LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka TAUDHAT tasaka kayanta da barin dajin zuciyarta tam cike da farin ciki….

Muje zuwa masu karatu.. Auntyn luv takuce

[6/11, 11:56 AM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 08☆

Da mutuƙar ɓacin rai NUFAISAT ta jefar da gyalanta akan kujer falan nata..
Nan tahau zaga ɗakin tana me cije leɓe da tunano abinda ya faru tsakaninta da TAUDHAT..
TAUDHAT ta yaudareta.. Yaushe TAUDHAT ta lalace haka.. Yaushe tunaninta ya juye haka. Yaushe al’amuranta suka canja haka..
“Hmm mutum kenan..
Ta furta hakan abayyane tana ƙoƙarin zama.. Saidai kanta idda zaman nata. Zainab yayarta tashigo falan da sallama…
Aiko da sauri taje ta rungumeta tana me fashewa da kuka. Faɗi take… “Ashe haka mutum yake Aunty Zainab.. Ace kaf mutanan duniya arasa wacce zata yaudareni sai TAUDHAT…
“Ke waime yake faruwa ne.. Zainab ta tambayeta hankali tashe lokacin da tasamu nasarar zaunawa kan ɗaya daga cikin kujerun falan tare da ita…
Babu ɓata lokaci nan NUFAISAT ta kwashe duk abinda ya faru tsakaninta da ADAMCY daran jiya da yau da safe.. Sannan taƙare da bata labarin abinda ya wakana tsakaninta da TAUDHAT..
Shuru Zainab tayi cike da mamakin komai..
Ta tausayama ƴar uwar tata Dan tasan kishiya da zafi take.. Sannan tasha mamakin TAUDHAT matuƙa
Cikin wani hali ta dubi ƴar uwar tata tace.. “Kwantar da hankalinki sister.. Kishiya ba abar tada hankali bace.. Musamman idan kika yarda da kanki.. Nasan tunanin dazai fara ziyartar kwakwalwarki duk lokacin da kika tuna za’ayi miki ita.. Shine baki haihu ba. Kina tsoran kar mijinki ya wulaƙantaki.. Kina tsoran kar sanadin hakan kishiyar ta rainaki..
NUFAISAT karkisa tunanin ko ɗaya daga cikin waƴannan aranki. ADAMS ba irin waƴannan mutanan bane.. ADAMS bazai taɓa wulaƙantaki ba.. B’cos yana miki wani so. Wanda yafi ƙarfin akirasa da MASEEFAR SOOH..
Zaiyi Auran ne dan mahaifansa badan ya gaji da ƙaddarar da Allah yasaukar miki ba…
Kiyi nazari. Kiyi tunani. Ki nutsu kiyi amfani da iliminki wajen kishin da yake shirin tumfaroki.
Kiyi hakuri kamar yanda mummy ɗinmu tayi lokacin da Dadynmu ya qara Aure..
Amatsayina na ƴar uwarki.. Zan nemi wata alfarma daga gareki.. Karki ƙara kaima wani kukanki imba Allah ba..
B’cos ba abinda wani zai iya yimiki akan abinda Allah ne ya lamince musu da suyi..
Nasanki da ibada. Toki dage wajen gayama Allah buqatarki kamar haka…. ALLAH KAINE ALLAH. ALLAH BA WANI SARKI A BAYAN KA ALLAH. ALLAH NA ROK’EKA IDAN WANNAN AURAN ALKAIRI NE AGARENI DA MIJINA ALLAH KA TABBATAR DA ALKAIRIN.. ALLAH IDAN BA ALKAIRI BANE AGAREMU ALLAH KA HANA YUHUWARSA. ALLAH IDAN YA KASANCE SAI ANYI. ALLAH KADUBENI DA FUSKAR RAHMA. KAYAYEMIN KUNCI DA BAQIN CIKI DA TASHIN HANKALI DA DAMUWA. BAMA NI NASAN KA YAYAEMIN BA. KOWA DA NAKE TARE DASHI YA SHEDA HAKAN. ALLAH KA DORANI AKAN MIJINA DA ABOKIYAR ZAMANA. KA HANA MUNAFUKAI DA MAHASSADA SHIGOWA CIKIN AL’AMURANA DA MIJINA DA ABOKIYAR ZAMAN TAWA.. ALLAH KA MALLAKAMIN MIJINA. KA HANESA KUNTATAMIN KAHANESA WULAƘANTANI KA HANESA AIKATAMIN ABINDA ZAISA MAQIYANA SUYIMIN DARIYA. ALLAH NABAKA AMANAR KAINA. DA DUK WANI ABU DAYA SHAFI RAYUWATA. KA KYENTANI FIYE DA WANNAN BAIWAR TAKA DA ZAKA HAD’ANI ZAMA DA ITA…
Sister ki dage da wannan addu’ar karki qara yarda da wata qawa arayuwarki..
Batun TAUDHAT idan tazo gareki. Karki nuna mata kin canja mata matsayi afuskarki. Nuna mata tabi Allah. Tadena aikata duk wani abu da wannan matar tagaya miki akanta… Daga nan saikice mata daga yau ba’ita bake..
Karki kuskura ki qara qawance da TAUDHAT.. Nagaya miki..

Share hawayenta NUFAISAT tayi da kama hannun yar uwar tata tace. “Insha Allah Aunty Zainab zanyi duk abinda kikace min..
Nagode ma Allah daya bani ƴar uwa kamarki. Kin bani shawarar dazata kaini ga hanyar dacewa..

