LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
“Kuma me…. Sannan meyasa kaji hakan… NUFAISAT ta katseshi da faɗin hakan cikin sauri..
Da wani hali Yakama hannunta da cewa.. “Nima ban sani.. Ya kamata kiyi wani abu akai. Dan yanayin yana qara shigata sosai fah..
Saurin kallan TAUDHAT tayi wacce kawai tayi saƙale tana kallansu kamar bata gane me suke cewa ba tace da ita.. “TAUDHAT kificce daga falan nan kije gida kawai sai nazo. Dannafi buqatar daidaituwar ZUCHIYAR MIJINA fiye da tsayuwarki anan…
"Laaa????. Karki damu!.. Wata ranah nidake zamu daidaita zuciyar inda muna raye.. TAUDHAT na faɗin hakan taficce daga falan zuciyarta tam farin ciki. Dan tasan tunda ya shaqi qamshin. Kuma ya magantu akan qamshin tasan yarigada ya shigo hannu...
Saidai tatsorata sosai ganin bai rikice ba
Dan tatab’ama wani alhajinta shigen irin hakan. Alhajin na shaqar qamshin. Nan take ya rikice mata.. Tobataga hakan agun ADAMCY ba. “Hmm. indai kere na yawo zabo na yawo wata ranah zasu had’u..
Tafad’i hakan abayyane lokacin da masu gadin gidan suka bude mata get d’in gidan danta fitta….
NUFAISAT ta kalli ADAMS tace.. “wai me TAUDHAT take nufi da wannan kalmar na zumu dai-daita ZUCHIYAR nida ita.
Janta ADAMS yayi izuwaga shashinsa yana cewa.. “Ki kula dani awannan lokacin yafi ki tsaya kina min wannan wawiyar tambayar…
Shuru NUFAISAT tayi kawai bayan sun kasance a bedroom nasa tana me tayasa cire kayan jikinsa dan yashiga wanka…
Muje zuwa. Rahma nalele ce???????? taku ƴan hannuna…????????
[6/11, 11:57 AM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 9☆
Bayan ya fitto ya tarar da kayan data fito mai dashi na bacci
Doguwar rigace dai me santsi. Sanda ya feshe jikinsa da turare da mayika kana yasaka da gabatar da sallar magrif saboda lokacin da ake kira har akayi sallar yana wankan.
Sanda ya sallame sannan ya fitowa falan yana me wurga ido alamun nemanta. Aiko can ya ganta kan dining tayi dagumi kawai alamar tana cikin wani hali.
Rungumarta yayi ta baya batare dayace komai ba.
Can data samu nutsuwa daga d’uminsa saita kama hannunsa ta zaunar dashi kan d’aya daga kujerun wajen wacce yafi zama akanta. Ta had’a mishi komai na abin data girka masa tare da zuba nata ta zauna idanta cikin nasa tace. “Ina fatan wannan yafi na d’azu dad’i. Murmushi yayi tare da cewa. “Ai daga ganinsa zaifishi dad’n. Musamman idan nayi duba da yanda yaketa zuba qamshin nan.
Murmushin jin dad’i tayi da fad’in. “Saidai kamin afuwa abisa Kalmar daka fad’i d’azu. Na wai karna qara bari wani yasamin hannu akan abinda zakaci.
Wallahi duk aunty Zainab ce tasamun hannu daga na d’azu harna yanxu da zakaci
“Karki damu matata. Saida nayi furucin nagane dole sai ansaka miki hannu kafin nasamu yanda nakeso.
Murmushi tayi dad’an duqawa ta sakar mai kiss agoshi tace. “Nayi maka alqawari mijina. Daga aunty Zainab ba wacce zata dinga samun hannu akan abinda zakaci. Ita d’imma nawani d’an lokaci ne. Dantace 2 month kawai zata d’auka tana koyamin
Murmushi yayi shidai yana San matarsa. A hankali yace mata. “Allahma yasa ki iya a 1 month kawai.. “Insha Allah zanyi qoqarin iya duk wani abu Wanda nasan zai dace dakai Wanda zaka soshi. Ka qaunaceshi. Kaji dad’in shi koda a 1 month d’inne
Yaji dad’in furucinta sosai. Hakan yasa yace mata idan tagama taje ta canja kaya. Tace ina zasu. Yace yau rakiya zatamai zuwa gidansu dady amman saiya dawo daga sallar isha kannan ma itama tayi sallar.. Toh tace mai tare dajin wani mafificin dad’i saboda yanda yake kod’a abincin yana nuna mata santinsa azahiri danya qara qarfafa mata gwiwa
Haka daya dawo ya d’auketa basu zame ako ina ba sai’a gidansu.
