “Yanxu tafad’i d’an saurayi. dan Allah katemaka min ita kenan gareni..
ADAMS ya kalli MUSLEEMA dake hannunta kamar bata da rai. Kana ya kalli yaran nata da suka zuba musu ido shida Yusuf. Saiya fitta daga motar Yusuf ya biyo bayansa. Ahankali ADAMS ya d’auki MUSLEEMA Yusuf ya bud’e mai gidan baya yasata.
Sannan ya kalli YAWO da cewa. “Kushiga muje asibiti.
Da sauri yawo tashige ciki da yaran. Yusuf ya koma wajen zamansa yana cewa. “Mujuya kawai adubata ma dawo ka duba Hajjiyan namu..
“Toh. ADAMS yace mai jiki babu kwari dan haka kawai yaji jikinsa ya mutu da ganin yaran MUSLEEMA.
Shi idanma idansa ba gixo yake masa ba zai iya cewa yaran na kama dashi.

Shima Yusuf yaga kamar amma sam wani abu bai dirsu a zuciyarsa ba.
Suko yaran kallan ADAMS kawai suke zuciyarsu na raya musu ayya basu san wannan mutumin ba.
Yawo ko gabanta fad’uwa yashiga yi. Yayinda hankalinta duk ya tashi da ganin Adams d’in. Dan ganin ya qara kyau sosai. Ga wani kwarjininsa daya maketa. Ita tsoroma taji tace tasanshi bare har takaita da cewa ya Auri jikarta harda yara uku. Wayyo Allah ya kawo mata sauki cikin lamarin..

Awannan lokacin TAUDHAT na tare da malamin nata sun gama tsula tsiyarsu. Dan cema ADAMS tayi ya sauketa agidansu tana da maganar da zatayi da mamanta.
Toh shinefa daya tashi fitta office d’azu da safe ya sauketa.

Shine yana tafiya tayi wajen malamin nata karb’ar maganin mata. Shi kuma yace mata saiya jita.

“Dan Allah kamin had’i na musamman. Dan naga kan ADAMS bai dena rawa akan NUFAISAT kwanan nan ba. Ka duba yau zai Shiga girkinta sai wani nishad’i yake. Ina jinsafa yana cemata tayi masa tuwo ta turamai office shi zaici yau da ranah.
Kumafa karka manta idan da nice nayi masa tuwo sam bazaici ba.. TAUDHAT ta fad’inma malamin nata hakan da damuwa.

Murmushi malamin nata yayi da shafan gefan fuskarta yace.. “TAUDHAT kina da futuna. Nina rasa me kike gani agun wannan kishiyar taki da kike kishi da ita.
“Kai bazaka gane bane. Yanxu dubamin kaga me yake tafiya a tsakaninsu.
“Toh.. Yace mata da wargaza qasarsa yana Zane Zane cikin gwanancewa.
Can ya d’ago ya kalleta a furgice. Sai kuma yaci gaba da zane zanen nasa.
Sanda ya gama tsaf ya ture farantin qasar tasa gefe yace da ita.. “Tabd’ijan.. Lalle ambar baya da qura..
“Ban gane me kake nufi da ambar baya da qura ba.

“Ina nufin NUFAISAT da ADAMS ba wani abu na tashin hankali agaresu. Qara san junansu suke kamar yanda kika sani.
Baya da quran da kikaji nafad’i ko shine Wallahi ga wasu yara nan kyawawa na mijinki ADAMS har uku. wata qaramar yarinya ce tahaifa masa su. sam shi bai samma yaransa bane..
Haka ita yarinyar ayanzu bata cikin hankalinta.

???????????? Inda ace kawunan TAUDHAT uku ne ba shakka da saita waro dukka idanunta dasu.
A razane. A furgice. A haukace tadafe qirji da cewa.. “Kutumar uba. Ban gane me kake nufi ba. Ka fahimtar dani na fahimta. Wallahi kwakwalwata ta hautsine.. Isma’in ina san nayi haukafa..

