Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaisawa Hajiya Rukayya suka yi da Mami, Mami tace “Ki ce kun dawo Nigeria kenan Hajiya” Hajiya Rukayya tace “Ina fa, just came a week ago to put things in other, ina ga xuwa jibi ma xan koma” Mami tace “Ayya, ashe baxa mu hadu ba kenan, ya yarana fa?” Hajiya Rukayya tace “Suna can, Jaheed ne dai ke Lagos” Mami tace “Toh maa sha Allah, naji dadin da kika kira wllh, kina Abuja koh?” Hajiya Rukayya tayi dariya tace “Toh ai baki sani ba, Aliyu na gani ma ya sa na kira ki yanxu” Mami tace “Haba dai…” Hajiya Rukayya tace “Wallahi kuwa ashe ya dawo gidansa, na fito gida xan je mall yanxu na gansa a mota shi ma” Mami tace “Toh, ni ban san me yasa ya koma Abuja da xama ba yanxu, sai mu yi wata ma ba mu gansa ba, idan nayi magana yace aiki” Hajiya Rukayya ta d’an yi shiru kafin tace “Amma yyi aure ne Hajiya Khadijah?” Mami tace “Ina fa, ba na gaya maki abinda yayi ma yarinyar nan da yake nema jiddah ba, da suka fisa iskanci ai mayar masa da kayansa suka yi, kinsan halin Abbansu, to in gaya maki bai taking Wani action ba sai ma cewa da yyi ai bai isa aure ba, kinga yayi supporting dinsa kenan, ni dai nasan in har yarinyar nan yaudararta yyi hakkinta baxai bar sa ba” Hajiya Rukayya tace “Ikon Allah, to ni kuma da wata na gansa da yara har biyu a mota, da na tambayesa aure yyi sai ce min yyi matar abokin sa ce ai xai maida ta gida, to mutum ba iyali me matar abokin sa taje yi gidansa, and the way he replied, gaskiya it’s suspicious, to da yake kinsan ai bbu nisa tsakanin gidan nasa da namu, in gaya maki na taka da kafa har na isa gidan na kwankwasa gate sai ga wata da alamar dai yar aiki ce ta fito, da na tambayeta mai gidan sai ce min tayi ya fita da familyn sa yanxu, abun dubawa a nan shine anya Hajiya Khadijah ba aure Aliyu ya xo yyi a Abuja ba tare da sanin ku ba, yaran fa yan watanni ne” tun da ta fara xancen Mami ke saurarata baki sake, can Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tana share xufar da ya keto mata tace “Hajiya Rukayya yaushe kika ce xa ki koma?” Hajiya Rukayya tace “Ranan talata in sha Allah” Mami tace “Toh gobe da sassafe xan taho Abujan, ina shiga xan kira ki don Allah” Hajiya Rukayya tace “A’a ke kuwa a bi komai a sannu mana, ko ni ba sai in je in samesa ba, idan ba haka xancen yake ba fa? kuma ace da gasken matar abokin sa ce, ke dai kawai ki bar komai a hannuna xan same sa da kaina sai kace ba d’a na ba Hajiya” Mami ta girgixa kai tace “Inaa ai dole ne kawai in taho Hajiya Rukayya, dama kusan shekara daya kenan da Aliyu ya canxa hali totally ya dawo kamar mara gaskiya tun bai bar Damaturu ba, kar ki ce masa komai ki jira sai na xo, idan ma haka ne idan ma ba haka bane duk xa mu sani, nagode sosai Hajiya, sai kin ji ni” daga haka Mami ta katse wayar ta mike tana jin xuciyarta na tafarfasa, mace da yara? Ina ya samo su? Wani murmushi tayi ta fita daga dakin. Shopping sudais yyi ma twins din na abubuwan da suke ci tun daga kan golden morn, biscuits, custards, quaker oats, chocolates da sweets, sai Pampers da turaren yara, ita dai Khadijah na rike da little sudais dake kuka baya son ta dauke sa sai mika ma Sudais hannu yake, shureim kuwa sai kara kankame Sudais yake wai kar Khadijah ta karbesa shi ma, Duk little sudais ya cika shopping mall din da kuka, Sudais yace “Yanxu meye amfanin haka yaron ki baya son ki daukesa Amira?” Ita dai bata ce komai ba yace “Amira, are you thinking xa mu dauwama tare ne na har abada ne? Of course no, yaran nan ne dolen ki they are now ur new world, show them love Amira” mika mata trolleyn yyi ya karbi yaron ba shiri yyi tsit yana leko uwar tasa, duk yanda sudais yyi da ita ta dauki abinda take bukata a mall din kin daukan komai tayi, ya siya masu ice cream sannan suka bar mall din, har suka koma gida Khadijah ta ki cewa komai, yana gama parking nanny ta fito ta dau yaran gaba daya ta wuce ciki, juyawa yyi ya kalli khadijah da ta bude mota xata fita yace “Wait” sannan ya fito ya shiga back seat din motar ya rufe yana kallonta, hade kai tayi gwiwa tana shesshekar kuka, ya dago kanta a hankali yace “Daga na gaya maki gaskiya Amira?” Hawaye na sakko mata cikin rawar murya tace “Toh nice nace su dinga tsoro na?” Murmushi yyi yana kallon