LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka MUSLEEMA take bana wasa ba. tana zuwa wajen NUFAISAT tajijjigata taje wajen ADAMS ta jijjigasa tana rokwansu dasu tashi suci gaba da rayuwa..

Kaf doctors d’in asibitin da ma’aikatan asibitin ba wanda bai tausayama MUSLEEMAT ba…
Sannan sun tsinci kansu da mummunar fad’uwar gaba da suka fahimci DR ADAMS LEEKITAN ZUCHIYA ne da matarsa tafarko NUFAISAT sune suka rigamu gidan gaskiya. Anan wasunsu masu raunin zuciya suka fara kuka wiwi… Suna fad’i dole MUSLEEMA ta shiga tashin hankali dan sunfi kowa sanin waye ADAMS. Haka suna samun labarin matarsa NUFAISAT da kirkinta da haƙurinta kamar yanda duk abinda kakeyi idan mutane na kanka….

Aqarshe dai bayan Dr Aryan ya samu daidaituwar numfashin YUSUF sai yasa ma’aikatan wajen dasu kaisa wani d’akin. Kana ya kalli MUSLEEMA da zubar hawaye dan mutuwar ADAMS d’in tashigesa sosai shida matar tasa NUFAISAT.. Cikin wani hali ya kama hannun MUSLEEMA da cewa “kiji hak’uri MUSLEEMA.. Amma kin rasa NUFAISAT da ADAMS rasawa irin wacce ba’a dawowa

Tsayawa cak MUSLEEMA tayi da kallansa cikin matuqar qarin shiga razana tace.. “Da gaske… D’aga mata kai yayi alamar tabbatarwa… Aiko tana ganin hakan tafad’i qasa luuuu sumammiya…

Mahaifan ADAMS
Mahaifan NUFAISAT
Mama Mahaifiyar TAUDHAT
YAWO
Y’an uwa da abokan arziqi
Jama’ar gari..
Ba wanda bai zubda hawaye akan mutuwar ADAMS da NUFAISAT ba..????
Mutanan azziqi.. Masu gaskiya da amana. Masu san mutane. Masu ruk’o da addini. Masu yarda da qaddara..

(Ina san nidake dakai me karanta wannan littafi nawa na LEEKITAN ZUCHIYA muyi koyi da kyawawan halaye irin nasu.. Dan muyi mutuwa irin tasu. Irin mutuwar da kowane musulmi yake so. Wato cikawa da kalmar shahada. Bacin hakan jama’ar gari da yan uwa suyi kukan rashinmu. Suta fad’in alkairin mu. Suna binmu da kyakkyawar addu’a irinta fatan alkairi agaremu.)

Ammi da Dady sunyi kukan rashin ADAMS da NUFAISAT kamar ransu zai fitta..
Haka mommy na NUFAISAT da Dadynta da ƴar uwarta Zainab sunyi kukan rashinta kuka bana wasa ba..

Haka Yusuf bai tab’a tunanin zai rasa ADAMS nan kusa…
Dan qaunar ADAMS yake har cikin b’argwansa..
Komai jiyayi ya tsaya masa cak dan ganin yayi babban rashi arayuwarsa.
Ya saka a zuciyarsa zai rayuwa da MUSLEEMA rayuwa irin ta gaskiya da rukwan amana..

Haka MUSLEEMA ta bala’in fitta daga harcinta ganin rashinsu da tayi.
Ta kamu da ciwan ZUCIYA dan akwalla ya ibeta shekara d’aya kafin aka samu kanta da lafiya..
Kullum tunaninta YAYANTA ADAMS da AUNTYTA NUFAISAT sun tafi sun barta…
Ni akayima mutuwa ba kowa ba. Hakan take fad’i dazaran an sakata agaba dan taci abinci ko ana mata fad’a kan tatsaida tunaninta…

Itama Haneepha shekara biyu tsakani tabi bayan NUFAISAT da ADAMS.. Sakamakwan amai da gudawa da tayi….



Dake Yusuf ya saka aransa zai rayu da MUSLEEMA zai aureta. Sai kawai yaji aduniya ba macen da yake so kamar ita..
Dan haka bayan rasuwar Haneepha da wata biyu yaje gun Ammi yace mata shifa yana san a d’aura masa Aure da MUSLEEMA..
Lokacin MUSLEEMAN tana falan alokacin da yake maganar..
Dan haka Ammi tace mata to taji abinda Yusuf d’in yace shin ta’amince..
Kallan Ammi tayi hawaye ya zubo mata da cewa.. “Wallahi na amince tun sanda Ya ADAMS yace mai ya Aureni..
Murmushi Ammi tayi da sunkuyar da kai tashare hawayenta dan bata san taji an ambaci ADAMS d’in.. Yanxu yanxu sai qewarsa ta dameta..????

Daurewa YUSUF yayi da qarasa wajen MUSLEEMAN ya share mata hawayen..
Da cewa.. “Gobe nake san a d’aura mana Aure Babyna..
Kallansa da sauri MUSLEEMA tayi dan aduniya bata ba mance duk wata kalma da ADAMS ya kirata dashi….
Dan haka Ahankali tace.. “Ko yanzu ne INA san a d’aura Ya Yusuf..
Qara share mata hawayen yayi da fad’in.. “Kin tabbatar..
Da sauri ta d’aga masa kai alamar tabbatarwa..

