Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Breakfast, just light????

Sai kusan karfe uku saura Baby ta tada Khadijah tayi sllhn azahar ganin lkcnsa na ta wucewa kuma da alamar ta samu saukin jikinta sosai ganin she is sleeping peacefully…. Khadijah ta mike xaune da kyar, xuwa lkcn kam ciwon da ta dinga ji daxu da safe a xuciyarta ya rage sosai, sai dai gaba daya taji gaba daya she is weak kanta ya mata nauyi, Tana kallon Baby cikin sanyi tace “An daura auren koh Baby?” Tana magana ne hawaye cike idonta, Baby ta kasa ce mata komai… Ta hade kanta da gado cikin rauni tace “Matar nan xata iya kashe ni wllh, nobody want to consider me, nobody is willing to understand what I mean, Baby tsoron ta nake.. ” Baby ta kauda kanta bata ce komai ba sai dai wani mugun tausayinta ta dinga ji har ranta, Bayan wani lkci a sanyaye baby tace “Ki tashi kiyi sllh Khadijah, lkci na wucewa” Khadijah Bata ce komai ba ta sauka saman gadon tana kokarin ganin bata bar hawaye ya sakko mata ba, kamar iska xai kadeta ta shiga bathroom, khadijah na idar da sllh Baby ta fiddo mata daya daga kayan biki da aka dinka mata, tana kallonta persuasively tace “Plss Iman put on this ko baxa kiyi kwalliya ba, am begging you” Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Bayan wani lkci ta mike ta shirya cikin tsadadden lace din, Baby na murmushi ta wara ido tace “Waow kin ga yanda kayan suka maki kyau kuwa Iman, plss ki bari ko powder in shafa maki, just it” khadijah bata mata musu ba, duk da har xuciyarta bata so, daga powder baby ta lallabata ta sa mata har eye pencil da chappete, sosai Khadijah tayi kyau just like the bride she is, Baby ta daura mata dankwali tana kallonta da sha’awa, Frnd din Umma ce ta shigo dakin da warmer din abinci ganinta tace “Kai maa sha Allah ko ku fa? Da xa ku bari wata kishiya can ta bata maku wannan ranan, show her she is a liar bata isa ba ne, sai ma mun je kai ta gidan tukun” Murmushi kawai Baby tayi tana kallon khadijah da ta ki dago kanta. Tun bayan da suka bar masallaci bayan an daura auren Aliyu ke rike da kan sa a mota, su biyar ne motar, Khaleel na driving, Dr Yusuf na xaune gaban motar, sai Barrister da Aliyu da Farouq a baya, tun da suka dau hanya Sudais ke danna wayarsa bai dago ba shi ma, the journey was very silent da alama kowa da abinda ke ransa har suka iso dai dai kofar gidan su Khadijah, Khaleel yyi parking a hankali ya kashe motar, Shi ya fara sauka sannan Farouq da Dr Yusuf, Aliyu ya sauka sannan Sudais ma ya fito yana mayar da wayar sa Aljihunsa, ganin xai shiga ciki Aliyu ya riko hannunsa yana kallonsa da idanuwansa da suka kada sosai, Barrister ya kasa hada ido da shi, Da mugun karfin hali yace “Barrister… am still confuse, I think am yet to understand the meaning of the drama that took place at the mosque minutes back, ka ganar da ni don Allah, I am confuse plss, nayi tambaya a mota kun kyaleni…” Sudais dai bai iya yace komai ba, Dr Yusuf ya rungume hannayensa yana kallon Sudais don Aliyu bai ma kai sa confusion ba, jiran abinda Sudais din xai ce shi ma yake, shi dai yasan daurin auren abokin nasa ya xo tun daga Yobe sai kuma ya ga otherwise, Farouq dai murmushi kawai yyi ya jingina da mota ya rungume hannunsa, khaleel ya tako har gaban Aliyu yana kallonsa, bayan few seconds yace “What is it that u don’t understand Aliyu?” Aliyu ya kallesa a hankali yace “Everything…. I… I don’t get everything” Khaleel ya shafa kansa cikin sanyin murya yace “The fact is that, Kai xaka gyara abinda ka 6ata doctor, we think this is just the best for the both of you, Barrister Aliyu ya sadaukar maka ba don baya so ba sai don la’akari da our today’s world, kwanciyar hankalin khadijah ya fi masa auren ta…..” Sai a sannan Sudais yyi murmushin karfin hali yana kallon Aliyu a sanyaye yace “I have no option… She is dear to me… Ita din abar tausayi ce, they are a lot of challenges ahead for her and the little boy in dai ba gidan ka suke ba, I don’t wish that for her, and her condition don’t need that, shi yasa na hakura domin farin ciki da kwanciyar hankalinta, nasan I am not making a mistake giving up for you because I know