Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace “Who’s there?” Muryar small mum dinsa yaji tana cewa “Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba” a hankali yace “Nayi a nan Anty… Was having a slight headache ne” tace “Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani” daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace “Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it’s her look alike…. But….” mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace “Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah….” Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace “Who’s there?” Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace “Yaya ni ce” yace “Ya aka yi” bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace “How was ur nyt?” Ya dauke kai yace “T’was good” Tace “Mumy wai ka fito ka yi breakfast” yace “Ohk” daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace “Bacci kike na tashe ki?” Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace “Na tashi” yace “How are you feeling now?” Tace “Alhmdllh, ina kwana” yace “Lafiya lau” jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace “You cried!” Ta girgixa masa kai kawai, yace “Noo you cried malama” lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace “Shiga ciki” ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin SUDAIS da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye…. Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana… tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall, taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace “Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba” bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace “There” ta karaso ta dau shayin yace “With d bread” girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace “Look…” ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace “ur injection” tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace “You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji” yyi kasa da murya yace “And please kar sake kuka ur condition isn’t encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai…” Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la’asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace “Who’s there?” Yace “Koh” bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace “Sorry….” Da sauri ta katse sa tace “Ohh bakomai” yace “Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama” ta d’an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace “Dama cewa xan yi, sorry… me yasa kika gudu daxu?” Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace “Toh kin ci abincin” kai kawai ta gyada, yace “How you feeling now” tace “Naji sauki” duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace “Alluran ki…” Da sauri tace “No naji sauki, xan sha maganin” shiru yyi na kusan thirty seconds, yace “Malama” sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace “ohk… Ki sha maganin” daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar.

Haske writers association????

Noor-Al-Hayat

By khaleesat Haiydar????✍????

11….

Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba yana sauraren fadan Kanwar Dad din tasa, A fusace tace “Wai ba da kai nake ba ka min shiru Aliyu” ya dago ya kalleta da kyar don har wani ciwon kai fadan ke sa masa, ya marairaice fuska yace “Wllh ina ji Anty, ina jin ki” tace “Nace ka gaya min me yasa ka bar min breakfast kayi ficewar ka daxu?” yace “kiyi hakuri mum, ban san xan jima haka bane” Tace “To xaka ga uwar da xata baka dinner yau a gidan nan kuwa” murmushin karfin hali yyi ta juya tayi ficewarta, komawa yyi ya kwanta kansa na ci gaba da sara masa, tun safe har xuwa lkcn bbu abinda ya ci ban da ruwa da yake sha, bbu inda bai shiga ba a wasu daga streets din UK ko xai ga Iman amma sam bbu alamarta, shi ya ma rasa gane ko ita ce ya gani ko ba ita ba, ya mike xaune da damuwa yace “Ya Allah…” Har agogo yyi stucking karfe shidda na yamma yana xaune dakin, aka bude kofa tare da sallama, Maryam ce ta shigo dakin tace “Yaya Aliyu are you sick?” Ya kalleta yace “No I am not Maryam” ta xauna gefen gadon tace “Toh naga tun jiya duk ka xama wani iri, gashi daxu ko breakfast baka yi ba ka fita, nasan baka yi lunch ba ma” yace “Kirana aka yi na fita” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ya school ko baki je ba yau?” Tace “Naje daxu na dawo” yace “Ohk, ina su Baby da Fadil” tace “Suna assignment a daki” yace “Idan Anty ta gama lunch ki dibar min kadan ki kawo min” tace “Toh” sannan ta mike ta fita, ba a dau lkci ba kuma ta kawo masa abincin da ruwa ta ajiye masa.
Kulawa sosai Khaleel ke bata a kwanaki ukun da tayi a gida bata je makaranta ba duk da shi ya hanata xuwa makarantar sae taji sauki sosai, kuma cikin ikon Allah ta warware bata jin ko wani ciwo sae dai Kawai ta kasa mance incident din ne, ba a minti goma Aliyu bai fado mata ba, ko kadan Khaleel bai son ganinta cikin damuwa, he’s as kind as she never expected, duk da wani lkcn he is pretending not to be, kamar dai yasan tana da damuwa, bata kuma yi mamakin ya gano haka ba tunda likita ne shi din, duk Safiya kafin ya fita sae ya tabbatar ta karya ta sha magungunan ta, da yamma kuma idan xae dawo it’s either ya taho mata da fruits ko abinci, har books masu dadi na turanci ya kawo mata ta dinga karantawa, ae kuwa books din also contributed don nishadi suke sa ta idan tana karantawa, idan kuma ta gaji da karatun ta dauko hotunan su Sudais da Shuraim tun daga lkcn da suke jarirai har xuwa girmansu, yawanci kuma hotunan duk tare da Sudais ne wannan dalilin yasa bata gajiya da hotunan, ko gida bata fadi ma su Umma bata da lafiya ba. Yau kamar ko da yaushe tana kwance parlor bayan ta raka su Vanessa da suka xo gaishe ta tun da rana, bell aka danna, ta mike don tasan shi ne, ta isa gun kofar ta bude, gaishesa tayi tana kallon sa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, lkci daya kuma yana tambayarta ya jiki, ta karba tace “Da sauki” yace “Maa sha Allah” xae juya tayi saurin cewa “Are you sick?” Juyowa yyi yana kallonta yace “Just Stomachache, but na sha drugs da sauki sosai” da damuwa tace “Allah ya sauwake” yace “Ameen” daga haka ya rufe mata kofa ya shiga apartment dinsa. Ajiye ledan tay kan table ganin fruits ne, tana ta xaune parlor har kusan Magrib kafin ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, nan parlorn tayi sllh, ta gama addu’o’inta sannan ta mike ta shiga kitchen, tunanin me xata dafa ta shiga yi don yunwa take ji, garnished cous cous tayi da yaji kayan hadi, duk da bashi da yawa kawai tayi deciding ta debar masa, ta zuba a karamar warmer snn ta sa hijab ta fita kai masa, a hankali ta kai hannu ta danna bell, sai da ta sake dannawa ya bude kofar, singlet ne jikinsa da dogon wando, kallon sa ta tsaya yi ya juya ya koma kan kujera ta bi sa da ido, can ta bi bayansa ta rufe kofar, ajiye abincin hannunta tayi ta durkusa gefensa tana kallonsa da damuwa tace “Cikin ne har ynxu?” Gyada mata kai yyi a hnkli yace “But… Sure I will be okay” cike da karfin hali yyi maganan, shiru tayi tana kallonsa taji tausayinsa sosai, a hnkli ya sauko kan kujeran ya duka kan gwiwowinsa, kamar xata yi kuka tace “Ko xaka je asibiti” girgixa mata kai kawai yyi, sai kuma ya kwanta nan gun, kana ganinsa kasan namijin kokari kawae yake, hawaye ya cika idonta, tashi xaune ya kara yi yana runtse ido a hankali yace “Get me water pls” tashi tayi da sauri ta nufi fridge ta bude taga duk masu sanyi ne, ta shiga kitchen ta dau glass cup ta dibo masa na tap, tana dawowa ta duka gun sa ta mika masa ya karba ya fara sha, sae kallon sa take sai ka rantse tare cikin ke masu ciwo ynda tayi da fuska, lkci daya ya ajiye glass din ya mike ya nufi bathroom dake parlorn, ita ma ta mike tsaye, amai sosai yake yi a bathroom din, ta kasa motsawa daga inda take, can ta durkusa ta fashe da kuka, yana fitowa parlorn ya hade kansa da kujera, tashi tayi ta isa kusa da shi cikin rawar murya tace “Don Allah mu tafi asibiti plss” ya dago idanuwan sa da suka sauya xuwa ja, komawa baya tayi da sauri don idanuwan suna kalau ma tsoronsu take barin kuma yanxu da suka kara wani kala kan na da, da alama ya kasa mata magana