LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi YAWO tayi dace mai.. “Wallahi baka nan Allahn ka nanan bamu da abin yabo sai matarka NUFAISAT..
Tunda nake arayuwata ban tab’a tunanin zanso wata y’a mace har cikin jinina bayan MUSLEEMA sai NUFAISAT..
ADAMU ina san NUFAISAT kuma ina bayanka kayanke duk wani hukunci dazaka yanke akan MUSLEEMA idai har zata takawo ma NUFAISAT d’in wani wargi….

Murmushi NUFAISAT tayi da zuwa wajen MUSLEEMA takama hannunta da cewa.. “Zan rayu dake qanwata rayuwa irinta yaya da qanwa.. Ina sanki saboda san da kika nunama ADAMS a Ruga. Ina qaunar y’ay’anki dan Allah badan san da nake miki ko nake ma ADAMS ba.
Saboda idan naso su dan ADAMS wata rana baya nan.
Idan naso su saboda ke wata ranah bakya nan.
Yau naqara ganin ishara agun abokiyar zaman TAUDHAT.. Dan haka dan Allah ina rokwanki daki saka Allah azuciyarki mubama mijinmu Farin ciki da kwanciyar hankali…
Kallanta MUSLEEMA tayi hawaye ya zubo mata ta rungumi NUFAISAT d’in tace… “Aunty zan biki. Wallahi zan biki. Ke uwace agareni yanzu. Sannan abokiyar zama. Auntyna. Wacce zanna gayama damuwata.. Haka kawai naji sanki azuciyata. Haka kawai naji qaunarki azuciyata. Haka kawai naji ina san nayi rayuwa dake..
Uwa uba nasan bazan tab’a samun wani Farin ciki tsakanina da mijina ba idan har ban biki nasaka azuciyata zan rayu dake da amana da gaskiya ba.
Aunty ina sanki dan Allah kiyarda aranki haka ne..

Murmushi NUFAISAT tayi da cewa.. “Nima ina sanki MUSLEEMA. Allah ya shige mana gaba akan dukkanin al’amuranmu..
“Amiin.. Dukkansu sukace..
Sannan Dady yaqara sakama NUFAISAT albarka. Ya rungumi yaran MUSLEEMA jikokinsa yayi musu addu’a sannan suka d’an tab’a hira kad’an inda Ammi take cewa yanxu Adams yasa masu kwasar kaya suzo su kwashe kayan TAUDHAT sukaima Mahaifiyarta ayau.
Sai gobe ayima MUSLEEMA d’an gyare gyare ya saka mata komai na rayuwa saita koma d’akinta. Tunda ba wani batun gyara Aure tsakaninsu dan har yanxu tana nan a matsayin matarsa dan bata kai iya adadin da za’ayi musu gyara ba…
Nan ya amsa mata da to insha Allah zaiyi yanda tace…

Da MUSLEEMAN su Dady suka tafi gidansu..
Dan Ammi tace tana san tad’an tab’a hira da ita kafin tashiga d’akin nata..

Sai gidan ya kasance daga NUFAISAT sai Haneepha da Adams sai masu hidima..

Anan ADAMS yasa masu kwashe kaya sukazo suka kwashe kayan TAUDHAT tas ko tsinke basu gari ba sukayi gidan maman nata dashi
.
Tun alokacin aka fara gyaran shashin TAUDHAT d’in…

Komawar su Ammi gidansu ko abin daya faru shine. Dady nayin ido hud’u da Hajjiya Rukayyat ya danqara mata saki uku..
Ai yana danqara mata nan tafad’i sumammiya..
Dama lokacin qanwarta na gidan. Nan Dady yace tafitar masa da ita daga gida..
Sannan zai turo musu da kayanta tas..
Aiko hakan ce tafaru..
Dan qanwar tata na tafiya da ita asibiti Dady yakira masu kwashe suka kwashe kayanta tas zuwa gidansu..

A asibitin cewa sukayi b’arin jikinta ne ya shanye.
(Rahama nalele tace Toh ALLAH ya bata lafiya✋????)

NUFAISAT rungumar Haneepha tayi awannan dare suka sha baccinsu.
ADAMS na kallansu yace da NUFAISAT tasan fa bai iya kwana shi kad’ai ba.
Tace yau dai saidai yayi hak’uri dan bata tab’a jin qaunar Haneepha aranta irin nayau ba.
Shuru yayi mata.. Dan abin gwanin ban tausayi ne..
Yasaka aransa zai riqe Haneepha kamar yanda ya faro.. Dan dama yana santa yana qaunarta..
Dan haka bin bayan NUFAISAT yayi ya kwanta tana jinsa taqara rungume Haneephan a gabanta.
Saiya sakar mata kiss awiya da cewa “Ina sanki matata…
Murmushi tayi batare da tacemai komai ba..

Washe gari komai ya kammala.. Na d’an gyare gyaren da akama MUSLEEMA na shashin TAUDHAT..
Dan haka tun a ranar ADAMS ya turama da NUFAISAT kud’i ta account nata yace tafara tunanin abinda zata siyama MUSLEEMAN.

