LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Jan hancinta ADAMS yayi da fad’in “Kawai ki gayamin mekikejin tsoro.
“Ina jin tsoran kar nasake da ita tazo ta auremin kai. Kamar yanda TAUDHAT tayimin.
“Kina san dawo da hannun agogo baya my luv. Kince min kin gane manufata na auran TAUDHAT danayi. Ya kamata kibar batun TAUDHAT. Sannan batun da kike akan wannan Babyn tayimin qarama ASO. Tayaya zan fara iyawa da ita idan na auretan.
Ya dace ki gane kece da ZUCHIYAR ADAMS har abada.
Kece me iyawa dashi har abada
Kece wacce ya fara so da qauna arayuwarsa….
"Kaga naji naji. Takatseshi da fad'in hakan. Tana me cigaba da cewa. Saidai katabbatar duk ran danaga MUSLEEMA tazama mata agareka zan d'auki hukuncin daya dace akanka. Sannan duk abinda nace awannan lokacin saika yishi..
Murmushi yayi da manna mata kiss???? yana cewa “Na yarda…
“Ba yarda kad’ai ba. So nake ka d’aukimin alqawari.
“Na d’aukar miki alqawarin bani ba Auranta…
Tashi NUFAISAT tayi daga jikinsa fuskarta cike da murmushi ta manna masa kiss da cewa. “Idanko ka kuskure zaina yanka kowa ya rasa????????♀..
Waro ido ADAMS yayi???? da cewa. “Yankawa fa kikace.
Da dariya sosai tace mai. “Eh. Kuma sai kana bacci zan yanketa fil????
Murmushi yayi dan ganin yanda taqarashe maganar tata da rufe idanta alamar taji kunyarsa. Kana ya tashi da qarasowa gabanta. Ya zare hannayanta daga fuskar tata yace… “Idan kika yimin hakan kinsan bani ba qara rayuwa. Magana ta gaskiya my Luv. tunda nake arayuwata ban tab’a d’aukar alqawari na tsinci kaina cikin fad’uwar gaba ba sai yau. Gaskiya wannan alama ce na akwai kuskure cikin alqawarin dana d’aukar miki yanxu..
Dan Allah kiba zuciyata nutsuwa kiyi hak’uri da wannan alqawarin. kiciresa daga zuciyarki kisa aranki tamkar ban d’aukar miki shi ba dan Allah..
Kama fuskarsa tayi da hannu biyu tana cewa. “Ai tunda naganta nasan akwai wani abu Wanda zai faru dani akanta nan gaba. Walau ni ko wani nawa.
Ina ganin akanka ne abin zai faru shiyasa naji araina.
Kawai na share nabarma Allah ikwansa. Zan kuma karb’i duk qaddarar dazata sameni sanadinta. Zan karb’a da hannu bibbiyu… Tana kawowa nan azancenta tarungumesa. shima rugumeta yayi cikin matuqar MASEEFAR SONTA..
Daqer ta kwaci kanta agunsa takoma wajensu YAWO.
Nan takaisu wani shashi na baqi agidan.
Falo ne da bedroom me toilet acikinsa
Ba komai a falan saisu TV da kafet da kujeru. Sai bedroom d’in shi kuma set d’in gado ne.
Bayan sun saka kayansu a durowa abinci me rai da lafiya NUFAISAT takawo musu
Nan YAWO tama NUFAISAT d’in godiya sosai.
Haka kawai NUFAISAT taji tana san YAWO da MUSLEEMA da yaranta
Nan tarungume yaran tace tara tabasu abincin nasu da kanta.
Murmushi MUSLEEMA tayi mata dan itama taji santa aranta sosai.
Ahankali taje ta durqusa a gabanta tace da ita. “Aunty dan Allah zaki d’aukeni matsayin qanwarki. Wallahi tallahi haka kawai naji ina sanki.
Sanda NUFAISAT tagama ba Khalit abincin da takai mai baki Sannan ta kalli MUSLEEMAN tace da mata. “Kawai kin rigani fad’a ne.
Zan d’aukeki kamar qanwata idan har kika sakemin way’annan yaran suka zama kamar nice mamansu…
Murmushi taqarayi da qarasa matsowa kusa da ita tace.. “Aunty na baki su. Dama yaranki ne. Kawai ni na Haifa miki sune..
Ahankali NUFAISAT ta kalleta. Nan take taqara jin qaunarta aranta Amman tashare da cewa. “Idanko haka ne zanyi saurin y’antaki cikin ZUCIYATA. Musamman idan kika kasance meyimin ladabi da biyayya..
“Aunty na d’auki alqawarin zanyi duk abinda kike cemin.. idan dai bazai sab’awa Allah da manzansa ba.
“Yauwa my sister yanxu kiyi wanka bara na kawo miki kayan bacci kisa dan kifi samun nutsuwa.
YAWO ma tayi. kiyima yaran Sannan ku kwanta. Na tabbatar zakufi samun nutsuwa…
“Toh MUSLEEMA tace mata.
Nan NUFAISAT taje ta kawo mata kayan bacci. Kana tayi musu sallama takoma shashin mijinta.
Lokacin bata samesa ba. Da alama yayi shashin TAUDHAT ne
Eh yana falan TAUDHAT dan duba lafiyarsu kamar yanda yasaba idan ya dawo yake shiga d’akin wacce bata da girki dashi dan duba lafiyarta.
