NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwantawa tayi jikinsa cikin shagwa6a tace”mancewa nayi fa bazan k’ara ba ai kaga ban fad’a ba ko,cike da yarinta tayi maganar,jan hancinta yayi”to ai nasan badon Umma ta gobjemin bakin Babyna ba yau da tayi 6aran 6arama,dariya tasaka”ai bazan sake ba amma fa naji zafi,hura mata bakin yayi “tom sorry my luv,
Gyara kwanciya tayi jikinsa Yaya Lameer barci nakeji,yace”kinyi sallah ko,tace”nayi tare ma da Kaka mukayi kafin kazo,yace”tom asha barci lfy,ya gyara mata kwanciya jikinsa,shi kuma ya d’auki romote ya kunna TV tare da rage k’ara lokaci k’ank’ani barci ya kwasheta daman ita bata da wahalar barci,
Bedroom ya kaita ya shimfid’eta kan gado,tare da ja mata barko ya koma farlour
Muje zuwa yawan comment yawan typing
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
_**NI DA YAYA LAMEER**_
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to my fans
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️5↪️6
Jin kiran la’asar yasa ya mik’e bedroom ya shiga,domin tada Ummi(Wato Zainab)ganin ankira sallah kuma koba haka bama barcin yamma ba ya da kyau,
Tafin k’afarta ya fara shafa mata a hankali,bud’e idanuwanta tayi tana ganinsa ta turo baki cike da shagwa6a,tace”nifa barcin nan bai isheni ba Yaya Lameer,kwa6e fuska yayi kamar yadda itama tayin yace”My Wife an kira sallah fa,mik’ewa tayi tana dire dare,
Kamota yayi yace”meye hakan Babyna,tace”ba kai bane kawai ina barcina,yace”tom sorry anjima zakiyi barci,muje kiyi sallah,
Haka suka shiga bathroom ya mata alwala yayi sannan ya kinkimota sai kan dadduma ya mik’a mata hijab,yace”to ayi sallah bari naje masallaci luv u so much,
MUrmushi tayi”luv u too Yayanah,kiss ya manna mata a goshi ya fice,
Bayan ta idar,cire hijab tayi ta nufi part d’in su Ammi tasan yanzu sun daw
o,
Taci sa’a kuwa a kitchin ta isketa tana had’a abinci,domin Ammi da kanta take girki bata yarda da sai ‘yan aiki sun girka mata ba,saidai suyi wanke wanke da shara da sauran abinda ba’a rasa ba,
Tace”yauwa Ammina kamar kinsan yunwa nakeji,murmushi Ammin tayi,kasa uwar barci kin tashi kenan ai na lek’a Lameer yace kina barci,murmushi ita ma tayi,tace”na tashi Ammi,
Kallonta Ammi tayi,saikizo ki tayani girkin kema don nan gaba ki k’ware sosai,turo baki tayi gaba,ta fara kunkunai,tasan abinda Zainab bata so kenan aiki musamman girki,tace”kai Ammi banfa iya ba,
Tace da hakan ai zaki kowa,ba don son ranta ba ta fara tayata saidai duk shirme ne,daga k’arshe Ammi tace ta bari kawai,cike da murna ta koma farlour bayan ta had’a tea ta koma tanasha kafin agama girkin,
Da dare bayan anyi sallar isha’i wajen takwas da rabi gaba d’aya suke zaune kan dinning table suna cin abinci,
Zainab tace”Ammi fa kin iya girki,dariya sukasa tace”ai shiyasa nakeso kema ki koya don wataran ki yi da kanki,Lameer yace”haba dai Ammi duka nawa take da zata fara koyan girki tun yanzu,
“Kai rufe mana baki duk kai ke k’arasawa Ummi bata son koyan abu,yanzu idan bata koya tun yanzu ba sai yaushe ko so kake nan gaba kazo kana mana kukan bata iya girki ba,
Abbu girgiza kai kawai yayi yana murmushi yace”rabu da d’an tselan d’an nan naki nan gaba idan yazo yace haka ni nasan amsar da zan basa,cikin shagwa6a yace”kai Abbu yau harda kai,yace”eh hardani,
