LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Da damuwa TAUDHAT tadawo gida.. Tana saqa tataya zata gane MUSLEEMA tana al’ada bare takawoma bokan abinda ya shaifi jinin nata..

Dan dai tayanke shawarar zata sakama MUSLEEMAN ido sosai har tacinma borinta..


Bayan sati biyu zanso me karatu yaga yanda MUSLEEMA tacanja.
Tacanja kamar ba MUSLEEMAN ruga ba..
Dan mayukan da NUFAISAT tabata dan tadinga amfani dasu sun goge fatarta sunmai da ita gwanin ban sha’awa. Dama yanxu take kan cikowa dan haka data fara samun gyara dacin abinci me gida jiki nan taqara murmurewa.
Haka yaranta ma gwanin ban sha’awa. ADAMS san yaran yake kamar me. Wannan ma ya qara baqanta ran TAUDHAU.
Musamman yanda taga NUFAISAT tana zagewa akan lamarinsu. Yanda ta maida su y’antattu kamar tasan yaran ADAMS d’in ne.. Wannan abu na k’ona ran TAUDHAU matuqa.. (Batasan NUFAISAT tasan komai fiye da saninta ba????)

Dake yau LAHADI ne ADAMS yana dawowa gida da wurri. Dan haka sai NUFAISAT tasa MUSLEEMA tayi wanka tayi makeup.
bayan tafito daga wankan wasu riga da siket na atamfa NUFAISAT ta d’auko mata. Kayan yana d’aya daga cikin wanda tad’inka mata.
Ba qaramin karb’arta atamfar tayi ba. Dan ita kantama NUFAISAT santa taji sha’awarta. Nan tabata turare me sanyin qamshi d’aya daga cikin way’anda take sawa.
Nan MUSLEEMA ta saka…

NUFAISAT takalleta da nutsuwa tace.. “Yauwa yanxu bazai wcce minti goma ba zai shigo. dan haka ina buqar kisan duk yanda zakiyi ya ganki.
Na tabbatar zaiji wani abu aransa. pls kifa nutsu dakyau dan bani san asamu matsala.
Murmushi MUSLEEMA tayi dace mata. “Karki damu Auntyna. Insha Allah komai da kika tsaramin yana nan a kwakwalwata..
“Masha Allah. Yanxu ni zanyi wajen shaqatawar gidan nan. Nasan komai zai faru akan idona. Danta k’ofar baya zai shigo. Dan Allah ki ankare dan Adams daban yake acikin maza.
Murmushi MUSLEEMA taqara yimata da d’aga mata kai alamar taji..

Aiko NUFAISAT na barin wajen saiga Adams ya dawo..
Da nutsuwa ya fitto daga motarsa yana mejin dad’in yanda NUFAISAT ce dashi.
Shi kawai yana rayuwa da TAUDHAT ne badan tana gamsar dashi abubuwa da dama na rayuwar aure ba. Dan nesa ba kusa ba NUFAISAT tafita sanin abubuwan da suka dace..

Yana wannan tunanin ne yaci karo da MUSLEEMA.. “Subhanallah.. Shine abinda yace. Dan sunbigi goshin juna.
Ahankali cikin sanyayyiyar murya MUSLEEMA tace.. “Dan Allah kayi hak’uri YAYANA bansan kana tawowa ba daban tawo gabaki d’aya ba..

Lumshe ido ADAMS yayi. Shifa ya lura kwana biyun nan MUSLEEMA na canjawa. Dan fatarta ta goge ga wani kyau da take qarawa. Sannan uwa uba Shifa yana jin wani iri sosai idan magana tana shiga tsakaninshi da ita
Yau kuma gashi yaji qamshin d’aya daga cikin turaran da NUFAISAT take sawa ajikinta..
Wai me yake faruwa ne.. Ya tambayi kansa..

Bud’e idansa yayi ahankali ya sauke akan dara daran idanunta kamar madara yana me cigaba da qare mata kallo daga har qasa. Tayi mai kyau sosai ga gashinta yasha gyara. Wallahi jiyayi kamar ya rungumeta..
Cikin wani hali yace. “Na hak’ura..
MUSLEEMA najin hakan taratsa tagefansa ta wucce. Saiko yabi bayanta da kallo cikin mamakin had’uwar datayi…
“INA SANTA…. Ya fad’i hakan abayyane ba tare dayasan ya fad’i ba… Yana juyowa danci gaba da tafiyarsa kawai sai yaga NUFAISAT tsaye!!! nannad’e da hannu tana kallansa.
Nan yahau kame kame yana cewa.. “Umm amm dama… Kasa cewa komai yayi dan haka sai kawai ya nemi wucce NUFAISAT d’in dan Wallahi wata kunyarta ce ta bala’in kamasa..????

Ainan cikin sauri NUFAISAT tasha gaban sa da cewa. "ɗan jini kaɗan mana malam..

Tsayawa yayi batare daya kalleta ba. Ganin hakan saitaci gaba da cewa. Kace kana santa ko..
Kallanta yayi ahankali da girgiza mata kai alamar aa…
Murmushin yaqe tayi mai daci gaba da cewa.. Hmm. Kasandai y’ar d’akina ce. Dan haka yanxu saika bada dubu d’ari saboda wannan furucin da kayi…
Cikin marairaicewa ya had’a hannuwansa biyu ???????? alamar tayi hak’uri bazai sake ba.

