LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bama wannan ba. Shi Wanda zanyi dominsa baci zaiyi ba..
Ko kin manta yanda nasha wiya wajen cusa masa San cin girkin TAUDHAT
Kinsan Daga na Ammeensa saina nata Yanxu kawai yakeci
Jan numfashi Zainab tayi da cewa.. “Toh meyasa yau kikesan kiyi masa da kanki..
Bayan nasan shine yake had’a muku breakfast..
“Ki bari kawai y’ar uwa.. Ina San ganinki pls idan kin tashi daga office yau
Ina san gaya miki wani abu..
“Ok.. Zainab tace da ita.. Sannan tagaya mata yanda zatayi..
Cikin iko na Allah ko sai tayi dai-dai da yanda tagaya matan…
Dan duk gidansu Zainab ce kawai tayo momynsu wajen iya girki..

Shidai ADAMCY daya dawo yayi mamakin ganin NUFAISAT a kitchen.. Bama wannan ba. Mamakinsa yafi tsayawa akan yanda yake jiyo ƙamshin farfesun kaza..
Yasani wannan aikinsa ne na safe ????
Murmushi kawai yayi da girgiza kai yayi part d’insa yana dad’a jin mamakinta..
Dan yafi kowa sanin koda wasa NUFAISAT bata shiga kitchen dasunan wai tashiga dan yin girki..
Wato Kishiya ba abinda bata saka mata…
Haka yata surutansa a ZUCIYA.. Har yayi wanka da saka kayansa ya feshe jikinsa da turaransa me maƙalewa azuciya..
Kana ya nufi wani shashi na gidan nasa Wanda yake basa damar ganawa da baƙinsa..

Watoh tunda yau ta kasance asabar.. Baya zuwa asibiti ranar asabar da Lahadi
Kawai yana zuwa kasuwancinsa ne.. Amman kafin nan yana ganawa da talakawa way’anda basu dashi wajen temaka musu daga ƙarfe takwas da rabi zuwa ƙarfe goma..
Toh da zaran ya gama dasu d’inne yake dawowa ga matarsa yaci breakfast d’in daya had’a musu. Kana ya nufi wajen kasuwancin nasa…
Toh yau ƙarfe takwas ya nufi shashin dayake ganawa dasu…
Kasan cewar yau Matar gidan tatashi da himma???? ta canjesa wajen girka musu abin da zasuci.
Hmmm yau zaici girkin NUFAISAT ya fad’i hakan aransa..

Itako bayan tagama jitayi jikinta ya dauki ƙamshin girkin.. Hakan yasa taqara shaqa wanka tayi shigarmu irinta hausawa. Inda tasaka wata doguwar rigar atamfa… Kasancewar kalan ja da bak’i ne saiya haskata… Ba abinda zai baka sha’awa sai d’aurin data kafa… NUFAISAT nada kyau naban mamaki.. Macece so sweet.. Abin San kowane namiji.. Matsalarta biyuce inji ADAMCY.. shine bata masa shagwaɓa yanda zatana tsuma zuciyarsa.. Kasancewarsa d’an luv.. Sannan bata iya girki ba..
Waƴannan sune matsalar agun ADAMCY..

Falo tadawo duk ƙamshi ya rufeta.. Anan ta zauna ta d’auki wani littafin sister Rahma Nalele me suna YA FARU AKAN KAINA daniyar San karantawa..
Saidai kash.. Bai cancanta amatsayinta na wacce akace za’ama kishiya zuciyarta tabarta haka kawai ba..
Dan haka kasa karatun tayi.. Tayi shuru kawai da afkawa cikin kogwan tunanin ya zatayi da ganin mijin nata da wata mace.. Tafi kowa sanin waye shi.. ADAMCY daban yake acikin mazaje… Komai ya iya.. Bataga abinda ADAM bai iya ba..
Yanxu duk abinda yake mata haka zaima wacce zai Aura…….