Tashi yayi ya sungumi Zainab ya sa6a yace”mu,mun wuce saida safenku,yayi gaba,bayan fitarsa suka saka dariya,Ammi tace”yau naga yaro,Alh kaga yaran zamani ko?,murmushi yayi”wannan ai ba sabon abu bane a gurinmu tunda,tunda cen yasaba tunkan ya aureta bashiyasa muka musu auran ba kar azo a wuce gona da iri d’an yau baka shaidarsa,tace”haka ne kam Allah dai ya shirya mana zuria,ya amsa da amin,
Bai ajeta ako inaba sai kan bed,turo baki tayi wanda na lura kamar hakan ya zamemata jiki tace”kai Yaya Lameer yanzun saboda tsabar mugunta don kar inci abincin Ammi in k’oshi ka d’akkoni,yace”duk uban abincin da kikaci nagafa har k’ari kikayi idan kuma kinason k’atun ciki sai in mayar dake kiyi tumbi,6ata rai tayi don bata son tumbi tace”a’a wllh na k’oshi,dariya yasa mata yace”da sai na dunga miki wak’ar me k’aton ciki,
Acikin haushi takai masa duka,nan fa yaruga sai suka dunga zagaye d’akin yana mata dariya,ta fa shak’a sosai sai ta duk’e tana kukan shagwa6a,”ni wllh bazan yarda ba,
Zuwa yayi ya duk’a,da sauri ta d’ane bayansa ta mak’alk’alesa tana dry,yace”yanzun kin rama ko,tace”a’a sai kayi juya-juya dani,nan fa ya fara juya juyar da ita saida tace ta gaji sannan tace”wanka zanyi Yaya Lameer,
“To muje namiki,tace”wllh bana so,chaf wllh bazan yarda ba kama fita idan nayi sai ka dawo,yace”shikenan nima bari naje nayi nawa,
Haka ya fita,tashiga bathroom tayi wankanta,sannan tazo ta jura doguwar rigar barci,wacce bata wuce gwiwarta ba,
Zata kwanta kenan ya shugo shima cikin shigar doguwar rigar barci ta maza,hannunsa faranti ne da ya yanko musu kankana daman kullum kafin su kwanta sai sunsha,
Haka tana zaune jikinsa sunasha suna hira,har barci ya kwasheta,tashi yayi,ya bayar da farantin kitchin ya kashe wutar farlour da kayan kallo,ya dawo,nan yaza mudu bargo,Asuba ta gari
Insha Allahu zaku jini anji,Ina sonku masoyana a duk inda kuke,sai mun had’e anjima????????
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️7↪️8
Wajen bakwai na safe tuni suka gama shirinsu,Wow zo kuga Yaya Lameer ya had’u sosai cikin shigarsu ta likitoci,
K’ananun kaya ne jikinsa ya d’aura rigar likitoci a sama,Zainab ko sanye take da kayan boko,wando Ash colour farar riga da tazo mata har gwiwa sai hura ash da tasaka hijabinta wanda iyakarsa k’irji,jan hannunta yayi zuwa farlour,turjewa tayi,tana turo baki gama,
Murmushi yayi yace”menene kuma?,hawaye ta fara tace”Yaya Lameer nifa baganewa nake ba mkrntar nan kawai karabu dani banson zuwa,
6ata rai yayi yace”Wai Zainab meke damunki ne sam bakisan karatu duk k’ok’arin da nake akanki gami da karatu kyanyarnan taki haka take kamar dussa,
Hawaye ta fara,ta koma kan kujera ta zauna tc”tunda haka kace ba inda zani,nan fa tafara kuka wiwi,numfashi yaja,yadawo kusa da ita yazauna tare da jawo hannayenta ya murja,d’agowa tayi ta kallesa,shima ita yake kallo,
Yace”Zainab bazaki fahimta bane kingani nan mutum ne meson ilmi amma ke nalura ba abinda kika tsana irin karatu tanan fannin bazamu shirya ba,Kaka ce tun farko taja miki da idan kince bazaki ba tace”abarki ni bazan laminci hakanba gara tun wuri ki bayar da hnkl akan karatunki JSStwo kike amma ace bakisan komai ba,
Zuba masa ido tayi ganin yadda yake ta masifa aranta tace”daman ka iya masifa haka,a fili kuwa kwa6e fuska tayi tana niyyar sakin kuka,
Jawota jikinsa yayi yana shafa bayanta,d’ago fuskarta yayi suna kallon juna yace”Zainab ina so kiyi karatu mai zurfi hakan bazai samu ba harsai kin tsayar da hankali gurin fahimtar me ake koya miki,