LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda yaje gun TAUDHAT dansu gaisa har a lokacin bata tare da nutsuwarta.
Nanma sanda ya qara tabbatar mata Bafa wani matsala mutanan arziqi ne. Sannan ya nufi gunsu MUSLEEMAT d’in…

Bayan sun gaisa da Yawo Ahankali ya kalli MUSLEEMA ya amsa gaisuwar da take masa a shagwab’e. shagwab’ar tata tana shigansa da zafi fah????..
Da sanyin jiki yake cema YAWO “Zan turo salim qanina yakai yaran nan skull da islamiya anjima. dan bani san ganin yara haka ba karatu.
Godiya yawo tamai sosai sannan ya kalli MUSLEEMA tasakar mai murmushi shima ya mayar mata kana ya ficce daga d’akin zuwa motarsa.
Nan masu tsaran nasa sukayi gaba dashi..

Bayan NUFAISAT tagama komai na gyaran d’akinta saka Asiya tayi takira mata MUSLEEMA.
Bayan MUSLEEMAN tazo janta wani d’aki tayi suka zauna takira sunanta a nutse.
Nan MUSLEEMA ta kalleta da amsawa.
“Ina san kigayamin ainiyin labarinku. Dan zuciyata taqi gamsuwa da labarin da kakarki YAWO taba ADAMS akanku. Idan har kina san zama dani na amana to kiban labarinku na gaskiya..
Shuru MUSLEEMA tayi mata. Ita dai tun ganin farko taji tana san NUFAISAT d’in. Kuma taji aranta zata iya gaya mata komai na rayuwarta….
Qara kallan NUFAISAT d’in tayi da fashewa da kuka tace.. “Aunty kiyi hak’uri dajin labarinmu. Komai gaskiya YAWO tagayama Adams. Kawai dai ta boye wasu abubuwan ne.

“MUSLEEMA ina san sanin labarinku. Bazan iya hak’uri dashi ba..

Sanda MUSLEEMA tayi kukanta san ranta NUFAISAT bata hanata ba. Sannan takwashe labarinsu kaf ba abinda tarage tagayama NUFAISAT d’in.. Sannan taqara ta cewa.. “AUNTY MIJINKI ADAMS SHINE MIJINA UBAN ƳAƳANA. Wallahi Aunty ina matuqar laba’in sanshi kiyi hak’uri..

“Innalillahiwainna’ilaihirraji’un. Shine abinda NUFAISAT tace kanta na tsarawa. Nan tatashi taji jiri na ibanta.
Ai MUSLEEMA bata ankareba sai ganin NUFAISAT tayi ta zube qasa sumammiya..

Nan hankalin MUSLEEMA ya tashi. Gashi ba abin takira yawo YAWO ba. YAWO tasan tagayama NUFAISAT d’in komai.
Dan haka kitchen ta nufa ta ibo ruwa tadinga yayyafama NUFAISAT har Allah yasa NUFAISAT farfad’o..
Nan NUFAISAT taja numfashi duk da haka kanta bai dena Sara mata ba..
Nan hawaye ya shiga zubo mata.
MUSLEEMA da itama hawayen takeyi takama hannun NUFAISAT d’in tace.. “dan Allah Aunty karki nunama YAWO na gaya miki komai dan Allah..

Murmushi NUFAISAT tayi dace mata.. “Karki damu
MUSLEEMAT. Albarkacin qaunar da kika nunama ADAMS zan sadaki dashi cikin hikima. zakiji dad’insa fiye da yanda kikaji a rayuwar da kukayi a Ruga..
Saidai kimin alqawarin zaki kiresa amana. Kiza kik’eni amana.
“Aunty wallahi bani da mugun hali. Auntyna zakiji dad’ina. Aunty kece nake san kiriqeni amana. Aunty idan kin rikeni kamar qanwa zanji dad’in rayuwata. Bazanyi rashin uwa ba. Bazanyi rashi a maraici ba.

Rungumarta NUFAISAT tayi na d’an wani lokaci. Kana tace mata.. “Yanxu zaki fara sabuwar rayuwa. Zan fara gyaraki kafin nagayama Adams d’in komai. Idan kuma YAWO ta rigani shekenan kinga saidai kawai a gyara muku auranku.
“Aunty ina sanki Wallahi…
“Nima ina sanki Qanwata.

Sanda suka qara fahimtar juna sannan MUSLEEMA taje shashinsu.
NUFAISAT tayi murmushi da sakawa aranta zata riqe MUSLEEMA tsakaninta da Allah. Koda kuwa zata cutar da ita. Dan santa na hak’ik’a ne yayi ram da zuciyarta…

Follow me on wattpad @Rahamatnalele
Sadaukar da wannan shafi gareki ummu bashir nagode sosai da qaunar da kikemin cikinmu MARUBUTA. Ina sanki daji dake.. luv u 2 sister

Nagaida y’an hannuna????????
[7/31, 1:04 AM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

Yanxu zaku iya following nawa a wattpad. @Rahamanalele

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 26☆

Ga TAUDHAT ko MUSLEEMA na komawa shashinsu. tafito daga part nata dayi nasu MUSLEEMAN..

