LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan tad’auko gyalan nata direct shashin su MUSLEEMA sukayi…
ADAMS ya qara kallan MUSLEEMA mamaki cike tam azuciyarsa wai ita d’in matarsa ce..
“Kuzo muje kumana rakiyar unguwa..
NUFAISAT ta katse masa tunani da faɗin hakan gasu Khalit..
Murmushi ya sakarma YAWO yace.. “Unguwa zasu rakamu.
Itama YAWON murmushin ta mayarmai da cewa… “Toh kudawo lafiya…

Har sun shiga mota saiga Haneepha tafito da sauri daga part d’insu tana cewa.. “Dady ina zaku nima zan biku..
Murmushi yayi mata dayima masu tsaransa nuni dasu bud’e mata motar itama ta shiga.
Aiko tana shiga Adams yaja motar dan yacema masu tsaran nasa subari basai sunyimai rakiya ba yanxu zai dawo..

Tun ahanya ko yakira abokinsa doctor Aryan yabashi tak’aitaccen labarin dacigaba da cemai pls su had’u yanxu a asibiti ya gwada mai jininsa dana yaran….
Jan numfashi doctor Aryan yayi da cemai ai yanama asibitin tun d’azu sakamakwan matarsa tatashi da naquda tun da safe. Dan haka ya qaraso kawai zai samesa..

Bayan sunkai Nan Doctor Aryan ya ibi jininsu Khalit da Khalil da Rahma dana ADAMS yahau binkice.
Masha Allah bincike ya nuna Khalit Khalil Rahma ƴaƴan ADAMS ne..????
Nan ADAMS yaja numfashi da rungumarsu kamar zai cinyesu haka yadinga sakar masu kiss..
Cikin tausayawa NUFAISAT ta goge hawaye. Doctor Aryan ko murmushi yayi da bama ADAMS hannu yace.. “Na tayaka murna d’an uwa. Dan samun uku a lokaci d’aya ba qaramin abu bane….
Kan ADAMS ya bashi amsa saijin kukan Haneepha kawai sukayi. Tana cewa itama ayi mata abunda akayima su Khalit dan Dadynta yayi mata kiss ya rungumeta itama..????
Dariya sukayi dukkansu da rarrashinta kan bakomai aka musu ba tayi hak’uri basai anyi mata ba.

Saidai fur Haneepha taqi yarda saima qara volume na kukan nata da tayi..????

Sam ADAMS baya san kukan Haneepha Dan haka sai kawai ya biye mata yace doctor Aryan ya ibi nata jinin ya gwada da nasan.

Aiko Cikin rikicewa NUFAISAT ta goge gumin daya wanke mata fuskar tace… “Haba my luv kabarta basai ammata ba.
Ai Haneepha najin hakan taqara tab’arb’arewa da kukan…
NUFAISAT taja numfashi haka kawai taji gabanta na fad’uwa. Saboda tasan idan doctor Aryan yagwada jinin Haneepha dana ADAMS gaskiya akwai matsala.. ????

Murmushi ADAMS yayi dace mata.. Karki damu my luv. bari yayi mata kinsan Haneepha da rikice idan ba’a mata ba har dare kuka zatata mana yau..

Gyad’a masa kai NUFAISAT tayi dacigaba da goge gumi..

Haka tana ji tana gani doctor Aryan ya ibi jinin Haneepha ba abin ta hanasa ba..

Shi kansa doctor Aryan ya girgiza da ganin sakamakwan da binciken ya nuna masa na Haneepha ba jinin ADAMS bace????..

Dan haka Sanda yayi gwajin sau uku yaga duk abu d’aya sakamakwan yake basa. Sannan ya hak’ura da fitowa daga wajen gwajin jikinsa a sanyaye ya miqama Adams takaddar gwajin nasa da Haneephan..

Tunda Adams ya fahimci Haneepha ba y’arsa bace ya zuba Haneephan ido zuciyarsa na bugawa.

Canko sai ganinsa a qasa sukayi.. NUFAISAT da doctor Aryan sukayi kansa suna masu kiran sunansa..
Bashi da damar amsawa dan yarigada ya sume..

Minti goma tsakani Adams ya farfad’o da kallan NUFAISAT yace… “Wannan ma kina da sani akai..
Saurin girgiza masa kai tayi alamar aa hawaye na zubo mata tace…. “Banda da sani akan wannan sam
Shima hawayen ne yazubo masa yace.. Nagodema Allah daya saka mukazo da Haneepha har hakan tafaru..

NUFAISAT taudhat tacuceni.. Ta ha’inceni.. Duk halaccin danayi mata sanda ta munafunceni. Ashe abinda tagayamin ranar farkon amarcina da ita qarya ne..
Allah Kasan nakamu dasan wannan yarinya Haneepha Allah ka sassautamin.
“Amiin.. NUFAISAT da doctor Aryan suka ce.

