Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi ta dinga bin inda take kwance da kallo, Umma ce xaune dakin da Nanny da ta ci kuka har ta gode Allah, sai kyauta da tayi tagumi, Umma ta mike da sauri ganin khadijah ta bude ido ta karasa kusa da ita da damuwa tace “Sannu daughter, how are you feeling now?” Mikewa xaune Khadijah ke son yi amma kanta yyi mata nauyi ga kirjinta dake mata xugi, Umma ta riketa tace “Koma ki kwanta” Kyauta ta iso kusa da ita ita ma da damuwa tace “Sannu khadijah” Shiru khadijah tayi kamar me son tuno abu, Umma ta hade rai tace “Don’t stress ur self thinking of anything, just relax….” Hawaye ya kawo idonta ta kamo hannun kyauta cikin rawar murya tace “Anty mai girki ina sudais dina, ya mutu koh? Don Allah ku gaya min, kar ku” Umma ta dakatar da ita a mugun fusace tace “Ke kika kashe sa halan? Ji wani xance da kike ma mutane khadijah” Girgixa kai khadijah tayi da sauri hawaye na sakko mata, Kyauta tace “Toh yana nan lafiya khadijah, har ya tashi shi ma, suna can tare da d’an uwansa da wani likita” Khadijah na goge idonta tace “Toh xan iya ganinsa don Allah?” Harara Umma ta watsa mata tace “Da drip din xa ki je ki gansa, kuma ki rufe min maki haka, ance maki yana lafiya” Khadijah bata sake cewa komai ba sai dai ban da faduwa babu abinda gabanta yake, Umma ta mike ta shiga hada mata shayi, Nanny ta xauna kusa da ita cikin sanyin murya tace “Kiyi hakuri Khadijah, Sudais yana nan lafiya har ya tashi, suna tare da Shureim yanxu haka” Sai a sannan khadijah ta ji hankalinta ya kwanta sosai, Nanny ta mika mata wayarta tace “An kira ki har sau biyu, but I picked…” Khadijah ta karbi wayar tana kallon wanda ya kirata ta ga Khaleel ne, ta kalli nanny a hankali tace “Me ya ce?” Nanny tace “Na gaya masa abinda ya faru, yace xai xo clinic din” Khadijah bata ce komai ba ta ajiye wayar, ta ji tana ma son ganinsa, jin xai xo hankalinta ya kara kwanciya. All this while Aliyu na ward din da sudais yake tare da Shureim, kwata kwata bai son ya bar su ko na minti daya, da ya fita ba a jimawa xai dawo kuma har lkcn ya ki cire mask din bakinsa da hanci, damuwa ce sosai tare da shi, da ya kalli yaran ya tuna nasa ne sai yaji hawaye a idonsa, shi kuma irin tasa kaddarar kenan?? Har yan biyu ba ta hanyar aure ba, har ransa yake jin tausayin kyawawan yaran, he wished ba ta haka suka xo ba, Shureim bai ganesa ba sai dai ya lura da irin yanda sudais dake kwance ke kallonsa, A hankali ya isa kusa da yaron ya duka a sanyaye yace “You want something??” Sudais ya girgixa masa kai, Shureim ya kallesa da sauri na few seconds kafin yace “The voice…. sounds familiar” murmushin karfin hali Aliyu yyi ya sauke mask din fuskarsa a hankali yana kallon yaron, Shureim yyi shiru yana kallonsa can ya juya ya rungume hannunsa ya hade rai yace “You caused my brother’s accident” Jikin Aliyu yyi sanyi sosai, ya mayar da dubansa kan sudais ya ga ya ki kallonsa shi ma ya hade rai, bude kofa aka yi xai mayar da mask dinsa da sauri yaji muryar colleague dinsa, Dr Muktar ya karaso yana kallon yan biyun yace “Maa sha Allah, he is recovering fast” ya kamo hannun Sudais yace “How are you feeling now handsome?” A hankali Sudais yace “Alhmdllh” Dr mukhtar yyi murmushi yace “Good” kallon Aliyu yyi yace “Kasan kuna yanayi da boys din nan sosai, da ba don na san baka taba aure ba bbu abinda xai hanani cewa yaranka ne Dr” Aliyu ya kirkiri murmushin karfin hali yace “Gaskiya ne” Dr mukhtar yace “Naga kamar sun ma shiga ranka kai ma tunda gashi ka ki barin ward din tun daxu” Aliyu yace “Sure they are cute” Dr mukhtar yace “Just came to check on them dama” daga haka ya juya ya fita, Aliyu ya kamo hannun yaran murya can kasa yace “Am sorry for all that happened sweethearts forgive me