Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace “Nan ne gidan….” Hajiya Maimuna ta xaro ido tace “Nan kike xuwa?” Ta girgixa kai da sauri tace “Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah” kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace “Ina masu gidan nan” Mai gadin yace “Daga ina?” Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace “Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba” Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace “Hajiya Amina mun wuni lafiya?” Hajiya Aminar tace “Alhmdllh, in ji lafiya” Hajiya Salaha tace “Ba lafiya ba, ina d’an ki yake?” Da mamaki tace “Da na kuma?” Cike da jaraba Hajiya Salaha tace “Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan” Hajiya Amina tace “Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?” Hajiya Maimuna tace “Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da ‘yar mu” bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma ‘yar ta… Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki na rawa, Dai dai nan kuwa sai ga shi ya fito parlor, tsaye shi ma yyi yana kallonsu da mamaki, Mahaifiyarsa da ranta ya gama baci tace “Sadeeq, what’s between you two” ta fadi haka tana nuna masa khadijah, kafin yace komai Khadijah tayi saurin cewa “Nothing ma, kawai yana kawo min abinci yana ajiyewa cikin flowers ne in dauka in ci…” Buge mata baki Hajiya Maimuna tayi ta kunduma mata xagi tace “Kece sadeeq? Makira yar iska? Ke ta tambaya?” Sadeeq dai na tsaye yana kallon ikon Allah ya kasa cewa komai, mahaifiyarsa tace “Magana nake maka malam” ya juya ya kalleta yace “Mum I don’t think I have time explaining my self to any of this women, ni dai nasan the girl told me about how hungry she was ba’a a bata abinci a gidan, and I volunteered….” Uwarsa ta xaro ido tace “Volunteered what Sadeeq?” Ya d’an hade rai yace “She requested in dinga ajiye mata abinci a flowers din kofar gidansu thats all, sannan tun ranan bamu sake haduwa da ita ba cox dama gun wancen mai kantin muka hadu, sai kuma yanxu da take tsaye a nan, ashe dama taimako na xama laifi, kuma da ba su barta da yunwa ba har xata ce in dinga ajiye mata abinci she’s always hungry? Ba komai kuma yasa nake ajiye mata abincin ba sai don nasan bbu illar da ya kai barin ‘ya mace da yunwa, bana son ta shiga wani hali shi yasa, if not what’s my connection with her da har xan dinga bata 3 daily meals?” Tunda ya fara magana su Hajiya suka saki baki suna kallon Khadijah da ta sunkuyar da kai, Hajiya Maimuna tace “Toh kayi na farko kayi na karshe, dauki 3 daily meals din naka ka kai gidan almajirai ko marayu, kada ka sake xuwa mana kofar gida da abinci, ita kuma yanxu xa mu koma gida mu ji wanda yake barin ta da yunwa da tace she’s always hungry” Hajiya Salaha tace “Sai ma kin fada, kuma wllh Allah ya isa tsakaninmu da ita tunda mu ta ke bi gida gida a anguwar nan tana cewa muna barin ta da yunwa, bbu abinda xai hanani yi mata jina jina yau” Daga haka ta ja ta xasu fita, khadijah ta hade hannunta tana kallon sadeeq cikin rawar murya tace “I am very sorry” Rankwashi Hajiya Salaha ta kai mata da karfi ta ja ta suka fice gidan, Hajiya Amina ta kalli d’anta tace “Daga this very moment na raba ka da abinda kake yi” Hajiya Maimuna tace “Da dai ya fi maku” daga haka ta bi bayan su. Duka da xagi kam khadijah ta sha shi ranan, duk ta fita hayyacinta sai kiran Ummarte take, don Kansu suka kyaleta daga karshe, indomie da kwan kuma suka dauke suka juye a plate suka cinye. Tun daga ranan sadeeq bai sake ajiye mata abinci ba, kafin kwana biyu ta rama duk ta xama wata iri har lkcn ta ki kwantar da hankali ta ci abinci da suke girkawa, sai taji yunwar xae sumar da ita take tura abincin ko yaya shi ma wani lkcn har da amai sai tayi, tafe take kamar iska xai kadeta tsabar weakness dake tartare da ita, ta isa gun mai kanti ta basa takardar da aka aiketa ya karba yana tsokanarta kamar yanda ya saba, ita dai bata ce komai ba unlike before da xata fara masa turanci, kiranta taji anyi ta juya da sauri jin