Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR-AL-HAYAT
Khadijah ta xauna kan kujera tana kalle kallen parlorn tace “Umma nan ne gidan ku koh?” Umma ta bude fridge xata dauko mata ruwa tace “Ehh” Karban ruwan tayi tace “Umma yunwa nake ji ban ci komai ba” Umma tace “Toh me xa ki ci yanxu?” Murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta langwabar da kai tace “Indomie Ummata” Umma ma ta yi murmushin ta juya ta fita, Khadijah ta dinga bin madaidaicin parlon da kallo kai kana ganinta kasan she is just happy, muryar Umma taji tana kiranta daga waje ta fita da sauri ta sa takalminta tace “Gani Umma” Umma ta mika mata ruwa a buta tace “Gashi ki fara yin alwala kiyi sallah” tace “Toh” sannan ta durkusa tana alwala tana yi tana kallon yaran dake ta kallonta har da matar dake girki a kitchen, Umma ta shiga kitchen din ta dauko indomie daya ta fito ta kai parlorn ta sannan ta dawo rike da naira dari tana mika ma wani yaro da baxai wuce shekara biyar ba tace “Mudassir je kanti ka amso min kwai biyu” yaron ya karba ya wuce waje da gudu, Karamin tukunya Umma ta daura kan electric madaidaici dake parlorn ta bayan ta shimfida ma Khadijah darduma, khadijah na idar da sallahn Umma tace “Kin fara xuwa school a can gidan” girgixa kai tayi tace “A’a, kin san me Umma ta” Umma tace “Bari ki ci abinci” soya mata kwan da yaron ya kawo Umma tayi sannan ta ajiye mata a gabanta da ruwa a cup ta mayar da wani tukunyar ta sa mata ruwan wanka, Umma tayi tagumi tana kallon yanda take cin abincin, kana ganinta kasan yunwa kawai take ji, kafin ta gama Umma ta juye mata ruwa ta kai bayi da sabulu, ita ta rakata bayin sannan ta koma parlorn, khadijah na gama wankan ta fito daure da xanin da Umma ta bata, Shafah dake girki daga cikin kitchen ta bi ta da wani kallo hakan yasa tace “Ina yini” dauke kai tayi kamar bata ji ba, khadijah ta wuce cikin parlorn Umma tace “Wannan matar dake girki na gaisheta bata amsa ba” Umma tace “Kar ki sake gaisheta” daga haka ta cire hular kanta bayan ta kawo mata man shafawa, sakin baki tayi tana kallon gashin don tun kalaba shidda da ta yi mata kafin kawu ya tafi da ita kasancewar gashinta na da tsayin bala’i kuma bata son ana taba shi, Umma bata dai ce komai ba, ta dau gyalenta tace “Ban ce ki fito ba ki jira ni har in dawo” khadijah tace “Toh” daga haka Umma ta fita, bayan kusan minti ashirin ta dawo rike da Leda ta sake labulen parlorn ta bude ledan ta fiddo wasu dinkakkun riga da skirt kana ganinsu dai kasan taje ta karbo su ne tace “Tashi ki sa, gobe xan je kasuwa in siyo maki kaya kinji” khadijah ta sa kayan tace “Umma in kunna TV?” Umma tace “Ban ce ba” kwanciya tayi kan kujera bbu bata lkci bacci ya dauketa, Umma ta xuba ma jikinta ido ganin shattin duka, tagumi tayi tana kallonta tana tausaya ma marainiyar. Khadijah na tsugunne tana alwala tsakar gida da magrib bayan Umma ta tasheta tayi sllh taji an fixge butar daga hannunta ta daga kai tana kallon yarinyar da baxata wuce ta ba, Yarinyar ta murguda baki ta tafi ta kara ruwan ta fara alwala, mikewa khadijah tayi tace “Are you okay?” Yarinyar ta balla mata harara tace “Ki fadi wanda xan ji mana” khadijah bata sake cewa komai ba har yarinyar ta gama sannan ta wuce da butar parlornsu, khadijah ta xaro ido sai kuma ta juya ra wuce gun Umma dake parlor ta tsaya bakin kofa a hankali tace “Umma wata yarinya ta karbe butan ta tafi da shi” Umma ta fito tace “Wace yarinya?” Nuna mata parlorn da yarinyar ta shiga tayi, Umma ta kama hannun ta suka je har kofar parlorn ta bude labule tace “Wacece a ciki” Khadijah ta dinga bin yara kusan biyar dake parlorn da kallo sannan ta nuna mata yarinyar, Umma tace “Rahmah dalilin me kika karbe buta tana alwala?” Yarinyar da ta tsuke baki tace “Toh Anty namu ne ai” Umma tace “Kar ki sake, idan ko ba haka ba sai na bata maki rai” daga haka ta ja hannun Khadijah suka bar wajen ba tare da ta bi ta kan Uwarsu Hasana dake xaune parlorn ba, Umma ta dauko buta parlorn ta ta bata, Wata yarinyar ce ta shigo parlorn da abinci a er warmer ta ajiye ta juya ta fita, Umma ta daga kan khadijah dake kafarta a kwance tana bata labarin abubuwan da aka dinga yi mata gidan Kawu sannan ta mike ta jawo warmer din, shinkafa ce da miya sai nama biyu da salad a gefe, iya cin ta ne abincin, ta daura dankwali ta fita xuwa kitchen din ta dau wani plate ta bude tukunkya xata debi abinci sai ga Shafah da sauri tace “Amma dai Amina kinsan ba ke ce da kitchen ba, don haka baki da hurumin shigar min kitchen” Umma ta kalleta tace “Ae kin gan ni da bakuwa kika yarfo min er shinkafa a cooler kamar mayunwaci, don haka ke ma baki da hurumin hana ni debar mata abinci” Shafah tace “Bakuwa? Kin gaya min xaki yi Bakuwa in sa girki da ita ne, to wllh kin yi kadan ki kara diban wani abincin don na almajirai ne” Umma ta Debi shinkafar kusan cikin plate ta xuba miya kai da nama biyu tana kallonta tace “In ji duka” daga haka ta fice daga kitchen din Shafah tace “Ai kuwa ni da ke shege ka fasa Amina, mu xuba” tsaye Umma ta ga Hasana bakin nata parlorn tana lekosu tana ganinta ta shige ciki da sauri Umma tayi tsaki ta shiga ciki ta ba Khadijah abincin hannunta. Da yake khadijah tayi baccin rana har karfe goma idonta biyu tana ta ba Umma da tayi tagumi tana saurarenta labarai iri iri, Yar Shafa ta farko fadila ta bude kofa tace “Abba yana kiran ki” daga haka ta juya ta bar gun, mikewa Umma tayi ta fita tare da Khadijah tana rike da hannunta suka tafi turakar mai gidan, ba wani babba bane mai gidan don baxai wuce 48 ba, Shafah na xaune kan kujera da Hasana a gefenta, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah k’asa ta xauna ita na, Gaishe da shi tayi, khadijah na kallonsa tace “Good evening Sir” idonsa a kanta yace “How are you” tace “I am fine” Shafah da Hasana aka kyabe baki, mai gidan da suke kira da Abban Fadila yace “Wacece wannan Amina?” Umma tace “Kayi hakuri na so kiran ka tun kafin in iso kano daxu sai da bani da charge, duk da mun yi da kai gobe xan dawo kawai kuma na fasa, wannan ‘er marigayin tsohon mijina ce Khadijah, na taho da ita ba tare da ixinin ka ba, kayi hakuri ban ji dadin yanayin da na same ta bane shi yasa na daukota bbu shawara da kai” shiru yyi bai ce komai ba, can ya jinjina kai yace “Toh Allah ya kyauta” Su shafa aka kwalalo ido ana kallon khadijah jin wai er kishiyarta ce da ta rasu, Abban fadila yace “Dalilin ki na shiga kitchen ba ke ce da girki ba daxu nake son ji? Shi yasa ma na aika a kira ki” Umma tace “Ehh toh, sun ganni da yarinya mun dawo Abban fadila, sai da aka tashi xubo min abinci da magrib sai aka xubo dai dai wanda ni xan ci a yar cooler” yace “Shine aka ce ko shiga ki diba? me yasa baxa ki nemi izini gun mai girki ba ko kuma kice ta k’ara maki kina da bakuwa, ke ce kadai me karya min doka a gidana fa Amina” Umma tace “Watana kusan uku gidan nan yaushe da yaushe na karya maka doka Alhaji?” Hasana sai wani blushing ake Shafa na taya ta, Abban fadila yace “Toh tashi ki je” mikewa tayi ta daga khadijah da su Hasana aka bi da harara ta fice parlorn ta koma nata, daki ta nuna ma khadijah ta tafi ta hau saman gado ta kwanta, khadijah tace “Toh Ummata” sannan ta shiga dakin ta kwanta hade da lumshe ido don har ta mance Rabon da ta hau gado har tayi bacci a kai. Washegari da asuba Umma ta tada Khadijah taje tayi sallah bayan ita ta idar, khadijah ta fita tsakar gidan rike da buta tana mitsika ido, yara ne kusan biyar ko wanne na alwala tana kokarin shiga bayi tayi fitsari taji an fixgota ta juyo da sauri a tsorace, yarinyar da ta kawo ma umma