“Yauwa ƴar uwata.. Ki sama zuciyarki hakuri da dangana. Komai yayi farko zaiyi qarshe kinji
Gyaɗa mata kai NUFAISAT tayi alamum amsawa…
Haka dai Zainab tadinga kwantarma da NUFAISAT hankali har NUFAISAT ɗin tafara tunanin toh kishiyar tazo mana mezata tare mata..????
Nan Zainab tatayata abincin ranah wanda za’a kaima ADAMS d’in. Ta koya mata wasu qananun abubu na girkin saboda yamma tayi tana San tafiya gida…

Ba qaramin farin ciki sosai NUFAISAT taji ba. Lokacin da mijin nata ya kirata awaya yana nuna mata farin cikinsa na yanda yaji dad’in abincin da ta aikomai

Da misalin qarfe shidda ne TAUDHAT tafesa wankanta me matuƙar kyau. Ita kanta bata buqatar ace mata tayi kyau dan da gasken gaske tayi kyau d’in.. Cikin jar atamfa me ratsin blue. ɗinkin doguwar riga me bajajjen hannu irin na yara ƴan zamani.. Sosai ɗinkin ya karɓi jikinta abinka da farar mace..
Nan tafeshe jikinta da turaran da boka yabata. Kana tad’auki jakarta da gyalanta ko kallan mahaifiyarta batayi ba tasaka takalminta taficce daga gidan sai gidan NUFAISAT…

Dake lokacin NUFAISAT take sakaran dawowar ADAMSY kasancewar lokacin lokacinne lokacin dawowawarsa. Hakan yasa take fes da ita kamar yanda tasaba kimtsa kanta kan lokacin dawowarsa..
Tana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun falan nata TAUDHAT tashigo da sallama murya a sanyaye…
D’auke kanta NUFAISAT tayi bayan ta amsa mata sallamar..

Amunafunce TAUDHAT tazauna tana me fuskantar NUFAISAT d’in cikin sanyin murya tace.. “Nasan da cewa ban kyauta miki ba. Ina neman gafararki. Dan Allah kiyafe min. Hakan baza taqara faruwa ba. Wallahi nayi miki alƙawari..
Ahankali NUFAISAT ta kalleta da cewa… “Karki nemi gafarata TAUDHAT. Kije kinemi gafarar Allah. Dan nasan kinfi sab’a mishi fiye dani.. Nasani kin sani.. Dan haka kiji tsoran Allah ki koma garesa kidena aikata duk abinda wannan matar tafad’a min akanki. Ki tuba ki koma ALLAH. Allahn yasa mu dace gabaki d’aya amiin…

“Nagode NUFAISAT. Kuma insha bazan qara aikata ko d’aya daga cikin abinda kikaji ba…. TAUDHAT tace da ita hakan…

Kan NUFAISAT tayi magana saiga ADAMCY ya shigo falan da sallama...

Da wani yanayi NUFAISAT taje ta rungumesa tana me nunamai farin cikinta naganinsa da tayi
Gaskiya ADAMS yaji dad’in hakan. Kasancewar bata saba yimishi hakan agaban TAUDHAT ba..
Yana San tadinga bashi kulawa agaban kuma waye ba wai TAUDHAT bama..

“Wow uwar gidana. Kinga yanda kika tafi da zuciyata kuwa..
“Hmm.. aikai LEEKITAN ZUCHIYA ne. Tunda natafi da ita. Sai kasan yanda zakayi kadawo da ita..
Lakuce mata hannu yayi cikin matuƙar farin ciki yace.. “Abubuwa biyu sun sauya daga safe zuwa yanxu..
“Toya zanyi da raina????. Tunda na ɗaura ɗammarar bama megina dukkanin abinda zai sashi farin ciki…
Qara rungumarta yayi cikin so da k’auna… Kana yaɗan zareta kaɗan daga jikinsa ya kalli TAUDHAT tare da sakar mata murmushi yace. “Yau qawarki ta shareki takulani ko.
Murmushin itama ta mayar masa da cewa.. “aidama abinda yadace dani kenan Idan dai kana cikin gidan nan…
Tafadi hakan da tashi tana me sab’a jakarta ta ƙaraso kusa dasu yanda ADAMS zai shaƙi ƙamshin tana. Tana meci gaba da cewa.. Nizan tafi..
“Tofah???? yau bazaki bari ya rage miki hanya ba.. Cewar NUFAISAT
Kan tayi magana sai ADAMSY Wanda kansa yayi masa wani dum kasancewar ya shaqi qamshin turaran na TAUDHAT. ya sakarma NUFAISAT kiss awiya. Wanda yasata qanqamesa a lokaci d’aya kuma ta kallesa. Yace.. “Barta tatafi sweetheart. Yau bazan rage mata hanya ba. Kasancewar tasaka wani turare mara dad’i. Saidai duk da hakan yana tab’a ZUCHIYA.. Yana aika mata da wani saƙo. Sakwan da yake barazanar tarwatsata…
Azahirin gaskiya idan nace zan d’auki lokaci ina shaqar qamshin. Ba makawa komai zai iya faruwa da ZUCHIYATA…
Afurgice NUFAISAT tazare jikinta daga nasa. Taqara tsaida idanta akansa sosai tace.. “Ba wani saƙo dazaiyi barazanar tarwatsa ZUCHIYARKA idan har banice nabaka wannan sakwan ba.. Mezaisa kaji hakan daga TAUDHAT..
Taɓe baki yayi tare da kallan TAUDHAT ɗin ya maida kallan nasa kanta yace.. “Bansan me zance miki ba. Kasancewar yau nafara jin hakan. Kuma..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button