LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Afuwa sis hajjaju???????? ga LEEKITAN ZUCHIYA kema naki ne. Ki gaidamin da Habibat kice ina santa…

Nagaida y’an hannuna????????????????????????????????luv u ❤❤❤❤
[8/2, 7:13 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.. Viawattpad@rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 27☆

Qara qalqale NUFAISAT d’in ADAMS yayi cikin matuqar mamakin abinda TAUDHAT d’in take fad’a..
Itako NUFAISAT Yanxu tagane cikin hauka TAUDHAT d’in tayi maganar.

Cikin tsawa ADAMS yace da TAUDHAT d’in.. “Idan kika kuskura kika tab’amin mata Wallahi saina miki dukan mutuwa..
Ai TAUDHAT najin hakan sai tatsaya cak da fashewa da kuka…
Da sauri NUFAISAT tasake ADAMS tayi waje da gudu ADAMS yabi bayanta da kulle TAUDHAT d’in..
Hankalin NUFAISAT atashe yake matuqa…
Nan tahau safa da marwa a d’akinta tana mamakin abinda yasami TAUDHAT d’in. ADAMS ya bata labarin shidai yana bata takaddar saki tahau yimai sambatu. Sannan ya qara dace mata takwantar da hankalinta komai zaizo da sauri.
Nan NUFAISAT tabashi labarin abinda tasani tsakanin Hajjiya Rukayyat d’in da TAUDHAT d’in.. Sannan taqara mai da janta wajen boka da ita TAUDHAT d’in tayi…
Sosai ADAMS yayi mamakin wannan lamari. Anan ya rungumi NUFAISAT d’in dajin qarin sanda da qaunarta aransa..
Nan yakira mama Mahaifiyar TAUDHAT dasu Dadynsa ya gaya musu gafa abinda yake faruwa….

Koda sukazo gidan Hankalin Dady dana Amminsa ya tashi matuqa.
Mamah ko mahaifiyar TAUDHAT d’in sam bata wani damu ba. Cewa tayi dama haka qarshen mutane irinsu kenan yake zuwa.. Dan haka ADAMS yasata amota akaita gidan mahaukata. Karya wani saka lamarin aransa bare ya damesa. Dan alhakin mutanan dake kanta koyasa ayi mata wani temako cikin gidan nasa baza awani ci nasara ba.
Dan haka maza yanxu yasa akaita can gidan mahaukata..

Aiko ADAMS yabi abinda maman nata tace… Dan haka saiya dubi TAUDHAT d’in yace.. “Duk da na sakeki TAUDHAT kije ki qarasa rayuwarki nayafe miki duk abinda kikayi min.
NUFAISAT ma ta kalleta da hawaye tace.. “Nima na yafe miki TAUDHAT Allah ya baki lafiya..
Mamanta ma tace “Nima haka..
Abin gwanin ban tausayi. Dan Sai dariya TAUDHAT d’in take musu alamar haukar tagama shiga jikinta..????

Haka ADAMS yasa masu tsaransa sukaita can gidan mahaukatan sannan su tsaya tsayin daka su cika komai na abinda masu kula da lafiyar irinsu suke buqata suyi musu kana su dawo. Nan suka amsa masa da ladabi suka taficce da TAUDHAT tana ihu da kiran sunan Hajjiya Rukayyat da ADAMS d’in da mamanta harda NUFAISAT..

Kalamai masu dad’i da sanyaya zuciya Ammin Adams take gayama maman TAUDHAT na tayi hak’uri ta rungumi qaddarar da Allah ya aiko mata akan yar tata tilo…
Murmushin yaqe kawai maman TAUDHAT d’in tayima Ammin da cewa bakomai ai rayuwa haka take. Aduk yanda ka d’auketa haka zata zo maka. Jan hankalin da zatayi shine dan Allah idan da masu hali irin na TAUDHAT suyi gaggawar komawa ga Allah tunkan rayuwarsu ta wulaqanta idan sukazo gangara. Wallahi rayuwar bata da tabbas. Idan yau mune gobe bamu bane. Gashi dai kowa yaga farkwan TAUDHAT kuma kowa yaga qarshenta. Wannan kad’ai ya ishi mutum ishara. Bokaye da malaman tsubbu ba abinda suke iya yima mutum sai kaishi ga halaka.
Wallahi jama’a boka da malaman tsubbo manyan maqiyinku ne dan jefaku suke ga halaka suna baku biyan buqatarku nad’an wani lokaci.
Ni wannan abun ma yana bani mamaki.???? Tayaya zakaje wajen annamimai irinsu neman biyan buqata bayan ga ALLAH wanda yayika.. Wanda ya halicceka yayi maka komai na rayuwa sannan yace karoqesa zai biya maka buqatarka amma ka bijirema maganarsa kaje wajensu sannan kace qarshenka zaiyi kyau.. Lala lala????. Wallahi qarshenka-ki bazaiyi kyau ba

Yanxu ku duba NUFAISAT… Bata zuwa wajen irinsu neman biyan buqata ita Allah kawai tasa agaba… Ya hanata Haihuwa???? amma hakan baisata kauce masa ba.
Tana jin dad’in rayuwarta. Tunda ya bata lafiya ya bata kwanciyar hankali. Ya bata soyayyar miji. To itako mezaisa tayima Allah budulci taje wajen waninsa neman wani abu bashi ba. Mutane wallahi muyima kammu tanadi agidan lahira. Mudena biyema san duniya muna jefa kammu ga maseefa. Tun anan gidan duniya bamu tare da kwanciyar hankali hakama agidan lahira bamu ba samun rahamar ubangiji..????????????????????