Nan masu gadin gidan suka hau zubewa kamar yanda suka saba wajen girmama shi
Yayi musu kyauta me tsoka inda suka dinga saka mai albarka.
Anan babban falan gidan suka tarar da Dadyn nasa da Amminsa harda Hajjiya Rukayyat da Salim Nan suka sube suka shiga gaishesu.
Da farin ciki Dady da Amminsa suke amsa musu. Banda Hajjiya Rukayyat. Dan dama haka abin yake awajenta. Idan har Ammin ADAMS ce da girki bata sake fuska a wannan ranah. Dukko da cewar rabin lokacin nata ne..
Salim ya gaida Adams da NUFAISAT. Suka amsa da kulawa. Sannan Dady ya qara tsaida idansa akan Adams yana cewa. “Sannu ADAMS kunzo lafiya? “Eh Dady dafatan muma mun sameku lafiya. “aa lafiya lau lau. Yanxu nake maganarka kuwa da d’an uwanka Salim. Ashe kana kan hanya.
“Eh Dady. Allah yasa ba lefi nayi ba. ADAMS ya fad’i da murmushi cikin wasa.
Murmushin shima Dady yayi da cewa.. “Bakayi komai ba. Kawai hirar taka tazo ne. Nayi farin cikin yanda kazo min da NUFAISAT. Dan dama ina San mata magana akan Auran dana saka kayi.
Murmushi ADAMCY kawai yayi
Dady ya numfasa da kallan NUFAISAT yana me cigba da cewa. Kiyi hakuri NUFAISAT. Bawai zai qara Auran bane danke. aa zai qarane sabodani. Nasan kina da nutsuwa da hankali koda abin ya faru bazaki kawo wata matsala ba. Tuna hakan danayi shiya bani qarfin gwiwar ce mishi yayi. Allah yayi miki albarka ki dage da addu’a idan kina da rabo Allah yabaki me albarka..
Qara sunkuyar dakai NUFAISAT tayi cikin ladabi tace.. ” Dady ba komai insha Allah baza’a samu matsala daga gareni ba..
Murmushi Dadyn yayi cikin jin dad’in furucinta yace. “Allah yay miki albarka
“Ameen tace. Ammi tadafa kanta cikin jin dad’i tace. “Nagodema Allah daya bani sirika me hankali. Me kaifin tunani. Allah ya dubeki yabaki masu albarka.
Kwantar da kanta NUFAISAT tayi kan cinyar Ammin tana cewa amiin Ammina…
Tsaki Hajjiya Rukayyat taja tare da tashi tana kallan NUFAISAT tace da ita. “Kizo falo ki sameni Inasan magana dake. Tana fad’in hakan tabar falan afusace. Jiki asanyaye NUFAISAT takalli mijinta Adams Ya gyad’a mata kai alamar taje. Nanko tatashi tabi bayanta inda tataddata afalan nata tana zagaye.
“Momy gani. (Dake haka suke kiranta dashi )
Da sauri Hajjiya Rukayyat takalleta da cewa. “Ke wata irin shashashace. Waya gaya miki kishiya dad’ine da ita. Kishiya ba’abokiyar zama bace abokiyar gabace. Karki kuskura ayi miki ita. Banda sakarci irin naki wata macece me hankali zatayi abinda kikayi. Ko’an gaya miki so haukane.
Wallahi kika yarda Adams yayi Aure kashinki ya bushe agunsa. Bar ganin yanxu yana wani nuna miki so yana samun d’a daga wajen wata zaifara wulaqantaki yaga toke amfanin me kike masa daga qarshe ya turaki gidanku da farar takarda na saki….
Da sauri NUFAISAT takalli Hajjiya Rukayyat cikin matuqar tsoro. Itako ta gyad’a mata kai alamar tabbatarwa.
Gaban NUFAISAT yashiga fad’uwa ganin halin data shiga yasa Hajjiya Rukayyat cigaba da cewa.. Wallahi kima kanki qiyamal lalli kisan duk hanyar daza kibi kibi dan hana wannan Auran tabbatuwa. Idan kin kasa kizo zankaiki inda za’a share miki hawaye.
Gumi NUFAISAT tagoge da mayafinta tace da ita. “Toh momy zanyi tunani nagode.. Tana fad’in hakan taficce daga falan da sauri ta fad’a falan Ammi tazube kan ɗaya daga cikin kujerun falan tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun falfalangi.
Itako Hajjiya Rukayyat murmushin mugunta tayi tare da cije leb’e tana rayawa aranta wata qila ta’iya cin galaba akan NUFAISAT. Danta hango tsoro muraran akwayar idanta…
Murmushin jin dad’i tayi tare da gyad’a kai tashige bedroom d’inta