LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaban ADAMS ne ya fad’i sakamakwan tunanin dayazo masa kwakwalwa amma danya tabbatar da tunanin nasa saiya kalleta a nazarce yace da ita.. “Yanxu ina ne rugar taku.
Kallansa yawo tayi da tunanin tagaya masa gaskiya ne kodai tad’an jinkinta taga iya gudun ruwan lamarin. Gaskiya ita tsoran ADAMS takeji. Sam bata tab’a tunanin ganinsa da zatayi akaro na biyu zai kasance mata haka me matuqar kwarjini da kamala ba. Idan tace zatayi saurin gayamai lamarin qila yaqi yarda da ita. Koma yayi mata wata fassarar. Gaskiya bazata gayamai yanxu ba. Saidai zatasan yanda zatayi su rayu dashi. Daga nan idan ya fara sakewa dasu saita gaya mai gaskiyar lamarin.
Dan haka gyara nutsuwarta tayi da cemai. “Rugarmu nacan garin JOS basa.

Jan numfashi ADAMS yayi da cewa. “Gaskiya kinyi kuskuran bashi jikarki bayan kinsan baki san daga inda ya fito ba.
Sannan kuskure na biyu da kikayi shine na baro Rugarku da kukayi kuka fito yawan nemansa.

Yanxu dai ina buqatar sanin wata damuwa ce tasa ita jikar taki shiga cikin wani hali dahar ya haifar mata da ciwan ZUCIYA haka…

“Sanshi da qaunarsa ne ya haifar mata da hakan. Tana matuqar sanshi da qaunarsa. Dan kowane lokaci zancenta shine. Kullum cikin kuka take.

Jan numfashi ADAMS yayi da cewa “Toh nidai yanxu nayi niyar temakwanku. Inasan naji wane irin temako kikesan nayi muku.
“YAWO tashere hawaye cikin matuqar Farin ciki tace.. “Kayarda damu kan bazamu cuceka ba. Kakaimu gidanka matsayin y’an aiki ga matanka. Sannan dan Allah kabama yaranta kulawa kamar kaine mahaifinsu. Dan bani san sutaso da rashin soyayyar mahaifi agaresu.

Shuru ADAMS yayi da tunanin shi tunda yaga yaran qaunarsu tashigesa. Gaskiya wannan karan saidai Dadynsa yayi hak’uri dashi yabarsa ya raini yaran daba nasa ba.

Ahankali yace da ita. “Indai wannan ne insha Allah bazai zama da matsala ba. Zan nemi amincewar mahaifina yanxu naji tabakinsa. idan ya amince min shikenan.
Godiya YAWO tamai sosai..
Anan yakira Dadyn nasa a waya yace dashi. “Dan Allah Dady kamin afuwa ina san rainan wasu yaran wata yarinya da kakarta. Ina san basu kulawata. Dan Allah Dady karkace aa.
Shuru Dady yayi. Lokacin yana wajen shaqatarwar gidan nasa yana karanta jarida. Ahankali yace mai.. “Na amince amma ka kula dakyau. Dan kasan yanxu mutane babu yarda…
“Insha Allah Dady zan kula. damma naji ajikina basu da niyar cutar dani.
Murmushi Dadyn yayi da cewa.. “Kadai ka kula da kanka da matanka.
“To nagode Dady sainazo.
Yana fad’in hakan ya kashe wayar da kallan YAWO yana cigaba da cewa. “Yace ya amince min.
Sosai YAWO tanuna Farin cikinta da qara yimai godiya. Kana ya bata umarni kan taje can waje wajen jira idan yaje ya duba MUSLEEMAN yaga tafarfad’o zai gaya mata..
Toh tace mai da matuqar jin dad’i…

Qarfe biyu NUFAISAT ta aikomai da tuwansa datamai. Kad’an yaci yabama YAWO sukaci da yaran.

Sai kusan qarfe biyar da rabi MUSLEEMA ta farfad’o..
Dake YAWO ta roqi Adams lokacin daya kawo musu tuwo tace mai yabarta tazauna a d’akin da MUSLEEMA take dan tana san ta farfad’o akan idanta. Ya amince mata da hakan badan suna yin hakan ba.
To shine lokacin da MUSLEEMAN ta farfad’o Yawon tana d’akin.
Dan haka cikin sauri YAWON tabata labarin yanda akayi bayan sumewarta. Sannan taqara mata da cewa karta tab’a gayama ADAMS cewa ita matarsa ce koda ya tambayeta yanxu. Ita dai duk abinda zaice mata tajishi kawai. Dan tana san tasan yanda yake rayuwarsa kafin subashi gaskiyar labari….
Kallanta MUSLEEMA tayi da cewa. “Indai zan qara rayuwar Aure dashi akaro na biyu zanyi duk abin da kikace. Sannan na godema Allah daya baiyana mana shi cikin sauqi.????
Kan yawo tabata amsa saiga ADAMS d’in ya shigo d’akin.. Nan YAWO tashiga gayamai yanxu tafarka.
Murmushi yayima YAWON saita futa daga d’akin shi kuma yaja kujera Ahankali ya zauna daf da MUSLEEMA yana qarema fuskarta kallo yace.. “Mema sunanki.
Cikin sanyin murya gabanta na fad’uwa tace.. “Sunana MUSLEEMA.
” MUSLEEMAT. Ya maimaita sunan da cigaba da cewa.. Suna me dad’i. Yanxu me yake damunki.
“Ba abinda yake damuna.
“Har tunanin mijin naki.
Kallansa tayi da d’aga masa kai hawaye ya zubo mata tace.. “Eh har shi.
“Zan iya roqar wata alfarma agareki…
D’aga mai kai tayi alamar eh…
Yaci gaba da cewa. Zan d’auke ki matsayin qanwata idan har zaki iya cire damuwar mijinki aranki. Dan ina san naci nasarar bama zuciyarki kariya..