Ahankali ya tashi da saukowa daga gadan da doctor Aryan yasashi sannan ya karb’i makullin motarsa gun NUFAISAT yace su tashi suje gida..
Haneepha ta kalli ADAMS tace.. “Dady baka rungumeni kayimin kiss d’in ba..
Rintse idansa Adams yayi cikin wani hali ya rungumeta dayi mata kiss d’in..
Doctor Aryan ya dafa kafad’arsa yace.. “Kayi aiki da hankali abokina. Tunda kaga lokacin dakasan hakan akan Haneepha lokacin ne kake da arziqin su Khalit harsu uku..
Dan haka pls kanutsu sosai wajen yanke hukunci…
Murmushi kawai Adams yayima masa da ficcewa daga d’akin yana cema NUFAISAT susamesa a mota..
Haka da damuwa NUFAISAT sukabi bayansa..

Tuqi kawai Adams yake amma hankalinsa ya tafi kan tunanin wane hukunci ya dace yayima TAUDHAT..

Ahaka suka iso gidan jiki a sanyaye..
Direct part d’insa Adams yayi ya d’auki takadda da biro ya rubutama TAUDHAT saki har uku..

Itako tana zaune a falan nata zuciyarta cike da mamakin ina Adams ya d’auki NUFAISAT sukaje.. Saiji kawai tayi wayarta na ringing.. Bak’uwar number ce. Dan haka saita d’auka a yatsine..

“TAUDHAT nice me magana..
“Wake nan.
“Hajjiya Rukayyat kishiyar sirukarki.
“Ayya. Sannu Hajjiya. Dafatan dai Alkairi ne yasa kika kirani..
“Ai tunda kikaga ban tab’a kiranki ba. Yadace kigane wannan kiran ba alkairi bane agareki
“Ko.
“Kwarar
“To ina jinki..
Murmushi Hajjiya Rukayyat tayi da qara bajewa kan kujerar falanta tace.. “Dama na gaya miki saina baqanta rayuwarki kan abinda kika min ko. Toh yau ranar tazo dan ba abinda zai katangeki ga haukacewa yanxu…
Murmushi TAUDHAT tayi da faɗin.. “Lalle kanki ya kulle. Dan ina tabbatar miki har qarshen rayuwata bazan tab’a yin hauka ba.
“TAUDHAT kenan. Zaki gani yanzu a kwaryarki. Danni Hajjiya Rukayyat ban tab’a d’aukar alqawari naqi cikawa ba. Dan haka kibaza ido yanxu d’an zukuluzu zai baiyana agareki.. Hajjiya Rukayyat na fad’in hakan ta kashe wayarta da sheqewa da dariya..

Sororo TAUDHAT tayi da wayarta a hannunta. Kuma daidai lokacin ADAMS ya shigo falan nata..
Ahankali ya miqa mata takaddar hannunsa me d’auke da sakin dayayi mata. Tako karb’a cikin sauri da wareta dan taga me ta kunsa..

Agigice tatashi da kallansa tace… “Wai ni TAUDHAT kasaka ADAMS.????
Murmushi yayi mata da cewa.. “Eh. Na sake ki saki uku TAUDHAT. Sannan ki tattara kayanki a yanxu ki barmin gidana. Sannan nasan kinsan muslinci yaban Haneepha ko..
Dan haka ke d’aya zaki fitta batare da ita ba..

Cikin matuƙar gigicewa tace “Kan uba. Kutumar uba. Durin uwa.???? NUFAISAT ce ta gaya maka Haneepha ba y’arka bace ko..
Lalle tunda tayi sanadin datse igiyar aurena tsakanina dakai Wallahi sainayi mata abinda har tamutu bazata tab’a mantawa dani ba…

ɗauketa da wani matsiyacin mari ADAMS yayi..
Kanfin tadawo daga hayyacinta ya qara bata wani..
Nan take ta kwalla wata muguwar qara sakamakwan ganin wani jibgegen aljani da tayi a gefanta yana zaro mata ido kamar zai cinyeta. Sannan ya watsa mata wani abu kamar qasa ajikinta. Ai nan take taji kamar an zuba mata wuta.
Wannan shine yasata kwalla qara ba marin da Adams yayi mata ba..

Nan tafara cire d’an kwaninta tare da fara cizge gashin kanta tana cewa shikenan na haukace.
Zuba mata ido ADAMS yayi ganin kamar da gaske abinda take fad’a na shirin faruwa da ita..
Daidai nan NUFAISAT tashigo falan saboda ihun da TAUDHAT d’in tayi..
Ai NUFAISAT naganin abinda takeyi cikin rashin fahimta tace… “TAUDHAT kidena cizgar gashinki mana. Kokinyi hauka ne..
Kallan NUFAISAT d’in tayi idanta ya juye ya zama ja tace. “Nayi hauka NUFAISAT.. Na haukace. ADAMS ya sakeni bayan baqar wahalar dana sha wajen bin malamai da bokaye akansa… Sannan Hajjiya Rukayyat ta haukatar dani dan nayi mata asiri takwanta jinya tsawan shekara biyu. Yanxu kema zokimin naji dad’i dan kema nasaka malamina ya bata miki ni’ima dan kawai Adams ya tsaneki…. Takai qarshen zancenta da nufo NUFAISAT d’in..
Ai cikin sauri NUFAISAT tayi tsalle d’aya ta maqalqane ADAMS tana ihun wai ya kalli idan TAUDHAT tazama mayya????…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button