LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Aiko kallansa tayi cikin masifa tace.. “Wallahi bazanje jiyar tata ba.????
Ganin da gaske tana san saka mai kuka sai yahau lallashinta da cewa.. “Dan Allah karkimin kuka. Kawai mubarta ta mutu dama nafisan yin rayuwa dake ke d’aya y’ar matata. Y’ar cafai y’ar me kyau????.. Ya faɗin mata hakan cikin wayo da hikima..

Aiko nan tace.. “Hmm umm.. Lalle ma. Toni bazan iya barin qanwata ta mutu ba. Dan kasanfa ina santa kawai dai kasan ba kowace mace bace take iya d’aukar jinya irin wannan.. Amma zan kula da ita insha Allah wannan ba zai zama da matsala ba. Daidai tamutu koya kagani..
Murmushi yayi ganin yau yarinta tazo kwakwalwarta yace.. “Kuma fah..

Haka ya tafi office ya barta da jinyar MUSLEEMA.????

Akwana bakwan da NUFAISAT tabasu MUSLEEMA taji jiki sosai agun ADAMS.. Dan gaskiya fa yana jinta kamar NUFAISAT d’in ne
Hakan yasa ya yaqi saurara mata..

Saidai daya dawo d’akin NUFAISAT sai yaji ina da bambanci..????

Eh gaskiya NUFAISAT tad’anfi MUSLEEMA dad’in kusanta kad’an. Amma zai iya rayuwa da MUSLEEMA ahakan batare daya damu da rashin NUFAISAT ba..

Ma’ana dai yanxu ADAMS yana jin dad’in harka da matansa cikin nutsuwa fiye da yanda yake tare da TAUDHAT..
Idan yana tare da NUFAISAT yana qara qaunarta Sosai..
Idan kuma yana tare da MUSLEEMA yana ji kamar yarya barta dan shagwab’arta na tafiya da zuciyarsa matuqa har yadinga jin dama ace karya barta. Ya zauna kawai shida ita tana zubamai shagwab’ar..
Saidai kuma inda ace NUFAISAT tagane ADAMS yana matuqar san shagwab’a a rayuwarsa tafara yimai ba makawa saidai MUSLEEMA tayi zaman hak’uri agidan dan komai na Adams d’in tattarewa NUFAISAT d’in zatayi dan zaiji kawai da ita kad’ai zai iya rayuwa.

Wannan shine abinda NUFAISAT bata sani ba ajerin abinda ADAMS yake so arayuwarsa..
Kuma duk randa tasani tafara yimai zai iya juyama MUSLEEMA baya..

Da gaske hakan tafaru..
Dan wata ranah NUFAISAT tagane ADAMS yana shagaltuwa da MUSLEEMA idan tana zuba mai shagwab’a..

Dan haka sai itama ranar tashagwab’e akan duk abinda yake shiga tsakaninta dashi..
Duk maganar da zata mai sai tamai a shagwab’e..
Aiko awannan ranah taga rikicewar ADAMS akanta.
Dan qarara taga ya nuna mata kulawar da tunda suke ita dashi bai tab’a nuna mata ba.. Talura da MUSLEEMA da yanda take mishi magana aranar ya wani fitta daga harkarta.
Wannan shine dalilin dayasa NUFAISAT bata qara yimai irin wannan shagwab’ar ba dan bata san wani abu ya shiga tsakaninsa da MUSLEEMAN na rashin jituwa..
Saidaifa tana d’an tab’amai kad’an kad’an..????


Ran nan malamin TAUDHAU yazo wajen ADAMS ba kunya yake gayamai wai yazo karb’ar y’arsa Haneepha ne.
Nan ADAMS ya zuba mai ido har yakai qarshin shirin kunyarsa.
Sannan ADAMS d’in ya kira jami’an tsato yace su kulle shi karku tab’a barinsa ya fito dan zama da irinsu masifa ne acikin al’uma…

Ai malam isma’il yayi dana sanin tunkarar ADAMS da yayi da batun ya bashi Haneepha
Dan yanxu Gashi a kurkuku yana aikin wahala cikin nadamar abubuwan daya aikata arayuwarsa…


Wata shidda da tarewar MUSLEEMA tasamu ciki. Inda bai wani zo mata da wani laulayi ba har takai watan haihuwanta..
Inda tasamu y’a mace kyakkyawa san kowa in wanda ya sara..
Yarinya taci NUFAISAT..
Aiko NUFAISAT tayi tsalle tayi murna na Farin cikin takwarar da mijin nata yayi mata.. Haka MUSLEEMAN tatayata farin ciki sosai sam babu wani abu aranta..

Sati biyu da haihuwan MUSLEEMA akayi Auran salim qanin ADAMS inda salim d’in ya tare da amaryarsa Iyami acikin gidan Dady shashin mahaifiyarsa..
Inda ita Mahaifiyar tasa Hajjiya Rukayyat take gidansu ana cigaba dayi mata magani amma kamar ba’ayi mata…

Haka TAUDHAT hauka ba sauqi. Sai dai kawai muyi mata fatan samun sauqin nan gaba.????

YAWO da MUSLEEMA da Adams harda NUFAISAT da Ammi sunje rugar malam jauro sunyi mai godiya da kulawar da yaba ADAMS. inda yaji dad’in Sosai dan yaci gaba da ciwata ma Yawo dabbobinta.. Daga qarshe dai haka yawo. Tace ya riqe shanun sun bar mishi
Har kukan dad’i sanda Malam jauro yayi musu.