plss” a hankali Shureim yace “Ohk…” Kallon sudais da yyi shiru yyi yace “And you sweetheart?” Sudais ya sauke kansa yace “Me too” jawo yaran jikinsa ya yi cikin sanyin murya yace “I love you boys” lkci daya idanuwansa suka kada, how he wish Khadijah xata yafe masa ba tare da ta sa masa heart attack ba, ta ajiye komai su xauna tare da yaransu, bai taba saba maganar mahaifiyarsa ba amma da kamar wuya wannan karan, it will be different…. he will marry Khadijah and have his boys in sha Allah, and he will neva be ashame showing them as his children, wani mugun son yaran ne ke fixgarsa yana rungume da su, bude kofar dakin aka yi Umma ta shigo tare da wani likita, khaleel na biye da su a baya, A hankli Aliyu ya daga mask dinsa sannan ya juya suka yi ido hudu da khaleel, Dr Abdul yace “Dr their grandma and a Dr also, my frnd Dr Ayman” Aliyu sai kallon khaleel yake kamar yanda shi ma khaleel ke kallonsa duk da fuskarsa a rufe yake, Umma ta kalli Dr Abdul sanin ance baxa a bar su su shiga gun yaran ba tace “Mun gode Dr” Dr Abdul yace “Ba komai Mama” Dr Abdul yace “Ayman bari in koma bakin aiki na” khaleel yace “Tnxx Abdul” daga haka Abdul ya fita, Shureim ya sauko saman gadon ya rungume khaleel, khaleel ya daga sa sama yace “How are you” kamar xai yi kuka yace “I am fine but my brother isn’t” Khaleel ya ajiye sa ya karasa yana kallon Sudais cike da tausayinsa, Shureim kuma ya nufi gun Umma dake kallon Sudais ita ma a sanyaye, plaster ne gaba daya kansa, khaleel ya kamo hannunsa yace “You will get well soon in sha Allah my boy” Sudais xai fara kuka ya rungume sa yace “Noo don’t cry be a strong boy” Sudais yace “Uncle ina Antyna” khaleel yace “Xata xo yanxu” sudais yace “Ka kai ni wajenta I want to see her” Khaleel yace “Noo she will be coming soon” Aliyu dai na tsaye yana ya na kallonsu, Can ya kalli Umma yace “Plss Maa it shouldn’t take long xa ku iya tafiya yanxu the boy need rest” Umma tace “To xa mu fita yanxu Dr” khaleel ya juya yana kallon Aliyu, mikewa yyi ya isa gabansa yana kallon cikin idonsa yace “Then discharge him now, xa mu je gida in ci gaba da treating dinsa or I take him to another hospital” Aliyu yyi murmushi daga cikin mask din fuskarsa yace “And who are you to say that? His father? Or?” Umma tace “Aa bai kai haka ba Dr xa mu fita yanxu ai” wani kallo khaleel ya dinga ma Aliyu, Umma tace “mu je khaleel tunda a bakin aikinsu suke” kallonta khaleel yyi, duk da bai yi niyyar fita ba amma ya ji kunyanta yace “Toh umma” daga haka ya nufi kofa Shureim ya bata fuska kamar xai yi kuka yace “Uncle are you leaving us?” Sudais ma ya dinga kallonsa Kamar xai yi kukan, Khaleel ya juyo yace “Noo sweetheart I am around” Daga haka ya fita, Umma ta bi bayansa tana kara ba Aliyu hakuri tana fita ta rufe kofar, wata cleaner ce ta shigo dakin da abinci da ruwa da Aliyu ya sa ta siyo, ya mika ma Shureim nasa ya karba, Ya shiga ba sudais nasa da kansa. Khadijah duk ta damu tana son ta ga yaranta ganin har da Shureim ma tun da ta bude ido bata gansa ba, amma tsoron Umma yasa ta kasa cewa komai don tana iya balbaleta yanxu tunda ta ce mata they are all fyn, Khaleel dake tsaye dakin yana kallonta ya lura da yanayinta, ita ma ta tsaya kallonsa amma ta kasa ce masa komai ya san she Wants to say something, ya kalli Umma dake magana da wasu neighbours dinsu biyu da suka xo duba sudais, Nanny kuma ta koma gida tayi girki, Kyauta ma ta koma tace xata dawo ko da daddare da mai gidan ta, Khaleel ya karaso kusa da ita a hankali ya d’an duka yace “What?” Murya can kasa kamar xata yi kuka tace “I want to see my kids plss” wani kallo ya mata, sai kuma ya d’an yi murmushi yace “To sannu mai kids” ta bata fuska tana kallonsa alamar please, yace “Ohk wait bari Umma ta raka bakin nan