you love her also, and u love ur son…da dadewa na yarda da cewa abinda ya faru tsakanin ku tsautsayi ne, it’s not ur doing coz you are too responsible for that, u are responsible in every aspect, you are really a gentleman, ur family are just good also, kawaicin ka ma abun dubawa ne, I’ve studied you for long….” Aliyu ya runtse ido maganganun Sudais na yawo kansa kamar a mafarki, lkci daya ya bude idanuwansa, kawai ya rungume sa hawaye na xuba idonsa ya kasa cewa komai, Sudais da ya ji xuciyar sa ya masa rauni yyi karfin hali yace “It’s my pleasure, and a Suggestion from Dr Ayman…. nayi ma Khadijah wanda ya fi wannan ma, don haka nasan ban fadi ba, But ina neman alfarmar ka bar mu mu din ga xumunci sosai coz I love the little boy…” Cike da karfin hali hawaye na sauka idon Aliyu yace “How will I repay you Barrister…” Sudais yayi murmushi shi ma hawayen suka xubo masa a hankali yace “Ta hanyar rike Amira da amana, be her father be her mother, be her happiness, and finally prove to her that u are innocent, kadarrar ku ce a haka” Khaleel ya sauke idanuwansa a hankali ya juya ya shiga gida ganin he might not stand it anymore…. ????

Lunch, very light also, kar mutum yaje yana bacci da rana????

Umma kasa kwakkwaran motsi tayi bayan ta gama jin bayanin Sudais ta kasa daina kallonsa, jikinta yayi sanyi sosai, tsoronta daya a lkcn khadijah, ko ya xata dau batun nan, Wai Aliyu? Kallon Khaleel dake xaune shi ma tayi, ya d’an yi murmushi ganin damuwar dake fuskarta yace “Umma you need not to worry, I know you might be thinking of how khadijah will take this, but I think ba lallai sai an fadi mata ba she will see for her eyes, and surely nasan she have a very soft spot for Aliyu, the problem is that she is confuse, sannan one thing about her is that bata mance abun sharri da aka mata ko ya yake which is wrong, she need counseling Umma….” Murmushi Sudais yyi a hankali yace “Sure, gaskiya doctor ya fada Umma, fatan Allah yasa ke dai kin fahimce ni, nayi abinda naye ne saboda future, I really don’t want anything that will hurt her again in life, she have had enough… duk Allah ne mai tsara komai” a sanyaye Umma tace “I am really proud of u both, irin ku basu da yawa a duniya Allah ya biya ku da mafificin alkhairinsa, ko wannen ku ya taka rawar gani matuka a rayuwar khadijah, Kun mata abinda dangin ubanta da ni kaina na kasa yi mata, Allah ya saka da alkhairi, and one more thing Sudais ka maida matar ka don Allah…” Sudais ya girgixa kai a hankali yace “Umma I don’t think xan maida jiddah, na hakura da ita, Allah ya musanya min ita da mafi alkhairi, may be abubuwan da nayi mata years back kan khadijah ne Allah ya saka mata ta samu damar yi min abinda ta so, tun da na aure ta take wahal da ni, I have had enough…” Umma tace “A’a ba ayi haka ba, kayi hakuri don Allah, ko albarkacin yarinyar nan dake tsakanin ku” Dai dai nan Baby ta fito ta kawo masu abinci kamar yanda Umma ta umarce ta kafin ta taho gun su, ajiye abincin tayi ta kasa kallon Sudais don ba karamin kunyar abinda tayi masa a waya taji ba daxu barin da ta ga bashi da laifi, Kallon Khaleel tayi daga karshe tace “Ina yini” yace “How are you” ta mike tace “Alhmdllh” daga haka ta juya ta wuce Sudais ya bi ta da kallo ganin bata gaishesa ba, Khaleel na kallon Umma yace “And lastly Umma, I think I’ve found out dangin mahaifiyar khadijah if I am not mistaken in sha Allah” daga Umma har Sudais kallonsa suka dinga yi ko kiftawa babu, ya sauke kansa kasa a hankali yace “But I won’t reveal that to her sai tayi settling gidan mijinta, ta kwantar da hankalinta, still xa mu je can gidan dake Umma duk da su ma ban ce masu komai ba tukun, but babu tantama they are her mother’s family in sha Allah” Mumy ba karamin sanyi jikinta yayi ba jin sadaukarwar da Barrister yayi ma Aliyu, she couldn’t even utter a word, abun ya mugun daure mata kai, Abbansa shi ma ya jinjina lamarin sai dai abinda bai ji dadi ba shine yin gaban kansu da suka yi babu shawara da kowa, and a whole daurin auren 1st son dinsa baya gun, but all the same he is happy for his son cos he is always after his happiness kuma ya bukaci number