Mutan Rugar ko sunyi mamakin ganin Adams da tunanin dama haka yake babban mutum…

Haka dasu dawo MUSLEEMA bata manta da Hafsat wacce tatemaka musu a gidan Hajjiya Batula ba
Dan takanas ta kano Adams yasa jabi’an tsaro dasuje su akama Hajjiya Batulan
Abin yayi kyau sosai dama idan kaji irinsu suna cika bakin bata yanda za’ayi a kamasu to sai dai idan basu tab’o yaran manyan masu kud’i ba..
Hafsat tayi murna sosai da irin karamcin da MUSLEEMA tayi mata..
Dan kud’i me yawan gaske ADAMS ya bata kan tayi aure taja jari karta qara zuwa aiki wani gida..
Anan MUSLEEMA take tambayarta yanda suka kaya bayan tafiyarsu. Sai Take bata labarin ai ba yanda tayi amma tayi mamaki sosai dan tayi bincike kowa ya tabbatar mata baiga fitansu ba…

Wata ranah


Wannan ranah itace mummunar rana gareni ni MUSLEEMA????????????????????…

(Rufe Diaryn da nake karanta wa nayi ni Rahma nalele da kallan Junior Ramadan nace.. “Tun kan naji wannan rana naji gabana ya faɗi da ita… Pls gayamin mezai faru.. Murmushi junior yayimin da cewa… “Duk nasan abinda ya rafu a wannan ranar bazan iya gaya miki ba. Kawai bud’e diaryn kici gaba da karantama masoya LEEKITAN ZUCHIYA.. Jan numfashi nayi da bud’ewa kamar yanda yace min naci gaba da karatu kamar haka…)
????????????????????????????????????????????????????????????????

Yau MUSLEEMA tun da safe takejin gabanta na fad’uwa.
Tarasa meyasa takejin hakan..
Dan haka kasa hak’uri tayi tatashi tanufi shashin NUFAISAT dan ta gaya mata..
Lokacin qarfe takwas dai dai na safen. Dan harsu Khalit sun tafi skull..

Anan falo taganta ita da adams kanta na bisa kan cinyar ADAMS d’in. da alama ADAMS d’in ya gama breakfast ne yake dan hutawa kan takwas da rabi tayi ya ficce zuwa office…
Da damuwa MUSLEEMA tazauna gefansu tace.. “Auntyna yau narasa me yake min dad’i a duniyar nan.. Gabana sai fad’uwa yake. Kamar wani abu zai faru da wanda nake so…

Murmushi NUFAISAT tayi mata da tashi tadawo kusa da MUSLEEMAN tace.. “Ki kwantar da hankalinki.. Insha Allah ba wani abu dazai faru.

Tashi ADAMS yayi da zuwa kusa dasu ya kama hannun MUSLEEMAN yace… “Babyna ki kwantar da hankalinki kamar yanda Auntynki tace insha Allah ba abinda zai faru kinji..

Kuka MUSLEEMA tasa musu da cewa… “Wallahi bakuji yanda nake ji bane araina ji nake kamar zan rasaka Ya ADAMS.. Kamar zan rasaki AUNTYNA.. Kamar zan rasa YAWO.. Kamar zan rasa YARANA.. Kamar zan…
ADAMS bai barta ta qarasa ba ya rufe mata baki da cewa .. “Ya isa haka…

Shuru MUSLEEMA tayi cikin zubar hawaye saita kalli NUFAISAT ta kallesa..
“Bana san kiyi yin irin wannan maganar Babyna. Koda ace kina jin hakan kamata yayi kifara gayama Allah kafin ki gaya mana… Adams ya fad’i yana me janye hannunsa daga bakinta..

Ita dai MUSLEEMA shuru tamai dan bazasu gane me takeji aranta bane..

Itako NUFAISAT murmushi taqara sakar mata da goge mata hawayen dake zubo mata Tace.. “Bafa komai dazai faru K’anwata.. Kidena kuka bana so..

Murmushin yaqe MUSLEEMA tayi mata da janye hannunta daga na Adams takama hannun NUFAISAT d’in tace.. “Auntyna ina san kigayamin wani abu dan Allah..
“Toh ina jinki MUSLEEMA..
“AUNTY kimin alqawarin bazaki tafi ki barni ba..
“Haba MUSLEEMA.. Idan nabarki inyi rayuwa dawa.
“Yauwa AUNTY dan Allah karki barni kinji… takai qarshen zancen nata da qara zubo da wani hawayen..
ADAMS baya san kukan d’aya daga cikinsu dan haka tayar da MUSLEEMAN yayi da rungumarta yace.. “Kije d’akinki kiyi sallah raka’a biyu kiroqi Allah yasa koma menene kike tunani yasa yazama alkairi.. Yana gaya mata hakan ya saketa dayi mata nuni da hannu akan taje kartaji komai..
Har takai ƙofar fitta tajuyo da kallanta garesa tace.. “Dan Allah YAYANA karka barni kaima Wallahi ina sanka..
Kallan junansu sukayi shida NUFAISAT kana suka maida kallansu gareta yace da ita.. “Toh bazan barki ba shikenan..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button