“Ki kwantar da hanlinki yanxu ki koma gidan naki ki gano mana komai. Danni nayi bincike akan nasan komai. Saidai banga komai d’in ba. Yanxu saikin gano mana wani abu zan iya baki haske.
Da sauri TAUDHAT tatashi da saka kayanta ta d’auki yajarta ko sallama batayi masa ba taficce daga d’akin nasa hankalinta amatuqar tashe…

???????????????????? na gaida y’an hannuna

[7/28, 4:18 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

http://hausafulaniwriters.blogspot.com
” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 25☆

Koda ta iso gidan bataga kowa ba alamu sun nuna ba wani ma abinda ya faru. Nan takira malamin nata tace bataga kowa ba. Yace tabari Adams d’in ya dawo tukunna…

Su ADAMS ko bayan sun isa asbitin duba MUSLEEMAT yahauyi. Inda ya tabbatar tana d’auke da ciwan zuciya. Sosai yashawo kam matsalar yana me mamakin yanda tana qaramar yarinya haka takamu da ciwan ZUCIYAR

Ahankali ya kalli yawo dace mata. Bara suje ya duba kakarsa. Yana nufin Hajjiyansu Yusuf.
Bayan sun dawo ne yana zaune kan kujerarsa a office d’insa sai kawai ya shiga tunanin meyajama MUSLEEMA ciwan ZUCIYA tana qaramar yarinya haka.
Shuru yayi dajan numfashi ya kira ma’aikaciyarsa yace takira masa kakar yarinyar daya duba d’azu. Cikin ladabi ta amsa mai da kiran YAWO.
Bayan YAWO tazauna ya kalleta anutse da cewa.. “Baba ina san nasan sunanki.
“Sunana YAWO..
“Wannan yarinyar dana dubata y’arki ce ko jikarki.
“Jikata ce.
“Ina iyayenta.
“Atakaice dai yanxu ita marainiyace. Danni yara biyu gareni. Rahma da Musa. Kuma duk na rasasu. Yazu haka dai ita kad’ai taragemin da yaranta.
Waro ido ADAMS cikin mamaki yace da ita. “Kina nufin way’ancan yaran ita ta haifesu.
YAWO ta d’aga mai alamar tabbatarwa hawaye na zubamata tace. “Y’an uku ne su. Wata ranah wani yazo rugarmu da matsalar d’aukewar tunani. Ita ce tafara ganinsa. Sai me rugar nawa yasa d’ansa doctor yayi mai binciken lafiyarsa. Bayan yagane yasamu d’aukewar tunani. Sai muka saka masa suna Ahmad kasan cewar bamu san sunansa da inda ya fitto ba.
Bayan d’an me Rugar namu ya dawo dashi daga asibitin nashi. Sai jikar tawa tanuna qauna agareshi. Zai zauna wajen me rugar tamu. saitace ita tana san nakawosa gidana yazama yayanta.
Haka na yarda da abinda tace dan baqaramin so nake mata ba.
Ahaka ahaka soyayya tashiga tsakaninsa da ita. Taqi wanda suke da alk’awarin Aure. Tace shi take so. Nan banyi cikakken tunani ba. Banyi tunanin bansan daga inda ya fitoba. Banyi tunanin waye shi ba. Banyi tunanin ko sunansa bamu sani ba. Kawai saina duba nutsuwarsa da kyawun halinsa. Da ladabi da biyayyar da yake min. Kawai saina aura masa ita. Watansu tara tasamu ciki. Shine tahaifi way’annan yaran y’an uku.. Bayan wasu lokaci sai wanda yake da niyar Auranta dafarko wanda suke da alqawarin Aure dashi saiyaja shi wannan mijin nata daji ya makeshi da sanda.
Anan dai muka nemesa muka rasa..
In takaice maka shidai wanda ya makesan shine wanda yazo ya bamu labarin shine sanadin b’acewarsa.
Shine mukaxo garin kano nemansa dan nan yace mana ya turasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button