sai in kai ki” lkci daya hankalinta ya kwanta tace “Toh ngdd” Umma na fita don yin rakiya ya cire mata drip din hannunta da ya kusa karewa, duk da jirin da take ji ta mika masa hannunta ya rike ta sauko daga kan gadon ta sa takalminta sannan suka fita ward din da sauri tana jin kamar xata fadi ba don ya rike hannunta ba, direct ward din da yan biyun suke ya nufa da ita, a hankali ya murda kofar ya bude, khadijah tayi ido hudu da Aliyu dake ba sudais abinci, still tayi a gun taji komai nata ya tsaya, xuciyarta ya dinga bugawa da sauri da sauri, Shureim ya sakko ya taho da gudu ya rungume ta, sudais yyi murmushi cike da jin dadi ganin uwar tasa yace “Anty….” Mikewa Aliyu yyi ya rufe abincin yana kallonta da khaleel yace “You can come over… But just few minutes” Khadijah ta warce hannunta a na Khaleel ta janye Shureim a jikinta ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama, direct reception ta nufa, tana kallon nurses din cike da masifa tace “Who is the Dr in charge of this hospital…” Kallonta nurses din suka tsaya yi, can wata ta mike tace “Me ya faru madam” tana huci tace “ohk, I want my kid discharge immediately, ku bani bill din in biya in bar nan yanxun nan plss” cikin tsawa ta kare maganar nurse din ta koma ta xauna tace “Easy madam, this a hospital, they are patients all over, ki je gun likitan da ya karbe su, shi xai yi discharging dinsu ba mu ba madam” khadijah na mata wani kallo tace “Wani likita kenan ina office dinsa kuma?” Nurse din tace “Dr Aliyu, kina haurawa sama office dinsa is by ur right, xa ma ki ga sunansa a jiki” kallonsu Khadijah ke yi xuciyarta na bugawa jin sunan da suka kira, can ta juya kamar xata tashi sama ta wuce upstairs din, Har lkcn khaleel dai na tsaye bakin kofa yana kallon Aliyu, Aliyu ya isa dab da shi yana masa wani kallo yace “Da matsala ne malam, naga kallon yyi yawa?” Wani murmushi khaleel yyi yace “You watch and see” Dawowa khadijah tayi dakin cikin tashin hankali ta nufi gun yaranta ta cire dip din hannun Sudais ta sauko da shi kan gado ta kama hannun Shureim ta nufi kofa, tsayawa gabanta Aliyu yyi yana kallonta da kyau yace “Ba inda xa ki je da su Iman” xaro ido tayi jin abinda ya fada ta tura sa da karfi amma go gezau, xuciyarta na heaving da mugun mamaki tace “Ba inda xan je da su kamar yaya??? ka taba sanin su ne, ko kuma ni ka san ni ne? Where did you knw us from” yyi wani murmushi yace “Khadijah, am giving you my words, you are not moving a step forward with my kids, ki fadi duk amount da kika ga yyi suite din ki, tun daga daukar cikinsu, rainon cikin, haihuwarsu har xuwa girman su yanxu and I will pay you, kilan hakan kadai xai sa ki yafe min idan na amshi wahalata da na hada ki da at a very tender age, ni kuma baxan ji kunyan daukansu in kai su gida gun iyayena a matsayin yaran da na haifa out of wedlock ba, shikenan kema na raba ki da wahala na raba ki da rikon ‘ya yan da kika samu ta hanyar fyade da aka maki, sai ki tafi kiyi auren ki hankali kwance ba tare da kin kara tunanin kina da yaran da kika haifa ba ta hanyar aure ba, I am collecting my boys today for ur own good”
Kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bakin ciki da takaici ne fal idanuwanta, xuciyarta ya dinga mugun bugawa, ta hadiye abu da kyar, lkci daya idanuwanta suka yi jajir cikin muryar da ba ta ta ba tace “Come again Aliyu… I didn’t get you” Cire mask din bakinsa yyi gaba daya yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace “You are not daft Iman, you heard me right, or you ask ur bodyguard xai maki bayani da kyau” bai rufe baki ba ta sauke masa mari tana huci, wani murmushi khaleel yyi yana shafa sajensa yace “Seems you both need privacy” daga haka ya juya ya bar wajen har sannan yana murmushi, Aliyu