kwayar idonta yace “Ehh mana, ai ke ce baki sonsu, kalli fa ko breast baki basu ba kin yi xaton sun manta ne” turo baki tayi ta dauke kai tace “Amma sun san na basu sau daya ai” dariya ta basa ya dinga kallonta kafin yyi murmushi, ya kamo hannunta ya lumshe ido yace “In dai kina jin maganata, and i meant a lot to you, daga yau ki fara son yaran nan Amira” sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ganin yanda yake murxa mata hannu a hankali ta kwace hannunta ta koma daya side din ta bude motar ta fita, fitowa yyi shi ma ya bi bayanta. Kasa bacci daren ranan sudais yyi ya rasa dalili, duk ya ji he is restless, bayan ya gama sallolinsa misalin karfe biyu ya bude kofar dakinsa ya fito, khadijah dake xaune daki ita ma idonta biyu ta ajiye takardar hannunta da sauri karkashin pillow tana kallon kofar dakin, jin ba a bude ba ta sauka kan gado ta dau hijab ta daura kan sleeping wear din jikinta sannan ta bude kofa ta fita, downstairs ta sauka, tsaye ta gansa tsakiyar parlorn, jin ana sakkowa stairs ya juya da sauri, har ta isa inda yake kallonta yake, yace “Why are you awake by this time” ta girgixa masa kai kawai, xaunawa yyi kan kujera ta xauna kasa kusa da shi, jin bai ce komai ba murya can kasa tace “Daxu a shopping mall kace min we are not going to be together forever, why?” Muryarta na rawa ta karashe maganar, ido ya tsura mata, hawaye ya shiga sakkowa idonta, da sauri yace “Kuka kuma, I didn’t mean it Amira, abinda nake nufi shine….” Sai kuma yyi shiru, ta hade kanta da kujera tana kuka cikin raunin murya tace “Don Allah kar kace xaka bar ni watarana, I have nobody, just you, kai kadai gare ni yanxu, idan ka bar ni ya xan yi, who will take care of the boys” jikinsa yyi mugun sanyi ya sakko kasa yana kallonta ya dago kanta, cikin sanyin murya yace “Ban ce xan bar ku ba Amira, what I mean is death, kinsan rayuwar ba shi da tabbas” xaro ido tayi tana kallonsa ko kiftawa babu sai kuma ta kara fashewa da matsanancin kuka tace “Mutuwa xaka yi ka bar ni?” Dariya ta basa sosai, yace “Ni bance xan mutu ba, kuma idan mutum ya mutu ai lkcn sa ne yyi” rike hannunsa tayi hawaye na sakko mata tace “Baxa ka mutu ba until Allah is pleased with your soul in sha Allah” murmushi yayi yace “In sha Allah, kamar yanda ke ma baxa ki mutu ki bar ni da yaran ba” shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali tace “Gwara su su mutu ai” lkci daya mood dinsa ya canxa yana kallonta, ta sunkuyar da kai, da mamaki yace “Ashe baki da hankali Amira” a hankli tace “Kayi hakuri” rasa ma abinda xai ce mata yyi, can yace “Toh tafi ki kwanta” tace “Toh kai fah” yace “Bana jin bacci” tace “Nima” hade rai yyi yace “Tashi ki tafi nace” kamar xata yi kuka tace “Kai ma ka tashi” murmushi yyi ya mike ita ma ta tashi, yana kallonta yace “to mu je” ita ta fara tafiya sannan ya bi bayanta ta jira ya shiga dakinsa sannan ita ma ta shiga, daga masa hannu ta yi, yyi murmushi ya rufe kofarsa, ita ma ta rufe nata, kwanciya yyi ya rasa tunanin da xai yi a kan Khadijah, is it that…. He love her or what” lumshe ido yyi bai son tunanin daga haka bacci ya daukesa. Da asuba tun da ya dawo masallaci gabansa ke faduwa, he don’t knw why, har gari ya waye yana kwance idonsa biyu a bedroom dinsa, kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune da sauri, jiya da yamma Hajiya Rukayya… Tunanin da ya xo masa kai knn, ya dafe kansa a xuciyarsa yace to sai ta fara gaya ma Mami ta gansa da mace da yara, noo yasan she won’t, but it’s better su d’an bar anguwar for sometimes, da kyar ya mike daga karshe ya fita dakin ya shiga na twins har nanny ta masu wanka tana basu golden morn suna xaune cikin kekensu, suna ganinsa suka fara daga hannu ya daukesa takwaransa har da kuka, karasawa yyi ya daukesu gaba daya yana murmushi Sanin kuka xa su yi idan ya fita ya bar su, ya koma dakinsa da su, yana son fita misalin sha daya amma yan biyun sun ki bacci, bell ya ji aka danna downstairs, sai da gabansa ya fadi duk da bai san me yasa ba, ya mike xai fita twins suka fara kuka, dawowa yyi ya daukesu ya fita, ganin khadijah bakin kofar xata bude yasa shi tsayawa kan stairs, tun da yake bai taba jin faduwar gaban da yaji a lkcn ba ganin Mami ta shigo parlorn Hajiya Rukayya na biye da ita a baya.