Jitayi an shafi gefan fuskarta.. Koda ta d’ago da kan nata ADAM d’in tagani.. Aiko nan ya sakar mata Murmushi yana me cewa.
“Nasan tunanina kikeyi. Banda abinki waya isa ya kwace miki ni.. Ƙaryar wata mace takwace miki ni uwar ƴaƴana..
Sanyayyan Murmushi tasakar mai da cewa.. “Har yau nakasa gane yanda akeyi kake gane tunanina…
“Saboda nine me GYARA TUNANIN NAKI..
Ina mamakin yanda kike manta cewar zuciyarki da tawa abu d’aya ne..
“Idanko haka ne. ya dace tunaninmu shima ya kasance abu d’aya..
“Tabbas.. Ya bata amsa da fad’in hakan. Yana me cigaba da cewa. Ƙamshi ya dami hancina.. Zan rigaki zuwa dining fah????
Dad’i ya cika zuciyarta.. Tatashi ahankali daniyar zuwa ga dining d’in.. Shi kuma ganin hakan yasa shi rungumarta ya d’ago da fuskarta izuwa kallansa yana cewa… “Anya akwai ranar da zatazo nadena ganin kyen fuskarki kuwa..
Lumshe ido tayi da bud’ewa Ahankali tace.. “Ranar na zuwa.. Dan gashi nan alamun sun fara bayyana Yanxu…
“Toh gayamin.. Ina alamun suke..
“Banda hakan. Mezaisa ka ƙara Aure..
“Izuwa gaba zanji ba dad’i idan kika ƙara alaƙanta maganar Aurena cikin maganata dake..
Shuru tayi najin wani iri.. Wai ADAM wane irin mutum ne.. Tafad’i hakan aranta.. D’an qara tsaida kallanta tayi akansa kad’an tace.. “Insha Allah bakina bazai qara gangancin furta wata kalma dangane da Auran naka ba…
“Dts gud my sweetheart.. Nasan kina San mijinki… Kina kuma tsoran wata ta mallake miki shi. Kina san ganin kin haihu dashi.. Kina fatan kasancewa dashi har iya qarshen rayuwa.
Ina sanki NUFAISAT. Adai yanxu yanda nake jin ZUCIYATA!!! Bana tunanin zanso wata mace!! Kamar yanda nake qaunarki..
“Da’ace zai kasance har iya qarshe rayuwa zakaji hakan aranka ba iya yanxu ba. Dana tabbatarmah da kaina!!! Nayi dace duniya walahira
Cikin wani hali ya bata amsa da cewa. “Todai a’iya yanda nake jinki araina.. Ina tabbatar miki da cewar.. Kice afarkwanfarko cikin matan dazan rayu dasu cikin Auratayyata.
Zatayi magana sai yayi saurin had’e bakinsa da nata Yana me juya harshensu cikin wani hali..
Sanin makomarta Idan tabari ya d’auki lokaci ahakan yana me mata kiss d’in.. Shiyasata yimai cakulkulu tana me kyalkyalewa da Dariya…
Aiko nan take yasake yana cewa… “Watoh kinyimin hakan dan nabarki ko
“aa… Kawai gani nayi kana shirin cinyemin baki nah????
Da Murmushi yace “aiko da gaske wata ranah zan iya cinye miki shi.
Dariya taqarayi da kama hannunsa suka nufi dining tana cewa.. “Naka ne Mijina. Kayi duk yanda kaga dama dashi… Dan bani fatan naga ranar dazaka dena nunana qaunarka garesa

Murmushi yayi dai dai lokacin daya zauna tana qoqarin zubamai farfesu… Bayan tagama ta tura mai kwan data soya had’e da had’a mai komai Wanda ya dace dashi.
Sannan ta zauna itama ta d’an saka nata agaba cikin tsoron Allah yasa bata kwafsa ba..

Shuru ADAMCY yayi lokacin daya kwurb’i ruwan Lipton din data samai dan baya shansa da madara..
Eh.. Tayi qoqari ba lefi. Duk da cewar tamanta da abu biyu.. Wato ganyan na’a na’a da ganyen giris..
Yaji ba dad’i lokacin daya kai warnar kwan nan bakinsa..
Dan magi yayima kwan yawa over
Gashi ta kafesa da ido..
Kawai jira take taga me zaiyi
Ganin da tayi ya rintse ido sanadin kai wainar kwan bakinsa.
Tasan Daurewa kawai yayi ya had’iye..
Zai qara tayi saurin riqe hannunsa Kamar zatayi kuka take cewa.. “Ban sanka da fulako ba.. Alamu sun nuna banyi abinda ya dace ba.. Idan nayi duba da yanda ka rintse idanka yayin had’iyewa.
Shuru yayi mata..
Ganin hakan yasa tad’an gutsiri kad’an takai bakinta…. Aiba shiri tadawo dashi.. Dan magin yayi yawan dazai iya yima mutum illah..
Shuru tayi da sunkuyar da kanta..
Bai mata magana ba ya jawo farfesun kazar yakai bakinsa yana addu’ar Allah yasa tayi dai dai ashi..
Aiko addu’arsa ta karb’u.. Dan yayi dai-dai irin kadaran kadaham d’innan..
Dan haka ya zage yaci sosai..
Bayan ya gama ya kalleta kad’an dayin Murmushi dan har lokacin bawai ta d’ago da kan nata bane..
Kan natan yana qasa da alama ma kuka takeyi..

Jawo biran dake jikin rigansa yayi da wata y’ar fefa. Nan yayi mata wasu rubutu kad’an ya ajiye mata… Kana ya tashi da d’aukar laptop d’insa da wayoyinsa ya ficce daga falan yana addu’ar fita daga gida…
Sanda taji tafiyansa shida maso tsaran nasa. Sannan ta d’ago da kanta ta sauke akan farar takaddar daya ajiye mata..
Ga abinda yace..

Da’ace haka kike min tun da farko dana qara sanki da qaunarki.. Gaskiya ban taɓa cin farfesu me dad’in Wanda naci yanxu ba. Dan haka ina sauraran qaracin wani irinsa da rana idan zan samu..
Kisani Yanxu bana San naqara cin girkin TAUDHAT.. Idan kika bari wani ko wata ya qara saka miki hannu akan abinda zanci daga gareki!!! Lalle zanji ba dad’i. Zanji kamar kin munafunceni. Zanji zafinki sosai. Aqarshe koda kinyi nadama. Bazan kalleki ba..
Ina sanki matata..
Kidena wannan kukan da kikeyi.. Dan zai iya ɓatamin farin cikina ayau…
Sannan ki qara nutsuwa sosai wajen saka magi akwai. Dan idan kikaci gaba da sakawa da yawa kamar hakan… Lalle bazanƙici ba. Saidar cuta takamani.. Dan ayanxu nayima zuciyata alƙawarin duk abinda kika dafa zancishi ko Yaya yake..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button