Zainab yayar NUFAISAT yazo NUFAISAT d’in ta kwashe komai daya faru tagaya mata
Zainab qara godewa Allah tayi da bai bama NUFAISAT d’in muguwar zuciyaba
Tayima TAUDHAT da Hajjiya Rukayyat Fatan samun lafiya.

Har tsawan Sati d’aya tunda ADAMS yake zuwa gidansu baya cin karo da MUSLEEMA..
Gashi zuciyarsa tana buqatar ya ganta kawai magana tashiga tsakaninsu.????

Matsalar ba daga kowa bane daga ita MUSLEEMAN ce. Dan wata kunyar ADAMS d’in takeji tunda taga yasan komai daya faru tsakaninsu..
Shiyasa tana jin zuwansa gidan take shigewa can bedroom na Ammi tayi kwanciyarta har saiya tafi take fitowa..

Toh yau Allah yayi yau Ammi tace MUSLEEMAN zata tare a gidan nasa….
Dan haka takwas da rabi na dare dayaje gaisar dasu anan Ammin take CE mai yau zai tafi da MUSLEEMA. tunda tayi waya da NUFAISAT ta tabbatar mata tagama yimata siyayyar komai na rayuwar a mace a d’akinta..
Murmushi ADAMS yayi dace mata toh..

Aiko yana tashi tafiya nan MUSLEEMA tafito cikin riga da saket na material me mayafi d’inkin yayi mata kyau sosai
Nan suka yima su yawo sallama..
Dan Ammi tace saidai akawo Haneepha dan Khalit da Kahlil Rahma sai sunyi wata agunta. Dan haka akawo Haneepha ma dan idan direban da yake kaisu makaranta yazo yadinga tafiya dasu kawai lokaci d’aya..
Sannan Dady yace Yawo ma bazata koma gidan ADAMS da zama ba.

Dan Akwai wani shashi nan cikin gidan nasa ya mallaka mata nan d’in anan zata dinga rayuwarta.
Sannan shashin Hajjiya Rukayyat zaisa a canja mishi fasali Salim ya zauna aciki shida matarsa idan anyi auran.
Dan yazo da wata Iyami yarinyar me hankali yacema Dadyn ita yake so..
Kuma koda dadyn yayi binkice yagano gidansu yarinyar gidan mutanan arziqi ne..

Dan haka sai kawai suka tsaid’a magana za’ayi bikin dazaran yarinyar ta kammala karatunta..

Tuƙi ADAMS yake Ahankali shuru ba me magana tsakaninsa da MUSLEEMA..
Saima satar kallansa da MUSLEEMAN takeyi.. Tana tunanin yau ta’ina zata fara da mijin nata..
Ahankali ya kalleta da cewa.. “Wai miye ne kiketa wani satar kallona.
“Naga YAYAH aiba lefi bane idan na kalle ka ko.
“Toni aini naga ba Kallanki nake ba.
“Alamu sun nuna kamar kana fushi dani..
Murmushi yayi da cewa. “So nake naji dalilin dayasa kika hanani ganin kanki tunda kika bar gidana kika dawo gidansu Ammi..
“Kayi hak’uri bazan sake ba insha Allah.
“Nafa lura bada hak’uri ya zamar miki jinin jiki..
Cikin shagwab’a tace.. “Toh YAYA mezance maka bayan hakan..
“Kawai yanxu idan kinyi min lefi hukuntaki kawai zan dinga yi..
“Ban saba da hukuncinka ba YAYAH dan Allah ka rangwanta min..
Wani kallo ya watsa mata da cewa.. “Zaki saba dashi nan kusa..

Shuru tayi mai dan Kallan yashigeta sosai..

Ahaka batare da sun qarama junansu magana ba suka iso gidan..
Direct falan NUFAISAT suka shiga tana tare da Haneepha suna kallo..
Ai MUSLEEMA na ganinta taje da gudu ta rungumeta tana cewa.. “Aunty nayi kewarki sosai.
Murmushi NUFAISAT tayi da faɗin.. “Nima haka my sister.. Dafatan kina lafiya..
“Na daɗa samun lafiyar ne dana ganki Auntyna..
“Toh yayi kyau yanxu muje kiga shashinki idan komai yayi miki to. idan kuma akwai abinda kike buqata saimu barma gobe idan Allah ya kaimu na qarasa aikin ladana.????
“Aunty dukfa abinda kikayi kawai yayi.. Bani buqatar abinda baki buqata.
Murmushi NUFAISAT taqara yi. Wallahi ita dai tana san MUSLEEMA..
Yauwa Aunty.. Zan fara kawo miki qarar YAYA tun yanxu…???? Wai zai hukuntani idan naqara yimasa nefi. Wai yana fad’in bazai qara hak’ura da duk abinda zanyi masa ba.. MUSLEEMA takai qarshen zancenta da turo baki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button