Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????

Noor-Al-Hayat

By khaleesat Haiydar????✍????

7…..

Matar farouq ta sakko suka gaisa da Aliyu tayi serving dinsu abinci ta koma daki, farouq na lura da abokin nasa dake cin abincin a hankali, yayi breaking silence din after a while yace “Toh tun yaushe kasan Iman din nan ni dai ka ban labari frnd” Aliyu ya dago yana kallon sa, murmushi yyi ya ajiye spoon din hannunsa yace “Tun tana shekara sha hudu…” Farouq ya wara ido yace “Kace yanxu ta girma kam” Aliyu ya d’an bude ido yace “Uhn” Farouq yace “Kuma yaushe rabon da ka ganta a mafarkin naka” wani kallo Aliyu ya watsa masa yace “Ce maka nayi a mafarki na santa?” Farouq yace “Au, nayi xaton a mafarki ne ai” tsaki Aliyu yyi ya mike yace “Da gaske ka ma mayar da ni mahaukaci wllh” farouq yyi dariya sosai, Aliyu ya dau makullinsa yace “Am full frnd, gobe xan tafi UK in sha Allah” Farouq yace “UK? Ba last month ka dawo ba?” Aliyu yace “Yeah ina da aiki can, beside na fi jin ddin can wllh, ba takura…” Kofa ya nufa farouq ya mike ya bi bayansa, har gun mota ya rakasa Aliyu ya shiga ya tada motar yace “Toh sai na dawo frnd, a kulan min da boys dina” Farouq yace “Toh Allah ya tsare, ya sa ka taho mana da tsarabar mata ko da baturiya ce wllh don na gaji da ganin ka ba aure” d’an murmushi Aliyu yyi yace “Toh Abba….” farouq yace “Allah kuwa, Abban ma da ya gaji ya xuba maka ido ynxu, ni wllh da ma kawai su yi taking dinka unaware kana dawowa sai dai kaji ai an sa ranan ku da Hanan, ga mace har mace tana son ka amma kayi ta mata jan aji kana jiran Iman Aljanar ka, ni wllh ko Salmah ce a hadaku, ka kuma san gwara Hanan sau dubu kan salmah…” Aliyu bai ce komai ba don har ya 6ata masa rai, ya ja motarsa kawai ya bar gun Farouq na dariya.