don girgixa mata kai kawai yayi, xai komar da kansa kan kujerar tayi karfin halin rikosa da sauri tace “Doctor plss let me drive us to the hospital, ina makullin motar yake” murya can kasa yace “I will be alright Khadija, go to my room xa ki ga 1st aid box…” Bata jira ya gama ba ta mike da sauri ta shiga dakin, da box din ta dawo, ta ajiye kusa da shi, ya xamo kasa idonsa lumshe ya bude box din, bayan yan sakwanni ya bude idon ya dau wani allura da syringe ya mika mata, ta bude ido da mamaki ta dai karba ya mayar da kansa kasa, rasa abin cewa tayi, can dai ta balle bakin alluran ta xuke a syringe tayi karfin halin cewa “Ga shi nan” ja baya tayi tana xare ido ganin ita yake nufin xata masa alluran, duk da ta iya kawai niyyar nuna masa bata iya ba ta yi, amma tausayinsa da yanda shi ma ya nuna damuwarsa lkcn da bata da lafiya yasa ta kasa, hannunta na rawa tayi masa alluran, kin bude ido yyi ta koma baya tana kallonsa, bayan wasu mintuna ya mike da kyar ya kwanta kan kujera, ko minti goma bai kara ba bacci ya dauke sa, dawowa tayi kusa da shi tana kallon sa da tausayi ganin alluran bacci yasa tayi masa, mikewa tayi ta dauke glass cup din da abincin da ta kawo ta kai kitchen, ta mayar da box din 1st aid din daki, tayi disposing alluran da tayi masa sannan ta xauna kusa da shi tana kallon sa, giransa kadai ma abun kallo ne a fuskarsa kafin a xo ga long lashes din idonsa, a hankali ta sauke idanuwanta kan dogon hancinsa da ko Kadan bai da miskila xuwa bakinsa, kai kana ganinsa kasan duk yanda aka yi yana da alaka da larabawa, dauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, da sauri ta tashi tunawa da tayi bata yi isha ba, alwala ta sake yi ta gabatar da sllhn nan parlor, tana xaune tana azkar wayarsa ya fara ring, har ya katse bata mike ba shi ma kuma bai ko yi motsi ba, ganin an sake kira ta tashi a hankali ta nufi kusa da shi ta durkusa tana laluban aljihunsa ta fiddo wayar tana kallon screen din, Jawahir ta gani jikin screen din wayar, har ya katse tana kallon wayar, can ta ajiye a hankali ta daura chin dinta bisa gwiwowinta tana kallonsa, bacci yake sosai, ta so tashi ta wuce apartment dinta amma ta samu kanta da kasa yin hakan, bayan minti kusan ashirin ta dago kanta ta jinginar kusa da shi, daga haka bacci yyi gaba da ita a yanda take, A hankali ya bude idanuwansa yana bin parlorn da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kanta, ya mike xaune da sauri yana kallonta, kallon agogo yayi yaga biyu har yyi, fuskarsa ya kai dai dai nata, cikin bacci taji hannu a forehead dinta, ta bude ido da sauri, a hankali ya manna mata lips dinsa a kumatunta, a tsorace ta ja baya xata mike yyi saurin riketa, 6ata fuska tayi hade da buge hannunsa tace “Meye haka” sakkowa kasa yyi yace “Me kike yi a nan?” Sakin baki tayi tana kallonsa, can ta turasa xata mike ya ki saketa, hawaye ya cika idonta tayi da ta sanin kulasa ma da tayi, ya jawota jikinsa yana murmushi a hankali yace “Thanks for ur care Khadija, Neva knew you where this sweet….” Ta kara hade rai tace “Sake ni malam” ba musu ya saketa, ta mike ta nufi kofa, yace “Uhn.. it’s pass 2 now fah” da sauri ta kalli agogo, dawowa tayi kamar ya fada mata mugun abu ta marairaice tace “Lahh ban sani ba… I don’t know it’s late….” yace “Wait… But… But it seems u came with food daxu, ina abincin” da kamar baxata ce masa komai ba sai kuma tace “yana Kitchen” yace “I am just hungry” kitchen ta wuce ta kawo masa abincin sai a sannan ta tuna ita ma bata ci abincin ba ai, tashi yyi ya shiga toilet din dakinsa sai da ya wanke bakinsa yyi wanka snn ya fito sanye da jallabiya yana goge gashin kansa da karamin towel, duk ta gaji da jiransa ya fito ya rakata, ya xauna ya bude abincin ya dau cokali ya fara ci, kallonsa take ta yi kafin ta mike ta tafi ta bude fridge ta dauko masa ruwa, sai da ya kusa cinye abincin ya sha ruwa sannan ya kalleta da sauri yace “But daxu kamar ruwan tap kika bani koh” tace “Uhn” xaro ido yyi yace “Subhanallah, but I don’t take….” sai kuma yyi shiru, ita dai bata ce komai ba banda hararansa da take, jinginar da kai yyi da kujera ya lumshe ido, mikewa yayi ya shiga bathroom din parlor ya fito da alwala, a hankali tace “Ka raka ni pls dare yyi sosai” kallonta yyi kafin yace “Ohk as you wish tunda cinye ki xan yi a nan” daga haka ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofa ta matsa kusa da shi da sauri, ya fita tana biye da shi a baya suka shiga apartment dinta ya rufe kofar, ta sauke ajiyar xuciya tana bin parlon da kallo yace “Toh tafi ki kwanta” daki ta nufa yyi saurin cewa “Waittt… Xo ki kulle kofar tukun” dawowa tayi tana kallonsa ya buda ido yace “Sai da safe, I appreciate ur care” bata ce komai ba xai fita tace “You have…. A call” ya juya ya kalle ta, duk sai taji she sounds stupid, yace “Did you pick?” Tayi saurin cewa “Nooo, I just remembered now, I didn’t even check, just heard the phone ringing” ita kanta tasan kame kame kawai take, yayi murmushi yana shafa lallausan gashin kansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103Next page

Leave a Reply

Back to top button