Saiko ya tashi da kallan YAWO yaci gaba da cewa. “Zamma Dady magana yanxu YAWO. Tunda gobe jumma’a ne za’a d’aura Auran namu bayan idar da sallar jumma’a.. Dan Allah YAWO kar kibi tasu Ammi kan saisun sharyamin ita kafin akawota. Kawai idan dai dare yayi akawomin ita haka. Danna shirya mata komai.. idanko kunyi zanzo da kaina na d’auki abata… Yana fad’in hakan ya ficce daga falan ya nufi wajen shaqatawar gidan dan ganawa da Dadyn..

Murmushi ammi tayi cikin matuqar qaunar YUSUF.. Dan tunda suka rasa ADAMS ya qara shige musu yana nuna musu idan sun rasa adams ai suna dashi shi da Salim..
Wannan abu yana yima Ammin dad’i..

Haka YAWO tasa ammi tasaka aje wajen masu saidai maganin gargajiya anemo mata wasu saiwa ta had’ama MUSLEEMA maganin manta da bazawa kake tare. Kawai kalleta a budurwa..????

Aiko nan Ammi tasa y’an aikinta sukaje suka samoma yawo duk abinda take buqata..
Sannan ta daka na dakawa tabada na dafawa a dafa mata..

Nan tahad’ama MUSLEEMA me zafi????.
Ita kanta MUSLEEMA duk da a ranar tafara amfani da had’in amma sanda taji canji ajikinta..
YAWO fad’i take dama saboda y’ar albarka NUFAISAT naqi yimiki had’in mallakar miji. Saboda nasan idan nayima NUFAISAT d’in haka ban kyauta mata ba. Amma yanxu tunda Allah ya d’auke su Yusuf ya shiga uku..????
Murmushi MUSLEEMA tayi Kawai tana qara tuna NUFAISAT da mijin nata ADAMS..
Nan hawaye ya zubo mata. Itama YAWON hawayen ne ya zubo mata tayi saurin sharewa wai dan karta qara karyarma da MUSLEEMAN zuciyata..

Aiko a washe garin ranar aka d’aura Auran YUSUF da MUSLEEMAN..
Auran daya tara manyan mutane.. Dan abokan takar YUSUF da ADAMS ba qaramin qarama YUSUF d’in Farin jini tayiba agun jama’a.. Hakan yasa aka san YUSUF d’in kamar yanda aka san Adams d’in..
Haka kuma kunga Dady ne yaba YUSUF d’in Auran MUSLEEMAN
Wannan yana d’aya daga cikin abinda yasa Auran ya samu Albarkan matane masu mugun yawa..

Aranar ko aka kai MUSLEEMAT gidan YUSUF.. Gidan da YUSUF ya d’au shekara da shekaru yana tsari akansa…
MUSLEEMA tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fitta.. Sakamakwan tunawa da tayi ashe zamanta da ADAMS da NUFAISAT na d’an wani lokaci ne..????

Kafin akaita gidan sanda YAWO tace mata karta kuskure tabari YUSUF ya tare da ita awannan rana tadai bari sai bayan tagama shanye maganin tunda na sati d’aya ne..
Toh MUSLEEMA tace mata sannan suka mata nasiha sosai aka kaita gidan YUSUF d’in..

Salim qanin ADAMS ne kawai ya rako YUSUF d’in gidan nasa.. Dan yanxu shine wanda YUSUF d’in ya yarda daya shiga al’amuransa.. Kasancewar yayaba da Hankalinsa

Tsiya Salim ya shiga yima MUSLEEMA akan wai takula mai da yayansa akaro na biyu kamar yanda takula mai dana farko imba haka ba zai hukuntata.. Murmushi Kawai MUSLEEMA tayi kanta na cikin mayafi kamar dai yanda amarya me kunya takeyi idan ankaita d’akinta..
Bayan Salim d’in ya tafi kulle makeken gidan nasa YUSUF yayi da dawowa gurin MUSLEEMAN.

Ahankali ya d’ane gadan da yaye mata mayafin kan nata yana cewa.. “Haba Babyna. Wannan rufe kai haka aisai zafi ya illatarmin dake..
Murmushi tasakar mai..
Saiya kama hannunta taji wani zirr shima yaji amma yayi fuskar daci gaba da cewa.. “Mu biyu iyayanmu suka Haifa Baby. Daga ni sai qanwata..
Ina matuqar santa da yawa dan haka ina san kema ki sota dan Allah da gaskiya dan yanzu bata kowa saike.. Kinga Hajjiyanmu me kula damu bata nan. Tabi bayansu ADAMS.. Dan Allah matata karki saka wani abu aranki akan qanwata wanda zaijamin matsala dake..
Ina sanki MUSLEEMA Sannan ina san qanwata.. Ina san kizama uwa agareta tun daga yanxu duk da cewar zama ta iya girmanki Kinji..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button