Tunda Khadijah ta shiga daki ta sa key bata sake lekowa parlor ba kusan awa daya da rabi kenan, ita dai ta ga abinda ya isheta…. Khaleel taji kanwarsa ta kirasa da ko wa?? Kwafa tayi ta juya xuwa daya side din gadon da take kwance, kallon agogo tayi a hankali ta jawo wayarta dake gefenta ta gama dialing number ta kai kunne, Muryar Nanny taji, bayan sun gaisa tace “Umma fa?” Nanny tace “Umma na tare da bakuwa….” Tace “Toh xan kira xuwa anjima….” Nannyn tace “Ga su Sudais….” Khadijah ta d’an buda ido tace “Boy… how you?” Shiru tayi tana apprehending abinda twins din ke gaya mata a waya duk jikinta yyi sanyi sosai, Shuraim yace “Hello… Are you there Anty?” Ta lumshe ido ta bude cikin sanyin murya nace “Yea soldiers, hope ba ku ji ciwo ba” Shuraim yace “Not at all aunt, we where just freaked out, and an Uncle consoled us right there and made sure we where fyn, he was kind aunt….” Tace “That nyc of him, But did you both prayed?” Duk suka ce “We did…” Tace “Good, you make prayer ur daily routine before leaving home and when coming back, clear?” Suka ce “In sha Allah aunt” tace “Hand the phone over to Nanny…” ba musu suka kai ma Nannynsu wayar, ba su dau lkci suna magana ba tayi mata sallama ta ajiye wayar duk da ta so magana da Umma, har lkcn hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa xaune tayi a hankali, she can’t imagine loosing the boys, she just can’t….. Tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ta rike kai tana jin dama ta gansu kusa da ita a yanxu, ita kanta bata san wani irin soyayyan yaran bane ya dirar mata all of a sudden tun daga shekaru biyun da suka wuce, unlike before, kamar yanda bata son mutuwarta until her God is please with her haka bata son su, bata son su kusa da ita but now…. Reverse is d case, Allah yasan yanxu bata da kamarsu a duniyar nan gaba daya, she just love them, she know she love dem dearly… Ji tayi kamar xata yi xaxxabi ta koma ta kwanta, nan bacci ya dauketa, ba ita ta farka ba sai kusan magrib, bayan ta idar da sllh ta bude kofar dakin a hankali tana lekan parlor, bbu kowa parlorn kamar yanda ta yi tunani, ta karasa ciki a sanyaye a ranta tace ae da ka xauna ka jira ni, ta isa gun main door ta sa makulli tana kallon tray din abincin da ta kai ma fatima daxu, toh ko shi ya kawo ya ajiye daxun, ta bude plate din dake a rufe taga da sauran Irish din, da alamar fatima bata ci da yawa ba, ta dau tray din ta wuce kitchen, disposing din abincin tayi, duk da muryarsa da ta ji a baya bata leka ba har ta gama abinda xata yi ta bar kitchen din, Mis cals din Vanessa ta samu a wayarta, ta mayar da kiran bayan sun gaisa Vanessa tace yau ma tana ta jiranta, murmushi tayi tace “Sorry love, I had a visitor today, an unexpected one…” Vanessa tace “Alryt then, good nyt” daga haka Khadijah ta katse wayar ta ajiye, Daren ranan bata samu bacci me tsawo ba, don da tayi xata farka, karfe uku tana ta xaune har lkcn ta kasa baccin bayan ta idar da sallah, tashi tayi ta wuce kitchen don diban ruwan Lipton ta sha ko xata iya karatu, kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da shi xaune da uban textbooks a gaban sa yana sanye da siririn farin glass, ta cikin glass din yake kallonta, a hankali ta sauke idonta ta gama abinda xata yi ta kashe wutan kitchen din ta wuce. Har gari ya waye idonta biyu kamar warce ta sha wani abu, Shayi kadai ta iya sha da safe bayan ta shirya ta bar gidan misalin karfe bakwai da rabi don wucewa makaranta, throughout ranan bata da walwala a makarantar ma, bayan la’asar tare da Vanessa suka taho gidanta kamar yanda ta bukaci su je, suna gama cin abinci khadijah ta tafi tayi wanka ta bar Vanessa parlor tana kallo, bayan ta gama shiryawa ta dau waya ta shiga kiran Umma, a hankali ta gaisheta, bayan yan sakwanni tace “Umma yaushe su Sudais xa su yi Mid term break?” Umma tace “Mid term… gobe ne ai….” Ta d’an yi shiru sannan kamar me tsoron magana tace “Toh, dama Umma don Allah da sai su taho gu na da Nanny suyi hutun a nan plss” Umma tace “Saboda rashin hankali” shiru ta yi bata ce komai ba, Umma tace “Shi hutun kwana hudun ne xa su kwashi jiki su tafi UK” Khadijah ta girgixa kai tace “Toh shkkn Umma kiyi hakuri” Umma ta katse wayar ta, misalin karfe shidda suna xaune waje da Vanessa suna duba wani material na karatu khaleel ya bude kofa ya fito, 3 qtr da singlet ne jikinsa, tun da ta kallesa sau daya ta mayar da kanta kasa bata sake daga kai ba, taji Vanessa tace “Good evening” cikin cool voice dinsa yace “How you?” Tace “Am great” ya saci kallon khadijah sai kuma ya juya ya koma ciki, Vanessa tace “Ur neighbor?” Khadijah tace “Yeah” Vanessa ta wara cat like eyes dinta tace “He is damn cute, a Nigerian also?” Khadijah ta nuna mata kofar flat dinsa tace “You can ask him” Vanessa tayi dariya tace “Sure I can” suna nan xaune har kusan goman dare, Khadijah ta san ba don suna wajen ba da yanxu ya fito, sai taji dadin hakan ko ba komai dai sun hanasa xama wajen, a ranta tace ba don ba don ba ma a nan xata kwana a xaune, sha daya saura suka tattara takardunsu suka wuce ciki, ae kam ko minti takwas ba su yi da shiga gida ba taji fitarsa, Missed calls din Umma ta gani har biyu a phone nata dake daki, ta shiga kiranta bayan tayi shirin kwanciya, Umma tace “Kin yi bacci ne” ta girgixa kai tace “Yanxu xan yi Umma” Umma tace “Tunda ganin yaran kike son yi gobe xa su bi train xuwa Abj su yi boarding plane….” Khadijah ta d’an xaro ido tace “A’a Umma hutun ba yawa ai” Umma tace “Ai kinsan da ba shi da yawa kika ce su taho, so keep shut” shiru ta yi bata iya tace komai ba har Umma ta katse wayar, har ranta taji dadin abinda Umma tace, tayi murmushi ta kwanta hade da lumshe ido.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103Next page

Leave a Reply

Back to top button