Tab’e baki tayi dacigaba da cewa..
Bayan kabada kud’in daga baya sai muyi ciniki kawai nabaka auranta.
Cije bakinsa yayi cikin matuqar jin kunyar yace.. “Zan bada. Amman kafin nan muje falanki kiji wani abu.
Gyad’a masa kai tayi alamar suje…
Bayan sunje sakata yayi kan kujera da durqusawa gabanta ya kama dukkanin hannayenta yace.. “My luv wallahi akwai matsala babba.. Dan tunda nayima yarinyar nan kallan farko naji wani abu ya minsini zuciyata…
Magana ta gaskiya zuciyata na tsumuwa idan magana tashiga tsakanina da ita..
Gashi ita matar aure ce.
Bai dace naji hakan akanta ba… Kawai ni yanxu na yanke shawarar zan kaisu gidansu momy dan kare kaina ga fad’awa ga halaka.. Saboda yanxu haka da naji qamshin wani turaranki ajikinta jinayi kamar na rungumeta..
Waro ido NUFAISAT tayi????..
Cikin sauri yacigaba da cewa.. Wallahi gaskiya na gaya miki dan kinsan ban iya yimiki qarya ba.????

Shuru NUFAISAT tayi tana tunanin tagaya masa gaskiya ne yanxu kodai tabari sai nan gaba.
Idan tagaya masa yanxu gaskiya tatemakesa da ita kanta dan bazai kwashe mata su ba.
Idan kuma taqi gaya masa tasan tunda ya furta zai kaisu wajen su Dady to saiya kaisu.

Dan haka Ahankali taqara rike hannunsa fiye da yanda shi ya riqe matan tace.. “Ka godema Allah ya Mijina daya had’aka dasu MUSLEEMAT har yabaka ikwan temakwansu kakawosu cikin gidanka.

Kasan da cewa MUSLEEMA matarka ce ya Mijina
Kasan da cewa yaran MUSLEEMA yaranka ne ya mijina
Kasan da cewa ganinka da MUSLEEMA tayi shiyasata sumewa har katemaketa
Kasan da cewa sanadin sanka da qaunarka shine silar kamuwa da ciwan zuciyarta
Kasan da cewa labarin da YAWO tad’an gutsira maka da cewa wani ne ba wanin bane kaine wanda tunaninka ya d’auke har tabaka auran MUSLEEMAN..

Cikin zubar hawaye NUFAISAT takwashe komai ta gayama ADAMS kamar yanda MUSLEEMA tagaya mata..

Shuru ADAMS yayi saboda jin yanda kansa yake juyama..

Ahankali yasaki hannun NUFAISAT ya tashi da komawa kan kujera hankalinsa tashe.
Lalle Allah shine Allah. Bai tab’a tunanin hakan zata faru dashi arayuwa ba.
Wai ya rayu a ruga. Sannan har kiwo yayi. Sannan yayi Aure har da raban y’ay’a uku…
sannan tunaninsa ya dawo baisan yayi hakan ba.
Wannan kad’ai ya isa mutum ishara…

Sosai yayi nisa cikin tunani. sam baiji abinda NUFAISAT take cemai ba. Naya ya kwantar da hankakinsa..
Sanda tatab’a shi da miqa masa madara me sanyi sannan ya dawo daga duniyar tunanin daya fad’a..

Jiki asanyaye ya karb’i madarar yasha kad’an da tashi da niyarsa nasan ficcewa..
Shan gabansa NUFAISAT tayi da riqe qugu tayimai fari da ido tace dashi.. “Sam bazaka fitta ba saika gayamin me zuciyarka tashirya maka. Dan bamuyi da MUSLEEMA zan gayama kowa ba..
Murmushi yayi da rungumarta yace… “Kinyi kyau sosai matata.. Sannan kinyi arayuwa..

“Ba wannan na tambayeka ba. Kawai kabani amsata.
“Dama part nawa zanje nayi wanka daga nan saina fara shawarar da zuciyar tawa..

“Nifa ban yarda ba. Kawai ka gayamin..

“Wallahi NUFAISAT kina da futuna. To dama zuwa zanyi na kwashe yaran naje asibiti ayimin gwajin jininsu da nawa.
Idan naqara tabbatarwa saina Nazo wajen YAWO na tuhumeta kan meyasa tab’oye min komai tunda farko…

Murmushi NUFAISAT tayi da kallansa tana cewa.. “Gud… naji dad’i sosai. Saidai yau lahadi baku zuwa asibiti kai da doctor Aryan.
“Zan kirasa yanxu muhad’u ai.
“Bara naje na d’auko gyalena to saina rakaka..
Jan hancinta yayi cikin matuqar santa da qaunarta. Yace “idan bake bazan iya rayuwa ba.
Kiss tasakar mai da cewa. “Wayace maka nima idan bakai zan iya rayuwa…
Murmushi ya sakar mata..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button