Barrister Sudais, Mumy na ta kallon Aliyu da har sannan mood dinsa isn’t encouraging da damuwa tace “What’s it again Abuturrab, ain’t you happy” ya dago ya kalleta da kyar yace “Mumy bata sani ba fa, and I don’t know how she will take this, ba so na take yi ba, tana kulani ne kawai saboda kids din, albarkacin su nake ci” A hankali Mumy tace “Then you will teach her to love you son…” Bai iya yace komai ba, bayan few seconds ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana facing dinta, har lkcn idanuwansa basu dawo dai dai ba, cikin sanyin yace “Mumy me xan yi in biya su?” Shiru Mumy tayi tana kallonsa don tasan su wa yake nufi, ta d’an yi murmushi tace “Zumunci mai karfi da su is enough son” Aliyu ya sauke idonsa kasa a hankali yana tunanin xumunci yayi kadan ya biya both Dr Ayman and Barrister Aliyu, dafa sa Mumy tayi tace “That’s just it Abuturrab, mutanen nan biyu ka rike su a rayuwa, kaga riban hakuri… Da ka ci gaba a yanda ka fara da farko kana tunanin Barrister xai ga cancantar bar maka ita? Of course no, shi sa nake yawan ce maka you just have to be patient in everything in life” Bai dai ce komai ba, tace “Do what you are suppose to now, na kira su Siyama xa su je can gidan naka su yi abinda ya kamata, don xuwa anjima xa su kai ta can gidan, mun yi waya da Ummarta yanxu” Har sannan Kamar yanda khadijah bata san da wanda aka daura mata aure ba haka baby ma bata sani ba, gashi dai ana ta shirin tafiya da amarya wajajen karfe biyar, Umma duk ta kasa samun nutsuwa da ta tuna khadijah fa bata san da Aliyu aka daura auren ba sai taji gabanta ya fadi, tsoronta ma kada ciwonta ya kara tashi, daga karshe ta sa aka kira mata Baby bedroom dinta, Baby na kallonta tace “Gani Umma” cikin sanyi Umma tace “Khadijah kin san da wanda aka daura auren nan kuwa?” Girgixa kai Baby tayi da confusion tana kallonta, a sanyaye Umma tace “Yayan ki” still khadijah tayi tana kallon Umma baki bude ta kuma kasa cewa komai, a hankali Umma tace “Ban san yanda khadijah xata dau batun nan ba, am afraid….” A hankali baby ta dauke kanta tana sake nanata sunan yayanta a xuciyarta, to how comes??? Da kyar ta kalli Umma tace “Barristern fah?” Umma tace “Shi ya bar masa… For some concrete reasons which I found out to be nothing but the truth, Aliyu shi ne kadai rufin asirin khadijah da yaron nan, toh amma ba lallai ta gane hakan ba, ban san ta ina xan fara sanar mata ba” Baby ta sauke ajiyar xuciya, lkci daya jikinta yyi sanyi tace “Umma kar a gaya mata, she shud just see for her self, xasu sasanta kansu can din” Umma tace “I thought as much… Haka yawanci kowa ke ce min” Tagumi baby tayi ta rasa wanne xata yi a ciki, farin ciki ko bakin ciki, Umma tace “Tashi ki je ku gama shiryawa lkci na wucewa khadijah, har an gama kai kaya can gidan” Baby ta mike jiki ba kwari ta fita, tana komawa daki ta ci gaba da shirya ma khadijah few abubuwan da tace mata, Shureim ne ya shigo dakin da shadda irin wanda Sudais yasa ranan da hularsa, sai sheki kayan suke sun masa kyau sosai, tun wayewar gari sai sannan khadijah ta gansa, ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa a hankali tace “Where have you being today?” ya wara mata ido yace “Uncle ne ya tafi dani since, mun dawo yanxu, Anty daxu Umma tace min baki da lafiya, me ya same ki” Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin yanda yake kallonta ta rungumosa a hankali tace “Ae na samu lafiya yanxu” yace “Anty kinyi kyau sosai” Murmushi tayi ta ja hancin sa tace “Kai ma kayi kyau sosai, wa ya kawo maka kayan nan” Yace “Uncle, shi ma ya sa irin nawa, na tambayesa Ina na Sudais yace ya ajiye masa nasa” Shiru khadijah tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace “Anty what are they celebrating today?” Baby dake gefe sai kallonsu take ta dauke kanta a hankali, sai a sannan tayi mugun ganin dacewar abinda Barrister Sudais yyi, shkkn sai su hadu su rungumi d’an su, khadijah ta sunkuyar da kanta tuna irin xagin da Jiddah tayi ma yaron daxu ta kirasa da shege mara uba, hawaye ne ya kawo idonta sai dai bata bari ya gani ba, Jikin baby yayi sanyi don duk tana lura da ita, ta juya ta ci gaba da abinda