Murmushi tayi dinful nata ya losa tace.. “Nayi maka alqawari idan har ka’iya rik’eni da gaskiya. Ka’iya bama zuciyata kulawa da amana. Zan cire duk wata damuwa daga zuciyata na fuskanci sabowar rayuwa.
“Mijinki ya tab’a gaya miki cewa muryarki na dadad’i.
“Bashi da abin fad’a wanda ya wucce yaban duk wata halitta tawa.
“Toki kula da kanki. Dan yanxu zaki fara sabowar rayuwa. Bani fatan naqara ganinki kwance a wannan gadan dan matsalar ZUCIYA. Zan riqeki da gaskiya da amana qanwata. Zan baki kulawa fiye da yanda Yaya yake bama qanwarsa..
Ahankali ta sakar mai murmushi shima ya sakar mata. Sannan yace tatashi taci abinci ga toilet nan tayi sallah yanxu zaizo su tafi. Sunansa ADAMS..
Toh tace mai. Zuciyarta nasan tajita jikinsa. Ga qamshinsa me gyara tunaninta. Tana matuqar san mijinta..

Har yakai qofa tace da shi.. “YAYANA baka temaka min natashi ba.
Ahankali ya dawo da tsayawa gabanta yace. “Ba cemin kikayi yanxu baki jin ciwan komai ba.

Gabanta ne ya fad’i. Bata fatan ya futa batare dajita jikinsa ba.
Gaskiya qauna da SO da zafi suke azuci…
A shagwab’e kamar zatayi kuka tace mai.. “Na faɗin maka hakan ne kafin nagane qafata tana da matsala..
“Kina nufin bazaki iya takawa ba.
“Idan dai naganni a bayi na sakama qafar tawa ruwa me sanyi zata tashi. Dan dama tasaba yimin hakan… Takai qarshen zancen nata da shagwab’ewa. Abin gwanin ban wani iri haka????????.
D’aukarta yayi ahankali yakaita toilet d’in sannan ya fito dajin dad’in yanda tafara saurin sakewa dashi.
Murmushi yayi aransa yana fad’in koma waye mijinta sosai yake shan fama da shagwab’arta..????

Bai wani dad’e a office d’in nasa ba. ya kulle dan shidda har ta gota. Nan yasa masu tsaransa su kwashi kayansu MUSLEEMAT susa a shara…
Haka su MUSLEEMA sunaji suna gani aka saka kayansu a shara.
Saidai suna cikin tafiyar tasu suka biya wani saban biotic d’in Adams d’in daya bud’e anan ya ibamma MUSLEEMA kaya sunkai 20. Haka Khalit da Khalil ma & mamansa Rahma. Dan harya fara kiranta da mamansa. Dayaji sunan Amminsa take da shi.

Haka direct suka iso gidansa.
NUFAISAT taci adonta cikin riga da wando jajaye. Tayi kyau sosai.
A nazarce take qarema su MUSLEEMA kallo dayi musu sannu da zuwa. Sanda takawo musu ruwa da drink kana ADAMS ya mata nuna data biyosa shashinsa..

Dan haka saita cema su MUSLEEMAN tana zuwa.

Da mamaki akan fuskarta take tayasa rage kayan jikinsa dace mai… “Mijina suwaye way’an nan.
Jawota jikinsa yayi ta zauna kan cinyarsa saiya shiga bata amsa da… “Wasu y’an uwanki ne my luv. Dan Allah kiji tausayina ki tayani cika alqawarin danayi musu.
“Na kasa gane inda zancenka ya nufa.
“Bini Ahankali mana my luv aizan gaya miki komai..
Shuru tayi zuciyarta na bugawa.
Ahankali ya qara jawota jikinsa dakyau ya kwashe komai ya gaya mata..
Sanda ta nutsu sosai kana ta kallesa da cewa. “Nayi alk’awarin zan tayaka cika alk’awarinka mijina. Saidai bazan b’oye maka ba. Gabana ya fad’i lokacin dana d’aga ido na kalli MUSLEEMAT. Jikina ya bani zuciyarta tana d’auke da wani sak’o..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button