ya kauda kansa na few seconds kafin ya juyo a hankali yana kallonta da wani irin mamaki, hawaye na sauka idonta tana girgixa kai tace “Allah ya isa tsakanina da kai Aliyu, shari’ar mu da kai dama na fada maka sai a lahira, kuma yarana ba naka bane, ba kai ka haifar min su ba, you don’t have any right over them, idan duk duniyar nan xa su hade nan wlh wllh baxan baka su ba, ni na sha wahalan kayana ni na haife su, baka isa ka raba ni da su” ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, hakan yasa su shureim ma suka fara kuka suna rike da ita, kallonta kawai Aliyu yake da idanuwansa da suka yi jajir, ganin khaleel ya bar wajen khadijah ta kama hannun yan biyun ta da sauri ta juya xata bi bayansa Aliyu ya fixgota yayi jamming kofar yana mata wani mugun kallo, lkci daya ta cakumosa tana kuka mai taba xuciya tace “Ka bude mana mu fita Aliyu, ka bude kofar in fita da yarana kar in tara maka jama’a” yanda ta rikice haka yaranta ma suka rikice suna kuka, daukar ta Aliyu yyi ya nufi bathroom dake ward din ya tura ta ciki yace “I will teach you sense Khadijah….” daga haka ya rufe kofar da makulli ta dinga bubbuga kofar a rude tana kuka tana kiran sunansa, Sudais ya kara fashewa da matsanancin kuka yace “Why are you doing this to our Anty, plss let her out” Shureim ya dinga bubbuga kofar shi ma yana kuka yana kiran ta, Aliyu ya hade kansa da bango ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, lkci daya ya juyo ya kama hannun yaran gaba daya suna turturjewa ya watsa masu wani mugun kallo da idanuwansa da suka yi ja, ba shiru suka yi tsit ko wanne a tsorace, ya bude kofar ward din ya fita da su, ward na intensive care ya shigar da yaran tunawa da yayi bai taho da motar clinic din ba, banda kuka babu abinda suke yi suna kallonsa a tsorace, fuskarsa daure yace “I don’t want to hear any of you cry again” shiru suka yi sudais ya riko hannunsa yace “plss bring out our Anty from the toilet” sauke idonsa kasa yyi a hankali yace “Ohk i will do that now” daga haka ya fita ya rufe kofar yanda baxa su bude ba, sama ya wuce da sauri ya shiga office din Muktar ya dau makullin motarsa sannan ya sauko, yana bude kofa su sudais suka yi tsit daga kukan da suke, Shureim yace “Uncle where is she plss” hannunsu ya kama ya fita da su, ya bi ta bayan asibitin xuwa parking space, back seat ya saka yaran gaba daya sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar asibitin. K’asa kuka twins din suka yi a motar saboda Aliyu da ya hade rai, kana ganinsu kasan a tsorace suke barin Shureim, driving kawai yake har ya iso gida bayan yyi parking ya fito ya bude masa motar yace “Come down” da farko kin sakko suka yi, ganin kallon da yake masu duk suka fito, Shureim na goge idonsa cikin rawar murya yace “I thought you where a good friend, plss don’t kidnap us away from our Anty, she will be sad” Duk da hawayen da ya taru idon Aliyu hakan bai hanasa durkusawa gabansu ba ya rungume su gaba daya yace “I didn’t kidnap my kids, I brought you two to ur Granny” Sudais ya xaro ido yace “We left her at d hospital and this is not our home” Aliyu na kallonsu cikin sanyin murya yace “This is your father’s home” A tare suka hada baki gun ce masa “Where is he?” Shiru Aliyu yyi yana kallon handsome boys din, sudais yace yace “Anty told us our father… Is a Barrister, she said he travelled immediately we where born and that… he will come to us one day” Jikin Aliyu yyi mugun sanyi yana kallonsu, Shureim yace “We will love to see our dad” mikewa Aliyu yyi ya kama hannunsu ya wuce cikin gida da su. Sudais ya bata fuska kamar xai yi kuka yace “I thought you are taking us back to our Anty” gaba daya yan gidan na parlor xaune ana jajanta abinda Kyauta ta ma Anty khadijah, saleem sai cewa yake