Haka maman TAUDHAT tatafi gidan nata zuciyarta da sanyi dan taji d’ad’in sanyayyun kalaman da Ammin Adams tagaya mata..

Maman TAUDHAT d’in na tafiya Dady ya kalli Ammi dace mata suma ai saisu koma gida ko..
ADAMS ya gyara zama a falan TAUDHAT d’in dake duk anan suka taru yace da Dadyn nasa… “Dama ina san nagaya muku wani batu kuma..
Ammi tace “yauwa bamuji dalilin sakin da kayima TAUDHAT d’in ba tunkan tayi haukan..
Kama hannun Ammin tasa yayi ya kwashe duk abinda NUFAISAT tayagamai akan MUSLEEMA na matarsa ce kuma su Khalit yaransa ne. Sannan da sanin da yayi na Haneepha ba y’arsa bace. Da sakin dayayima TAUDHAT d’in sanadin hakan..

Dady Ammi sun girgiza dajin wannan batu…
Sunji mamaki matuqa.
Nan Dady yasa yaje ya kira masu su MUSLEEMAN su gansu.

NUFAISAT tace aa ya zauna bara taje ta kirasu..
Aiko nan taje shashin dasu MUSLEEMAN suke
Tagansu jugun jugun da alama sunfahimci wani abu na farawa agidan..

Su Khalit da Kahlil Rahma da Haneepha ko sai wasansu suke.
Nan NUFAISAT tasakar musu murmushi da gaya musu iyayan ADAMS nasan ganinsu yanxu a shashin TAUDHAT..
NUFAISAT na fad’in musu hakan tahad’a kan yaran tace subiyota tabasu minti.
Nan suka bi bayanta da murna.
Suma su MUSLEEMAN bayansu sukabi da tunanin Allah yasa ba wani abu sukayi ba..

Dake MUSLEEMA ce a gaban YAWO tana shiga falan YAWO tabiyo bayanta..
Nan YAWON idanta ya sauka akan Ammin Adams..
Ai a furgice Ammi tatashi da nuna YAWO tace.. “YAWO.. ????
Cikin sarqewar murya da mamaki itama YAWON tace.. “RAHMA..????

Ainan Ammi tazube qasa sumammiya..
ADAMS yashiga zuba mata ruwa cikin tashin hankali..
Shiko Dady zubama YAWO ido yayi yana tuna itace mahaifiya ga Ammin Adams..
Wacce sukasha nema ashekarun da suka gabata..

Bayan Ammi ta farfad’o kuka tasaka da tashi ta rungumi YAWO tana cewa.. “Haba mahaifiyata menayi miki arayuwa kika gujemin.
Kin hanani ganinki. Sannan kin hanani sukuni. Kwanciyar hankali nutsuwa duk na rasasu sanadinki.
Sanda nasaka araina baki raye sannan na samu nutsuwa..

Share hawayenta YAWO tayi da bata labarin dalilinta na barin BASA garin Jos sukazo gwambe.
Anan take cigaba da bata labarin mutuwan yayanta Musa da samuwar y’arsa MUSLEEMA da sukayi. Sannan taqara mata da labarin Auran ADAMS da MUSLEEMA data musu.. daidai wahalar da suka sha kafin su qara ganin Adams d’in akaro na biyu..????

Jan numfashi Ammi tayi dace ma Yawon…
“Wahalar ku taqare YAWO. Dan MUSLEEMA d’an uwanta ta Aura. ADAMS D’ANA NE YAWO..

Da mamaki YAWO ta kalli ADAMS da sakar mai murmushi tace.. “Ashe ba banza ba naji qaunarka da sanka a zuciyata. Sannan MUSLEEMA takafe kan kai take so.
Murmushin shima ya sakar mata da kallan MUSLEEMA wacce tayi saurin sunkuyar dakanta qasa tana wasa da awarwaran hannunta.. Yace.. “Nima ganin farko dana muku kan titi naji zuciyata tana san rayuwa daku.
Wannan dalilin yasani tambayarki meyake damun MUSLEEMAN lokacin da take a sume. Nagodema Allah dayasa mutanan nan suka min dukan dana rasa tunanina na fad’a hannunki kika bani Auran qanwata har hakan tafaru
Sannan ina qara godema Allah dayasa nake rayuwa da matata NUFAISAT.. Wacce ta kasance daban acikin mata..
Wallahi YAWO idan har MUSLEEMA bazatabi NUFAISAT a zamansu da zasuyi ba zan iya barin MUSLEEMAN na rungumi yarana na rayu ni kad’ai da NUFAISAT d’in..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button