Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Direct office din Dr Abdul khaleel ya wuce, ya samesa xaune yana aiki, ganin khaleel ya bar abinda yake yi yace “He is improving ko Dr” khaleel bai tanka sa ba isa gabansa ya dafa table yana kallonsa bbu yabo bbu fallasa yace “Dr Aliyu…. Where is his home?” Dr Abdul yace “Aliyu? Ba yana office ba?” Khaleel yace “Baya nan” da mamaki Abdul yace “Hope babu matsala dai?” A takaice Khaleel yace “Babu, ina gidansu yake” Abdul yace “Toh, he is not the type that mingle gaskiya I dont knw his home” juyawa Khaleel yyi ya fice office din, direct parking space ya nufa ya hau motarsa ya wuce gidan Farouq. Umma ta dinga kwantar ma khadijah hankali duk da taki saurarenta, daga karshe Umma ta fita ta biya bill dinsu don bata ga amfanin xaman asibitin ba, na khadijah kadai suka karba ban da na sudais kamar yanda Aliyu yyi instructing din su, da kafa suka fita asibitin don Umma bata xo da mota ba, suna isa bakin titi ta tsayar masu da abun hawa suka wuce gida. Girgixa kai Farouq yyi yana kallon Khaleel yace “Ni fa ba ruwana, kamar yanda na ki ba sa address din ka, to kai ma baxan baka address din sa ba gaskiya, ku kuka san abinda ya hada ku can..” Wani kallo khaleel ke masa kafin ya mike ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce, yana driving ya dau wayarsa ya fara kiran Khadijah, har ya katse bata dauka ba, nan ko tana zaune ita kadai daki tayi kukan har ta ji ba dadi, Umma kuma na parlor da Nanny sun yi jigum, Umma ta rasa ta ina xata fara yanxu ta ina xa su fara xuwa neman yara, Jin wayar ya sake ring Khadijah ta daga da kyar ta kai kunne, jin muryar ta jikin khaleel yyi sanyi, a hankali yace “Plss ki kwantar da hankalin ki Khadijah, xa a amsar maki kids din ki, he have no right over them, in sha Allah we will get back ur kids” kasa cewa komai tayi tana share hawayen da ke xubo mata, yace “Kin san address din can gidansu?” Shiru tayi kafin ta girgixa kai cikin sanyin murya tace “Na manta” yace “Amma xa ki gane gidan?” Nan ma ta d’an yi shiru, anya xata gane gidan yanxu kuwa, murya can kasa yace “Khadijah?” Tace “Kilan in gane” yace “Good, kuna clinic din har yanxu?” Ta girgixa kai tace “Mun dawo gida” yace “Toh xan taho yanxu, but promise me baxa ki sake kuka ba plss” a hankali tace “Toh baxan yi ba” yace “Good, ina tahowa yanxu” daga haka ya katse wayar, Sosai Khadijah ta ji hankalinta ya kwanta, ta ji ta samu natsuwa. Tun da Aliyu ya shiga dakinsa bai sake fitowa ba, Mumy da maganganun Anty khadijah suka fara sa mata ciwon kai ta daga kai tana kallonta a karo na farko tun shigowarta dakin, ban da kumfar baki kamar wata xararriya babu abinda take tana nuna yan biyun dake xaune kan gadon Mumy, suma yaran kallonta kawai suke a tsorace, Baby ma na tsaye sai hararan Anty khadijah take tana tabe baki, Mumy ta dakatar da ita a tsawace tace “Khadijah ki fita ki ban waje don Allah ki bar ni in ji da guda daya, ciwon kai kike kara min ki fita don Allah, ko makaho ya shafa yaran nan yasan na waye, Baxa ayi DNA din ba….” Anty khadijah da idanuwanta suka kankance da mugun mamaki tace “Anty fati ni kike cewa in fita in baki waje don ina nuna damuwa ta kan shegun da aka makala ma Aliyu aka ce nasa ne, Ni Anty fati??” Mumy tace “Ehh ki fita nace” tayi wani murmushi tace “Xan fita yanxu kuwa” daga haka ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Mumy ta kalli yan biyun dake bata tausayi har ranta, a hankali tace “Me xa ku ci?” Sudais dai bai ce komai ba, Shureim ya girgixa mata