Haneepha na jikinsa tana murnar ganinsa yake ba TAUDHAT labarin su MUSLEEMAT. Da yanda ya d’auki aniyar temakwansu.
Gumi ne yaketa tsattsafoma TAUDHAT. Hankalinta ya bala’in tashi da labarin da yake bata. Duk sai tanemi nutsuwarta tarasa…
“Wai meyake damunki ne naga kikata had’a gumi. Da alamama kamar kina cikin damuwa.
A furgice ta kallesa da gyara nutsuwarta tace da shi.. “Bansan me zance maka ba. Haka kawai naji hankalina bai kwanta dasu ba.
D’aga Haneepha yayi daga kan cinyarsa ya zaunar da ita kan kujera sannan ya qarasa gaban TAUDHAT da kama hannunta yace…. “Kar wani abu ya dameki. Hankalina ya kwanta dasu dari bisa dari. Dan haka kema ina san hankalinki ya kwanta dasu. Dan bazasu cutar miki da miji da qawarki da y’arki ba.????
Murmushi tayi mai da d’agamai kai.
Ahankali ya sakar mata kiss a goshi da sakin hannunta ya sakarma Haneepha ma sannan yabar d’akin..
Ai yana futta TAUDHAT tatashi a rikice takira malamin nata da gaya masa komai.. Sannan taqara da cewa “Pls kasan yanda zakayi yanxu kajefemin bakinsu dukkansu. Tayanda bazasu tab’a gayama wani komai ba. Sannan ina san ganin bayan yaran. Dan Wallahi idan suka taso tawa taqare. Pls kayi wani abu akai yanxu….
“To ki kwantar da hankalinki kibani minti biyar zan kiraki yanxu..
“Toh tace mai da kashe wayar. Tana me safa da marwa cikin matsananciyar damuwam.
Canko bayan ya gama binciken nasa nan ya kirata dace mata.. “Gaskiya akwai matsala TAUDHAT..
Dan ainiyin fulanin daji nesu.
Ba wani abu dani zan iya yimusu. Saboda ita kakar tata tarigada ta dafa kanta da maganin tsari kala kala. Hakama tajiqa jikar tata da maganin bana wasa ba. Sannan suma yaran tunda sukazo duniya ta wankesu da ganyayyakinsu irin na fulani Wanda duk maseefar me jifa da matsafi da maye bai isa yaci yaran nan ba.
Sannan ita kanta uwar tasu yarinyar tana da ibada.. Sosai takema yaran nata dan Allah ya kare mata su.
Agaskiya TAUDHAT kifita daga harkar muta nan nan. Dan duk inda zakije bazaki samu galaba akansu ba.
Iya gaskiyar kenan dazan gaya miki itace tunda kikaga basu gayamai gaskiyar lamarin ba. To kibarsu ahakan. Ki dinga yimusu kirsa da kisisina yanda zasubar gidan wannan itace mafuta agareki…
“Kaga da Allah malam dakata. Naji duk abinda kace. Harsai yaushe zanta zama da maqiyana kana gayamin nabarsu bazan samu nasara akansu ba.
To bari kaji… zanje wajan bokan dayayi sanadin aurena da Adams yayimin maganin wannan matsalar
“Ba wajen boka ba. Kowajen wa zakije bazaki samu nasara akansu ba. Kuma na gaya miki iya gaskiyar ne kasancewarki uwar y’ata bani san kije kisha wahala. Tsaki TAUDHAT taja da kashe wayar tayi jifa da ita. Ranta abala’in b’ace.
Haneepha na kallanta tace.. “Momy malaminmu na islamiya yace babu kyau zuwa gun boka..
Galla mata wata muguwar harara TAUDHAT tayi da cewa. “Dan ubanki angaya miki gunsa zanje.
Shuru Haneepha tayi. (Kar me karatu ya manta Haneepha bata wucce shekara shidda ba idan ma takai. Amma take gayama uwar tata hakan.)
Shiko ADAMS rungume matarsa NUFAISAT yayi sukaji dad’insu abinsu. Sam basu da wata matsala.
Washe gari da safe NUFAISAT taje suka gaisa dasu YAWO.
MUSLEEMA tace zata raka NUFAISAT kitchen tatayata aiki.
Aiko NUFAISAT taji dad’in sake irinna MUSLEEMA.
Dan haka tare suka had’a kayan breakfast d’in.
Taba MUSLEEMA nasun takai nasu dining tajera ita da gwanin nata.
Suna breakfast d’in ne ta kalli ADAMS da cewa. “Saidai kamin afuwa. Dan MUSLEEMA tatayani had’a wannan breakfast d’in. Fatan kayafemin.
“Nayafe miki matata. Kuma dama tunda kika bata matsayin qanwa agarki dole nayi hakuri da duk wani abu dazan samu daga gareki naci Dan nasan dole tatemaka miki.
“Nagode mijina. Dafatan komai yayi zamzam.
“Sosai mah. Dan karna yaba ne ki zargeni shiyasa yin shuru. Dannaga lokacin da kuke aikin tare.
“Yabi abinka ai qanwa ce agareni.
Murmushi yayi mata da shafar gefan fuskarta..
“Ina sanki da yawa matata
“Gaskiya da fahimtar juna ce takaimu har iyanxu a SO Mijina. Nima ina san ka.????