Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

A year and a half later….

Tun da khadijah ta tashi yau take ta girke girke iri iri duk da xaxxabin da ta dinga yi kwana biyu da suka wuce, kana ganinta ka ga mai karamin ciki, yanxun ma daurewa take girkin da take yi, don aroma din na hawa mata kai but she have no option, Aliyu ne ya shigo kitchen din yana rungume da little Fatima, yarinya da baxata wuce shekara daya da few months ba, she is just a duplicate of her mother, babu inda ta bar khadijah, kyakkyawa ce ta karshe yarinyar, Khadijah ta kallesu tace “Dear kasan yanxu xata ce sai na dauketa kuma ni ba taya ni aiki xaka yi ba” Yar dariya yayi yace “Tsoro nake kar in fita da ita tayi ta min ihu a mota, xan je airport dauko Umma, same flight kuma suka bi da su Baby” Khadijah tace “Lahh da gaske?” Yace “Sure, Aryan ma ba yarda xai yi ya bi ni ba da sai mu tafi tare da su…” Tace “Ae tun daxu na gane gida yake son wucewa ya gaji da mu” dariya Aliyu yyi yace “Aa miskilanci ne kawai, ya ki yarda in dauke sa ma” Ta dauraye hannunta ta amshi Noor ta mana masa kiss a lips dinsa tace “Toh Allah ya tsare babyna….” Yace “Uhn you are looking for trouble koh” yar dariya tayi ta kashe masa ido tace “Don ma ban maka french one ba” Ya wara ido yace “Toh mu je daki ki min” ta hararesa tace “Naki wayon” juyawa yayi ya fita yana murmushi, yau ranan farin ciki ne gareta don a ranan xata sama qualified pharmacist, a ranan xa ayi convocating din su, kafin Aliyu su shigo gidan ta gama komai tana jiran Ummarta da yanxu take auren yayan mahaifiyarta wato dad din su Maimoon, tare da Baby uwar gida ga Barrister Sudais, fitowa parlor tayi jin shirun Aryan yayi yawa, xaune ta ga little balaraben kan kujera kiris yake jira ya fara kuka, ta karasa gun sa tana murmushi ta ajiye Noor, ta daukesa ta rungumesa tace “Haba sweetheart, in dafa maka indomie xaka ci?” Kitchen ta koma tana rike da shi ta daura ruwan indomie sanin abinda yake ci kenan, tana tsaye har ya dahu ta juye a plate ta dawo parlor ta xaunar da shi ita ma ta xauna ta shiga basa, Babu inda ya bar ubansa tun daga kyau har gashin kansa, hatta idonsa irin na babansa ne, murmushi tayi tana ci gaba da ba sa indomien yana ci, tana gama basa ta wuce daki da shi ta sauya masa kayan jikinsa duk da ba su yi komai ba ta dauko masa favourite toy dinsa ta basa ya amsa ta kunna masa cartoon ta xaunar da shi kusa da Noor da ta kwanta kan kujera, sannan ta shiga daki don yin wanka, tana shiryawa bayan ta fito ta ji shigowar mota, ta gama saka kayan da sauri ta fito, Aryan na ganin xata fita ya sauka saman kujera xai fara kuka, ganin haka ta dawo ta daukesa, Noor ta fashe da kuka ita ma, dariya tayi ta dauketa ita ma, tana rike da su ta fita compound, tsaye tayi tana murmushi ganin motar Khaleel ne, jawahir ta fito daga motar, Aryan na ganinta ya fara murna, khadijah ta saukesa yaje da gudu ya rungume uwarsa ta daga sa tana dariya tace “Kai lallai khadijah, dubi yanda kika maida min yaro kato, wani irin abinci kike basa haka” dariya khadijah tayi tace “Bayan ma ya rame, duk kwanan nan a dole yake xaune gidan, naga alamar kewar ki yake” Khaleel ya fito daga mota yana murmushi ya nufo ta yace “Oum shureim good morning” tana murmushi ita ma tace “Morning doctor….” ya amshi Noor yana shafa dogon gashinta idonsa a kan khadijah yace “Congrat once more, Allah ya sanya alkhairi, our pharmacist…” Tace “Ameen Thumma Ameen, thanks much Abu Aryan” Bata rufe baki ba motar Aliyu ya shigo gidan, Baby ce ta fara fitowa daga motar tare da little Amira, khadijah ta wara ido tana kallonsu ta nufe su da sauri, Barrister Sudais ya fito daga gaban motar with Shureim, sannan Umma da ta fito ita ma rike da little Farouq yaron da baxai wuce wata bakwai ba da baby take goyo, khadijah ta rungume baby cike da murnan ganinta suka dinga babbaka dariya, lkci daya ta tafi gun Ummarta ta rungume ta ita ma, tsabar murna ta kasa cewa komai, ta rasa me xata ce, tana sake Umma ta daga handsome yaronta sama ta rungume sa ya dinga kissing fuskarta very happy seeing her….. Aliyu ya fito ya jingina da mota ya rungume hannunsa yana kallonsu, Kamar yanda Barrister Aliyu da Dr Ayman ke kallonsu suna murmushi su ma….

ALHAMDULILLAH

A nan na sauke littafina mai taken Noor-Al-Hayat kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min….???????? Darussukan dake ciki Allah yasa mu amfana da su Amin. Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah… She is my first love, my role model, my momma, my world, my everything… Allah bar min ke Hajjaju Yaya❤ My sweet Anty Didi ur daughter Jiddo is greeting with respect, tnx for being there for me during this book, Allah ya raya su Aneesah… And my second role model Anty Rukaiyya…???? am so grateful for the encouragement from the beginning of this novel till the end, I always gat ur back small mum ur daughter Khaleesat Haiydar is saying a big thank you, Allah bar mu tare ya raya Little Khaleesat Haiydar, Baby and Jaheed…
Na sadaukar da littafin Noor-Al-Hayat xuwa ga lovely sister na, my Blood… Khadijah M Bello (Amira/Baby) nd my sweet cousin like no other Khadijah Sadi Yusuf (Baby) Allah ya albarkace rayuwar ku ya raya mani ku bisa imani, ya baku ilimi mai albarka da amfani. Sakon gaisuwa ta na musamman xuwa ga wa enda for sure ba siyan littafin Noorul Hayat suka yi ba, ihisani kawai suka min, duk ina sane da ku kuma na so contacting din ku but I lost my contacts, ban san ya xan yi in same ku ba, Amma ku sani I will for ever be grateful, Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi duniya da lahira, nagode nagode…. And finally my fans, ban taba xaton yea da gaske I have fans ba sai a littafin nan, you guys really patronized me fiye da tunani na, you all made me feel loved???? words alone can’t express how happy I am, ku sani… Billah Khaleesat na ji da ku har ranta, Ina son ku, Ina alfahari da ku, Ina maku fatan alkahiri, Ina maku fatan rabuwa da iyayen ku lafiya, Ina maku fatan daukaka, Ina maku fatan gamawa da duniya lafiya, ina maku fatan samun aljanna, I wish you all the very very very best in life, nagode nagode nagode… Allah ya sa mu cika da imani ya yafe mana kura kuran mu…????????

Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) ????✍????

Thanks once more for patronizing my book fans… For those still wanting to buy the complete document it’s just 300 Via transfer ???????? 3276052019 Hauwa Jiddah Bello, fcmb.

07087865788.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103

Leave a Reply

Back to top button