Da mutuntawa YAWO take gaishe tana amsa mata daqer kamar ansata dole. Dama ita MUSLEEMA kallan farko datama TAUDHAT d’in nan tagane itace matar Adams d’in ta biyu..

Da izgilanci TAUDHAT take qare musu kallo musamman MUSLEEMA da yaranta. Sai zuwa can taja tsaki tace. “Dama kune y’an aikin da Adams ya kawo jiya.
Murmushin yaqe YAWO tayi mata da cewa.. “Eh mune y’ar nan. Kina buqatar muyi miki wani abu ne..

“Ba Sunana y’ar nan ba Baba. Kamar yanda kukazo aiki da Hajjiya ya dace kikirani.
“Toh Hajjiya kiyi hak’uri.
Tsaki taqara jah. Kana tace. “Amma wannan shine karanku na farko azuwa aiki ko.
Shuru YAWO tayi mata.
Saiko MUSLEEM ta karb’e maganar cikin sauri da cewa. “Eh wannan shine karanmu na farko. Allah yasa ba lefi mukayima Aunty NUFAISAT matar gidan ba…

Harara TAUDHAT ta galla ma MUSLEEMAN da faɗin. “Ce miki akayi NUFAISAT ita kad’aice matar gidan.
Murmushi MUSLEEMA tayi mata da cewa. “Ai mun d’auka ita kad’ai ce matar gidan.
“Toh mu biyu ne. Ita NUFAISAT ni kuma TAUDHAT.. Dan haka daga gobe zaku fara yimin aiki..
YAWO tace.. “Toh Allah ya kaimu darai da lafiya…
Tsaki taqara ja batare datace komai ba ta ficce daga d’akin zuciyar cike da baqin cikin ganin yaran MUSLEEMA.

Nan tahau safa da marwa afalanta tana cewa.. “Shegun yara sai idanuwa kwala kwala kamar na mayu. Ga fari kamar y’an shan jini. Ga kyau kamar d’awisu.????
Haka tadinga sambatunta kamar tab’abb’iya. daga qarshe dai tayanke shawarar zuwa wajen bokanta kan adawo da Haneepha daga skull..
Ko qaryar data saba shararama Adams idan zata wajen malaminta batayi ba tazari gyale da iban kud’i tahad’a da kin motarta sai daji..

Tana fitta ko wani saurayi yazo ya kwashi su Khalit yakaisu skull d’in da Haneepha take zuwa. Dake had’e da madarasa ce skull d’in nan da nan komai ya kammala na zuwa skull d’in su Khalil d’in.
Dan nan take skull d’in tabayar da uniform nasu har na madarasa ad’inka musu. Nan saurayin ya dawo dasu daba YAWO tabbacin gobe idan yazo d’aukar Haneepha zai tawo da uniform nasu asa musu ya tafi dasu. Dan agoben akesan sufara zuwa.
Godiya YAWO da MUSLEEMA sukamai..

NUFAISAT tayanke shawarar gobe zataje kasuwa da MUSLEEMA dan tafara aiwatar da udirinta akanta.
Nan taqara duba account nata taga tana da wadatattun kud’i sai tayi hamdala ga Allah tana rokwansa daya bata damar aiwatar da komai cikin nasara. Sannan yacire mata jin kishi da baqin hali ko hassada. Kana tashafa addu’arta dajin wani shauqi me saka zuciyata cikin sukuni..

TAUDHAT ko tasamu bokan nata yana da baqi sosai. Amma haka ta fad’a turakar tashi kuma ya saurareta dan shima dama yayi missing nata..
Sanda ya gama surkullansa ya d’auko wani magani ya bata yace tasama MUSLEEMA a abinci ita da yaranta. Yana tabbatar mata idan sukaci nan zasubi duniya ba Wanda zai qara ganinsu bare ya kawo labarinsu.

Aiko nan TAUDHAT ta karb’a da bashi kud’i yace sam tariqe kud’inta yafi buqatar jikinta akan kud’in..
Nan dai takwanta yayi yanda yaga dama da ita kusan awanni. Asannan ne yabarta tasamu dawowa gida..

Ai tana dawowa gida tadafa had’add’iyar jalof da kifi ta barbad’e maganin aciki. Da nufin takaima su MUSLEEMA..
Saidai kan takai musu sanda takira malaminta da farin ciki take cewa… “Toh naje gun bokan nawa har yabani magani nasama su MUSLEEMAN a abinci yace suna ci zasubi duniya kuma ba Wanda zaisan inda suke har qarshen rayuwa.
Jan numfashi malamin nata yayi da cewa. “Dama nasan sai kinje wajensa. Bazaki tab’a hak’uri ba. Toh wallahi nayi bincike basu bane zasubi duniya kece zakibi duniya. Dan haka ina shawartarki kafin ki aiwatar da udirin kije ki nemi yafiyar mahaifiyarki dan Wannan asirin da kika mata ya karye d’azu d’azun nan ajikinta. Sakamakwan temakwan da maman kishiyarki NUFAISAT tabata. Dan taje tagaya mata matsalarta tsaf. Ita kuma tasa wani malami ya b’ata abinda kika mata shekara da shekaru. Yanxun nan naga hakan nake qoqarin kiranki sai gashi kinkirani.
Sannan ki kawomin yata. Karsai kinbi duniyar nazo karb’a yazama hajadi….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button