kai shi ma bai ce komai ba, karasowa tayi ta xauna gun yaran tana kallonsu, wani sonsu take ji a xuciyarta, ta d’an yi murmushi tace “Ayi maku noodles and egg?” komawa Sudais yyi ya kwanta ta kai hannu jikinsa taji xafi sosai, kallon baby tayi tace “Xaxxabi ne jikinsa fa sosai…” Baby ta karaso ita ma ta taba yaron taji xafin jikin ta kalli Mumy tace “Mumy ko in kira yaya?” Mumy tace “Kira sa” juyawa tayi ta fita, ita ta fara dawowa dakin sannan Aliyu ma ya shigo, kallon yaron yake har ya isa kan gadon ya taba jikinsa, dago sa yyi ya xaunar da shi, yana kallonsa yace “Are you feeling pain anywhere?” Sudais ya nuna masa kan sa, kamar xai yi kuka yace “I want to go to my Anty plss” Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace “Ohk I will take you there” Mumy dake kallon Aliyu tace “Ina ita khadijahr take?” Kamar Aliyu baxae ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa murya can kasa yace “Bayan ta bani su tayi tafiyarta” wani kallo Mumy ke masa ganin yanda yyi maganar, can ta girgixa kai tace “Karya kake…” Da sauri ya kalleta, sai kuma ya marairaice yace “Mumy bata sani ba na taho da su, idan ta sani baxa ta bani su ba” Bude baki Mumy tayi tana kallonsa, da damuwa tace “Me yasa xaka yi haka Aliyu, me yasa xaka raba su da uwar su….” Kasa cewa komai yayi, Mumy da duk jikinta ya kara yin sanyi tace “Aliyu tell me how everything happened, garin yaya kayi ma yar mutane haka, where was I that day? kar ka boye min komai plss, tell me the truth….” kallon Mumy Kawai yake ko kiftawa babu, can ya xauna gefen gado ya rike kansa yana jin kamar ya fara mata hawaye, bai son tuna mummunar ranan nan a rayuwarsa, Mumy na kallon Baby tace “Baby xo ki tafi da su ki dafa masu indomie ki basu, shi wannan ki kai sa dakin ki ya kwanta” Baby ta karaso ta sakko da boys din daga kan gado ta wuce da su dakinta, Mumy na kallonsa tace “Ina ji Aliyu” Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali ya fara magana, “Mumy ni dai nasan I woke up fine that very day….” Ya d’an yi shiru, nan ya fara ba ma Mumy labarin abinda ya faru ranan bai boye mata komai ba har yanda bayan kwana biyu ya ba ma khadijah kudi me yawa yace ta wuce gun ummarta, hawaye kawai Mumy ke yi tana kallonsa a sanyaye, bai iya ya dago kai ba shi ma hawayen na sakko masa cike da karfin hali yace “Mumy nayi abinda nayi ne out of confusion, I was confused, ban taba xaton xan aikata ma khadijah haka ba, bayan tafiyar ta ku shaida ne, nayi bankwana da kwanciyar hankali da farin ciki na, I never had rest of mind again kuma na kasa gaya maki abinda ya faru ban san ya xa ki dau xancen ba, shi yasa a ko da yaushe nake ce maki ki taya ni da addu’a, wani lkcn idan na kwanta bacci ita kawai nake gani, kuma it’s not as if nasan da cikin bane, kawai ni dai nasan ban kyauta mata ba saboda marainiya ce bata da kowa, ban san ta Inda xan fara nemanta ba don ban san kowa nata ba, da babu abinda xai hanani nemanta Mumy, idan baki manta ba akwai wani lkci da na taba tambayar ki ko kina da number warce ta kawo ta kika ce baki da shi, ni ban sa ko Khadijah xata yafe min ba and it looks as if I don’t deserve that…. Amma abinda ke bani mamaki har yanxu shine yanda aka yi Anty khadijah ta san abinda ya faru bayan bata gidan kuma ita ta fita tare da su baby a ranan, gidan ya rage daga ni sai Khadijah, sai kuma jiya tana waya a bathroom din dakinta, I overheard all what she was saying on the phone…. Nan ya gaya ma Mumy duk abinda ya ji Anty khadijah ke fada a waya jiya, yana girgixa kai yace “We shud keep on pretending mum, she was so shock da ta gan ni a dakin, but i pretend ban ji komai ba, hakan kuma ya sa hankalinta ya kwanta, a sannu abinda take yi xai bayyana a fili tun da ba mu da hakkinta, kuma ina mai tabbatar maki soon komai xai bayyana, ke dai kawai ki ci gaba da sa mata ido, xan dai sa su Sanusi su tone bayan gidan to check what she was talking about on phone” Mumy ta dinga kallonsa ko kiftawa babu cike da shock, ya goge idonsa har lkcn bai kalleta ba yace “And… Mumy kilan idan ke kika yi ma khadijah magana xata iya yafe min, ni ta ki saurarata har yanxu, kuma mumy plss kar ki ce min baxan iya aurenta ba, hakan kadai ne xan iya mata in wanke kaina, I knw I can’t pay her all what she passed through, kar ki hana ni aurenta mumy…” Mumy ta sauke ajiyar xuciya har lkcn tana mamakin abinda Aliyu ya fadi mata kan Anty khadijah, she is still finding it hard to believe that, infact bata ma yarda bane tasan Anty khadijah baxata yi abinda Aliyu ke fadi ba, Aliyu yace “Mumy kinyi shiru” Mumy ta kallesa ta kara sauke ajiyar xuciya sannan tace “Idan kuma ita bata son ka fa?” Ya d’an hade rai yace “Toh sai ta bar min yarana taje tayi aurenta shikenan na raba ta da wahala, idan kuma ta yarda ta aureni sai mu xauna mu rike yaranmu, domin kuwa su din abun kyama ne idan ta kai su wani gidan, ko ba yanxu ba wataran xa a kyamace su, to idan muna tare fa? We can never do that to them” Mumy bata kuma cewa komai ba tayi nisa tunanin da take na Anty khadijah, Bude kofar dakin Anty khadijah tayi ta shigo tana kallon Mumy da kumburarrun idonta da ta sha kukan takaici, kallo daya Mumy ta mata ta dauke kai xuciyarta na kara karyata Aliyu, Aliyu kam bai ma kalli inda take ba, tana kallon Mumy tace “Ina son sanin matsayin auren iklima a gidan nan Anty fati, na hada kayana idan Ita ma in hada nata ne toh…” Sai a sannan Aliyu ya kalleta yace “Anty aure ya taba mutuwa ba ayi saki ba?” Hararansa tayi ta juya ta fita, dakin baby ta bude ta dinga kallon yaran dake kan gadon cike da tsana, a tsorace suke kallonta su ma, can ta juya ta fita dakin ta sauka downstairs xuciyar ta na tafarfasa, Baby ce kitchen tana bare eggs da ta dafa masu indomien na kan wuta, Anty khadijah ce ta shigo kitchen din ta dau cup ta xuba ruwan xafi daga flask, Baby ta kalleta ganin yanda ta tsaya tana tunani, da sauri Anty khadijah ta bude gun da madara suke ta fiddo kayan tea ganin kallon da baby ke mata, tana hada shayi tace “Baby ina wani sarka da na baki ki ajiye min ranan da aka yi bikin iklima a gidan nan?” Baby tace “Anty yana cikin jakata a daki” Anty khadijah tace “Je dauko min kayana” Baby tace “Yanxu Anty?” Anty khadijah ta balla mata harara tace “Aa anjima” a sanyaye baby ta juya ta fita kitchen din bayan ta rage gas kar indomien ya kone, Anty khadijah ta fara kalle kallen kitchen din da sauri, lkci daya ta fita waje ta kofar kitchen din ta tafi gun da ake ajiye snipper, Baby har ta fara haura stairs ta d’an tsaya, da sauri ta koma ta rabe jikin bango tana lekan kitchen din ta ga Anty Khadijah bata ciki, har xata juya ta bar wajen sai ga Anty Khadijah da gudu ta dawo kitchen din ta bude abun hannunta ta xuba cikin indomie da ke kan wuta, Xaro ido baby tayi taji kafafuwarta sun kasa daukar ta, lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya da sauri ta haura sama, dakin Mumy ta shiga ta fashe da kuka, Aliyu ya mike yana kallonta yace “Me ya faru?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103Next page

Leave a Reply

Back to top button