da ma da shi aka je ya lallasata ya cire mata hakora ya ga wanda ya tsaya mata, mumy dai bata ce komai ba sai kallon Anty khadijah dake kwance kasa take duk jiki yyi tsami don ma ta gasa jikin da ruwan xafi, baki a kumbure har da ido, iklima ma an sallamota tana sama a kwance, gaba daya occupant din parlorn suka dinga kallon Aliyu da twins din hannunsa, Anty khadijah ta mike xaune da sauri ita ma tana kallonsu, Baby ta mike da mugun mamaki tana kallon yaran tace “Laah yaran da muka gani a kasuwa daxu, yaya where did u knw dem from, mai ya samu kan wannan” Aliyu ya isa har gaban Mumy dake kallon yaran ya sake hannunsa, a sanyaye yake kallonta, yyi gathering courage da kyar yace “Yaran da Iman ta haifa kenan, she got pregnant after the incident” Ba Anty khadijah kadai ba har Mumy sai da ta girgixa ta mike tana kallon yaran dake ta kallonta sannan ta mayar da dubanta kan Aliyu cikin wani yanayi tace “How did you knw Abuturrab, where did you get dem from???” hawaye suka shiga sakko masa yana kallon mahaifiyar tasa a sanyaye yace “I met them today mum, I don’t knw if Khadijah will ever forgive me… I ruin her at a very tender age, this boys are my blood, Mumy na kawo su gida ne don nima in yi facing ko da kadan ne daga cikin abinda tayi facing a rayuwarta duk da ni na fita ga ta….” Kasa ci gaba yyi ya bar parlorn ya wuce sama hawaye na sakko masa, Anty khadijah dake ta xufa ga cikinta da ya tsure tace “Mun shiga uku, Anty fati kin ga wani sharri koh, kin ga wani hauka irin na Aliyu ko? yaushe Aliyu ya isa haifan wa ennan yaran? ta je an mata ciki a wani waje ta makala masa kuma ya yarda saboda wawa ne shi… a ina ma ya ganta???” Kai kana gani kasan kame kame kawai take duk ta rude, Su Shureim sai bin kowa na parlorn suke da kallo a tsorace, baby ta fashe da kuka cike da tausayin yayanta, Salim ma sai kallon yaran yake a duk jikinsa yyi sanyi ganin kamannin Aliyu sak tare da su, Mumy ta fashe da kuka sosai ita ma tana kallon yaran, hakan yasa su ma suka fashe da kuka, babu abinda take gani tare da yan biyun sai Aliyunta lkcn da yake kamar su, Anty khadijah ta haura sama kusan a guje tana cewa “Yau na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, ina yake ya xo ya fitar mana da shegun nan da ake shirin kakaba masa, ya xo ya mayar da su inda aka basa su, amma Allah ya isa tsakaninmu da yarinyar nan, ta rasa wanda xata ma sharri sai Aliyu saboda tsautsayi ya gifta tsakaninsu? Ni dai nasan da hankalin Aliyu baxai mata fyade ba, sharrin shaidan kawai da kuma sharrin ta don ita ke shisshige masa, wlh baxa mu amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri’ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d’an yayata ba” tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace “Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss” nurse na kallonta da confusion tace “Yanxun nan na shigo madam” da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace “Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana” khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace “Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su” ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace “Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi” Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace “Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana” a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa “Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku” umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa “Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana” tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma ‘yar tata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103Next page

Leave a Reply

Back to top button