muryar, ta ga Sadeeq tsaye bayan ta, ta yi murmushi tace “Good evening” a hankali yace “How you?” Tace “Fyn” kallonta ya dinga yi ganin yanda ta rame, ta juya ta karbi sakonta tace “Bye” yace “Khadijah” ta juya da sauri tana kallonsa, yace “You are always hungry koh?” Shiru ta yi hawaye ya cika mata ido, yace “I am sorry I cant help it” ta ce “Don’t worry, I appreciate the one you did before…..” Hannu ya sa a aljihu ya Ciro kudi ya kirga dubu biyar ya mika mata yace “Toh gashi ki boye wannan ko biscuits da doughnut sai ki dinga siya kina ci a nan kinji?” Shiru ta yi ya kamo hannunta ya sa mata yana murmushi ya gyada kai yace “Yeah” rike kudin tayi ya sake hannunta yace “See you some other time” ta daga masa hannu hawaye cike idonta tace “Thank you” hanya daban daban suka bi tana isa gida ta boye kudin, tana son fita ta siyo abinda yace da daddare ta kwanta amma tana tsoro, hakan yasa ta sha ruwa kawai ta kwanta cikinta na kugi don wake da taliya aka yi daren ranan. Bayan kwana biyu tana xaune ita kadai tsakar gida tana tankaden uban garin masaran da Hajiya salaha ta hada ta shi, duk kayan jikinta ya koma fari kamar warce ta yini a kusa da injin nikan, ga hawaye da ya bubbushe fuskarta, a kan tankaden nn tun safe Hajiya Salaha ke dukanta da tayi sai tace bai yi ba, hakan yasa take yi a hankli ynxu bayan ta ci kukanta ta koshi, bude gate aka yi ta daga kai ta ga Ummarta, still tayi rike da rariyar, kamar yanda ita ma Umma ta tsaya kallonta ko kiftawa bbu, hawaye ya cika idon khadijah ta mike da gudu ta nufeta ta rungumeta tace “Ummata” sosai Umma ma ta rungumeta duk jikinta yyi sanyi, can ta janyeta jikinta tana kallonta daga sama har kasa, hawaye ne ya cika idonta ta mata alamar ta dauko takalmarta, khadijah ta koma ta dauko takalman da duk sun tsinke ta sa su haka, Umma ta ja ta suka fice daga gidan, Khadijah dake ta bin ta tace “Ummata tafiya xa kiyi da ni?” Hawaye na sakkowa idonta tayi tambayar, Umma ta gyada mata kai kawai don ta kasa cewa komai, suna isa dai dai gidansu Sadeeq khadijah dake murmushin farin ciki tana rike da hannun Umma gam tace “Umma I have a frnd here, can I just go and bid him goodbye, he is more than kind” Umma ta kalleta for d 1st time ta bude baki cikin sanyin murya ganin hawayen dake ta sauka idon khadijar, tace Some other time dear, khadijah ta gyada mata kai har suka wuce kofar gidan, da sauri Umma ke janta har suka isa main road ta tsayar da adai daita, direct sai motor park, ta biya masu kudin mota bayan yan mintuna motarsu ya tashi xuwa garin kano, bacci Khadijah ta dinga yi jikin Umma don tun asuban fari aka tasheta a can gidan, har suka isa kano bacci take yi, Umma ta tasheta, ta bude ido a hankali, suka sauka cikin motar Umma na rike da ita suka fito bakin titi ta dau adai daitan da xae kai su har gidan da take aure. Ba laifi babban tsakar gida ne compound din mai dauke da small building har hudu, ko wani building na da parlor da daki a cikinsa, sai babban kitchen dake tsakar gidan, da kuma bayin wanka biyu da toilet ma biyu, a gefen kitchen kuwa ga rijiya a rufe, gidan da Umma ke aure kenan, tana kuma auren d’an kasuwa ne mai mata biyu, yara ne su kusan biyar ke ta wasa tsakar gidan da yake da yamma ne kuma ranan alhamis ba islamiyya, da wasu yan mata uku dake xaune kan tabarma suna danne dannen waya, umma ta amsa gaisuwar da yara kananan ke mata ba tare da ta sake kallon gun da yan matan suke va ta fiddo key ta bude part dinta, khadijah dai na tsaye sai kallon yaran take kamar yanda su ma ke kallonta, can ta kalli yan matan taga su ma kallonta suke, Umma ta kalli direction din kitchen jin kamshin girki suka yi ido hudu da Shafa kishiyarta dake lekosu ta cikin kitchen din, suna hada ido kuwa tayi saurin dauke kanta, Umma ma ta dauke nata kan, can ta hango uwar gidan mai gidan nata ita ma tana lekota ta windown parlornta ita ma suna hada ido tayi saurin dauke kai, Umma ta bude kofar ta ta ja hannun Khadijah suka shiga ciki ta dage labule ta daura kan kofar kasancewar parlorn ya dau xafi.