take, Shureim ya taho gunta yana gaisheta, ta rungume sa murmushi dauke fuskarta tace “Har kun dawo boy” ya gyada mata kai, shidda saura motocin tafiya da amarya suka iso gidan, nasiha sosai Mum din sadeeq da wata frnd din Umma suka yi mata, Kanta a kasa take saurarensu hawaye na sakko mata, ita kam bata samu gatar nasihar Uba ba, kalma daya Umma ta iya yi mata a lokacin bayan su Umman sadeeq sun gama “Allah maki albarka” hakan yasa khadijah taji dadi sosai, Shaheedah ta daga ta suka nufi kofa baby da wata kawarta na biye da su a baya, banda kuka babu abinda khadijah take duk jikinta yayi sanyi, duk aka bi ta da kallo cike da tausayinta, Baby da frnd dinta Hafsat sai mahaifiyar Shaheedah wato aminiyar Umma suka shiga mota daya da khadijah, sauran yan rakiyar Amarya suka shiga sauran motocin, Jikin baby bai gama sanyi ba sai da taga sun iso gidan yayanta, duk tausayin khadijah ya cikata a xuciyarta ta dinga addu’ar Allah yasa shock din ganin Aliyu as mijinta baxai yi affecting dinta sosai ba, dad’d’adan kamshin turaren wuta ke tashi ta ko wani angle a gidan, ga sanyin ac, parlorn so chill, har lkcn kuma su Siyama da kawayensu da frnd din Mumy suna gidan suna jiran Amarya, Su Hajiya Sajeedah suka wuce da khadijah well furnished bedroom dinta, ita dai har sannan fuskarta a rufe yake bata san kalan gidan ba gashi tun shigowar su gabanta ke faduwa ga hawaye ya ki tsaya mata duk jikinta yayi sanyi, ana xaunar da ita gefen gado ta riko baby cikin rawar murya tace “Stay beside me plss don’t leave me” a sanyaye baby ta xauna kusa da ita tana rike da hannunta, khadijah ta rike ta gam ta kwanta jikinta. Sai kusan bayan isha duk aka watse gidan har su Siyama suka wuce, sai da su Hajiya Sajeedah suka kara mata nasiha kan xamantakewar aure kafin su wuce su ma, gidan ya rage daga ita sai baby da Hafsat, kuka kawai khadijah take don tana ganin ko wani lkci jiddah xata iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d’an murmushi tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru ya d’an yi kafin yace “Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu” Tace “Toh” kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace “Waye ya kira ki?” Baby ta sauke idonta tace “Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya” khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana” dariya ta ba baby amma bata yi ba tace “Gobe fa da safe xan xo Iman” cikin kuka sosai Khadijah tace “Don Allah ki rufa min asiri ki kwana” Baby tace “In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya…” Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace “Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya” Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace “Ina yini yayanmu” yace “Lafiya lau” Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace “Alryt, sai da safe Dr” Aliyu ya kallesa a hankali yace “Baxa ka shiga ba?” Ya bude motarsa yana d’an murmushi yace “Gobe xan xo in sha Allah” Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace “Ku shiga xai yi dropping din ku gida” Ta d’an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace “Did she know….” Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace “Don’t keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe” A hankali baby tace “Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa” Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace “Ki basa hakuri idan kin shiga motar” shiru tayi, ya gyada mata kai yace “Yea, do that” a hankali tace “Toh sai da safe yayanmu” daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace “Good evening” sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace “Ina yini” yace “Lafiya lau” a hankali tace “Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri” kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace “Wai dama ke kika kirani?” xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace “I bet da muna kusa har duka sai kin kai min” sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace “Barrister ka kunna plss…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103Next page

Leave a Reply

Back to top button