abinci jiya ce, tana kallo yarinyar ta shiga bayin, ta ja gefe a hankali ta tsaya tana jiranta, bata gaya ma Umma abinda ta sake yi mata ba, bayan ta idar da sallah ta koma daki ta kwanta ta ci gaba da baccinta. Gari na fara wayewa Umma ta kuma tashinta daga baccin ta kai mata ruwan xafi bayi da sabulu da soso, ba a dau lkci ba khadijah ta dawo tana wasa da yatsunta a hankali tace “Umma wata yarinya ta fitar min da ruwan ta sa nata ta rufe bathroom din” fita umma tayi ta tafi kofar bayin da sauri tana kallon xanin waye kafin tayi kwafa ta nuna ma Khadijah kujera tace “Xauna nan ki kyaleta kawai, idan ta fito ki shiga” khadijah ta xauna tace “Toh” umma ta koma ta ci gaba da sharanta, yarinyar na fitowa khadijah ta mike ta shiga da ruwan da kyar ta juyo xata dau sponge case wata ta sake fitar da ruwan nata ta hankadota waje ta shiga ta rufe kofa, tsaye khadijah tayi baki bude tana kallon bayin, dai dai fitowar Umma da abun kwashe shara da tsintsiya, karasawa tayi da sauri ta tura kofar ta janyo ruwan waje ta fiddo sabulun yarinyar sannan ta dau na Khadijah ta saka tana kallonta tace “Xo ki shiga” yarinyar ta fashe da ihu tana buga kafa, khadijah dake kallonta baki bude a hankali tace “Why are they behaving like this” Umma ta shigar da ita bayin tace “Maxa ki fara wanka” Hasana ce ta fito da sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace “Walida ya aka yi, me ya faru” cikin kuka walidar tace “Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin” Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace “Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan” Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace “Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?” A fusace Hasana tace “Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu” Shafah ta rike ha6a tace “Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta” Hasana tace “Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su” daga haka ta kalli yar ta tace “In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe” daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa “Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala’in nan, muna xaman xamanmu dai” Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace “Shegiya kawai” kallonta khadijah tayi tace “Back to sender” sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace “Go outside and greet him. Come back immediately after that” khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace “Good morning sir” ya kalleta yace “Morning yar turawa, how was ur nyt?” Ta washe hakora tace “It was splendid” yace “Good, ina mamar taki?” Ta kalli kofa tace “Tana ciki” yace “Kira min ita” Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace “Naga baki shigo gaisheni ba” Umma tace “Bayan nayi sallah I just slept off” yace “Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata” Umma tace “Toh nagode, Allah ya kai mu” Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace “Gashi ki siya biscuit” xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace “Amsa” ta karba da hannu biyu tana murmushi tace “Nagode uncle” daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace “Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?” Hasana tace “Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan” Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace “Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??” Shafah tace “Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala’i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa’atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba” Hasana tayi shewa tace “In sha Allahu kuwa” Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu’ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita.