Noor-Al-Hayat COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace “Anty are you sleeping?” Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu’ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace “Ka ci abinci?” Ya dago kai yana kallonta yace “Uncle ya bani na ci” Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Hope ban tashe ki bacci ba Amira” ta lumshe ido a sanyaye tace “Ba bacci nake ba” Shiru ya d’an yi na wani lkci kafin yace “Gaya min me ya faru, what’s wrong with you” Ta bude ido da sauri cike da mamaki tace “A’a ba komai, am just tired, me ka ga?” Sudais ya girgixa kai yace “Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years, from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss” Tace “Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa” D’an murmushi yayi yace “Ohk then” trying to brighten up tace “Ya Namecy na fa?” Yace “Ga ta tayi bacci” Khadijah tace “Toh a shafa min kanta” Sudais yace “Alryt, Shureim yayi bacci?” Khadijah ta gyada kai tace “Uhm” yace “Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa” A hankali Khadijah tace “Ai ya fara ma” Yace “School din?” Tace “Ehh” yace “Shine baki fadi min ba Amira?” Ta langwabar da kai tace “Kayi hakuri” yace “Ke kika sa shi schl din” ta girgixa kai tace “Dr Ayman ya sa shi” Sudais ya d’an yi shiru sannan yace “That’s nyc” Khadijah tace “Next week din xaka taho?” Yace “Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?” tace “A’a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya” yace “Ameen, let me leave you dear, it’s late and kilan xa ki lectures gobe koh?” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu’a sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe kofarta Shureim yace “Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?” Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace “He is still sleeping dear” daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe, Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace “Iman” kasa kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace “Gida xa ki wuce?” Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a hankali yace “What’s wrong Iman?” bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace “Subhanallah, me ya faru Iman, plss ki gaya min, wani abu ya faru ne” ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa yace “Plss I don’t like this Iman, ki daina wannan kukan” Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya dago, cikin sanyin murya yace “What happened Khadijah?” Ta hadiye abu da kyar tace “Should I confide in you plss?” Kallonta yake ko kiftawa babu, a hankali yace “Sure Iman, you won’t regret doing so” Ta gyada kai cikin sanyi tace “Ohk, tnx” Shiru ne ya biyo baya na ‘ya dakiku…..
????Seriously I don’t like this short chapters da nake yi yanxu wllh, but dai ya fi babu d’an agwai da bak’in d’a….????
Gobe xa ku samu 5 read more????
Khadijah ta hade kanta da gwiwa a hankali ta ki cewa komai, ya fi minti biyu yana kallonta, can ya shafa kansa murya can kasa yace “Talk Iman…” lkci daya ta dago kanta ya dinga kallon jajayen idanuwanta, ta hadiye abu da kyar ta make kafada tace “I think I’ve changed my mind” muryar ta na rawa ta fadi haka, ya dinga kallonta a sanyaye yace “Why Iman??” k’in cewa komai tayi, wasu sabbin hawayen suka shiga xubo mata, da damuwa sosai yace “Why did u change ur mind Iman, am I not trustworthy” goge idonta tayi tana kallonsa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanuwansa, murya can kasa ya ji tace “Ina son xan wuce gida yanxu” Ya bude ido ya kalli agogon wrist dinsa a sanyaye yace “To mu je in kai ki” shi ya fara mikewa sannan ita ma ta tashi a hankali tana share idonta, har suka iso gun motarsa bai ce komai ba, sai da ya bude motar ya shiga sannan ita ma ta shiga, gaba daya she was absent-minded during the ride, idonta ne ya sauka kan wani karamin agogo mai kyau na yara cikin a cikin motar, ta kai hannu ta dauka tana kallon agogon ko kiftawa babu, agogon da khaleel ya taba siya ma su Shureim ne lkcn da suka xo hutu wajenta da xa su koma, ita dai ta san na Shureim na nan don da shi ma suka xo, Aliyu dai bai ce komai ba yana driving a nutse, ganin ta kallesa kafin tace komai murya can kasa yace “For little Aliyu….” Kasa cewa komai tayi da farko, a sanyaye tace “Where did you get it from?” Ya d’an yi murmushi kamar baxai ce komai ba shi ma, sai kuma yace “When he had an accident that very day agogon na aljihunsa, da muka tafi asibiti na cire” Khadijah ta sauke idonta bata ce komai ba, a hankali ta xuge zip din jakarta xata sa a ciki ya karba a hannunta, da mamaki take kallonsa, yace “Nima ina so, shi yasa na bar shi ma a mota” ta hade rai tace “Toh nima ai ina so” A hankali yace “But ai Shureim ma na da shi” bata sake saurarensa ba ta kai hannu xata karbe, bai san lkcn da ya sake steering ba ta fasa ihu a tsorace, parking yayi daga karshe inda ya dace yayi, ta dinga kallonsa xuciyarta na bugawa, yayi kokarin ganin bai yi dariya ba, dauke hannunsa yyi wajen ganin xata kwace agogon, Tace “Bana so ka bani abun yarona” a hankali yace “Nima ai yarona ne Iman” wani kallo tayi masa tace “A tunanin ka??” Murmushi kawai yayi yana kara kallon agogon, Mika mata yayi yana kallonta a hankali yace “Toh na hakura” kasa amsa tayi, ya dinga kallonta yana mika mata, dauke kai tayi ta turo baki tace “Toh na ara maka, xaka ban watarana” Murmushin sa yayi mai kyau murya can kasa yace “Toh ina godiya Iman” Ya mayar da agogon inda yake ya ajiye, ya juya yana facing dinta yace “But why did you change ur mind Iman?” kallonsa tayi sai kuma ta dauke kai, kamar baxata ce komai ba bayan few minutes a sanyaye tace “It’s Dr Ayman, and it looks as if it’s of no use telling you….” sai da gabansa ya fadi sosai, ya dake cike da karfin hali yace “What about him” ta jinginar da kanta da kujerar da take xaune, ji tayi abun ya dawo mata sabo, muryar ta na rawa tace “Kawai don nayi masa magana shine ya min walakanci” Aliyu ya ji komai nasa ya tsaya, a hankali yace “May be…. may be he misunderstood you Iman….” Ta fashe da kuka tuna abinda Dr Khaleel yace mata, ya lumshe ido ya bude yace “Toh wani maganr kika masa?” Babu abinda ta boye masa a maganarsu da khaleel na jiya, jin yanda take kuka Aliyu ya lumshe ido yace “Look…. pls ki daina wanann kukan I really don’t like it, stop it now” a fusace yayi maganan ta hadiye kukan da take tana goge idonta, ya jinginar da kansa jikin kujerar motar a hankali cikin sanyi yace “He really misunderstood you, but ke ma ba haka ya kamata ki gaya masa ba” ta kallesa tace “Toh ya xan ce masa?” Ya d’an yi murmushin karfin hali yace “You where direct, which is not suppose to be so” turo baki tayi ta rungume hannunta tace “Ae shikenan” Aliyu ya shafa kai murya can kasa yace “You want me to talk to him?” Ta buda ido sosai tana kallonsa da sauri tace “Kace masa me?” Ba tare da ya kalleta ba yace “I will only explain to him what you meant by wat u said to him, kila…” ta hade rai ta katse sa tace “Noo, you don’t need to, ba ruwana da shi, and am wishing him d best also” Aliyu na kallonta da kyau yace “Then forget him, kuma kar ki sake xubda hawayen ki” Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace “But I can’t forget him just like that, yayi min hallacci a rayuwa” ba tare da Aliyu ya kalleta ba yace “Me ya maki?” Hararansa tayi da kamar baxata ce komai ba, sai kuma a takaice tace “He nursed my Heartache, he always made sure I was fine” Kallonta kawai Aliyu yake, “Wani irin heartache?” Tambayar da ya mata kenan har sannan yana kallonta sauke idonta tayi daga karshe tace “Ciwon xuciyata” da wani expression yake kallonta kafin yace “Kina nufin kina da ciwon xuciya?” Shiru tayi bata ce komai ba, jin hawayen talaici na xubo mata ta shiga gogewa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, cike da karfin hali yace “I… i am the cause ko Iman?” Taki cewa komai, jin taki magana yace “Iman” sai a sannan ta juya tana kallonsa, sai ya rasa ma mai xai ce mata duk jikinsa ya mutu, tada motar sa yyi cike da karfin hali yace “Let me get you something to eat” Bata ce komai ba ya nufi wani gidan cin abinci da ita, suna isa bayan yayi parking ya juya yana kallonta a hankali yace “Mu je” daga haka ya bude motar ya fita ita ma ta fito, one side of the eatry khaleel ne xaune da cup din coffee gabansa ya jinginar da kansa da kujera har coffeen ya gama hucewa bai fara sha ba, kallonsu ya dinga yi ko kiftawa babu, ganin kujerar dake kallon nasa xa su zauna ya juya masu baya, Aliyu ya mika mata order list din da aka basa, kamar baxa ta karba ba da farko sai kuma ta amsa, ya dinga kallonta tunani iri iri a xuciyarsa, bata yi second talatin tana kallo ba ta mayar masa a sanyaye tace “Just anything” ya karba yana gyada mata kai, abinci iri daya ya sa aka kawo masu, duk da gaba daya ya ji ba ya da appetite hakan bai hanasa dinga cin abincin a hankali ba, ita ma haka, gaba daya suka fada duniyar tunani kowa da wanda yake, ita tana ganin yan biyunta tare da shi barin late Sudais, kuma ta dalilin haka har ranta tasan she is now comfortable with him even if it’s not 100% unlike before, shi kuma yana tunanin in har bai auri Khadijah ba till the end of him baxai taba samun rest of mind ba, a hankali ya dago daga karshe yana kallon yanda take cin abincin kamar ana tilastata sai turo baki take, suka hada ido ta yi saurin sauke idonta, ya d’an yi murmushi yace “Naga bakya ci” a hankali tace “Ina ci mana” shi ya fara matsar da abincin gabansa jin ya ishesa gaba daya duk da ba da yawa ya ci ba, ta kalli abincin nasa tace “Ka koshi?” Ya gyada mata kai, yanda yayi da bakinsa kamar Shureim idon bai son cin abinci, tayi shiru tana kallonsa, yayi murmushi yana shafa kansa ya matsar mata da sauran abincin nasa yace “Ko xaki kara?” Wani Harara ta maka masa ta tura masa nata tace “Sai dai ma ka kara da nawa” sunkuyar da kansa yayi yana dariya, tayi murmushi a sanyaye tana kallonsa komai yayi wani lkcn sai ta ga exactly her kids, it’s just too obvious, ya dau tissue yana goge bakinsa a hankali yace “Ranan Aunt dita ke tambayar ki, coz I told her a nan kike karatu….” Khadijah ta sauke idonta kasa tace “Ina gaisheta” lumshe ido yyi ya bude yace “Or xa ki je ku gaisa yanxu, tana son ki sosai, anjima sae in mayar da ke gida then u face Ur Dr Ayman…. Sai ki masa bayanin abinda kike nufi ya daina fushi da ke” ta hade rai tace “Ni ba ruwana da shi, bana son sa kuma” tana fadin haka ta kife kanta da table ta fara rera kuka, Aliyu ya dinga kallonta ko kiftawa babu, can yyi kasa da murya yace “Toh kiyi hakuri kar ki sake kuka, am sure shi ma ba har ransa ya gaya maki haka ba fa” Bata sake cewa komai ba ya biya bill din yana kallonta yace “Tashi mu je” mikewa tayi ya mike shi ma, tana gaba yana biye da ita Dr Ayman ya bi su da kallo har suka fita, har suka iso gun motarsa bbu wanda yace komai, ya bude mata motar yana kallonta, a hankali ta karaso ta shiga, ya rufe sannan ya xaga ya shiga ya tada motar ya fita eatry din, sae da suka hau saman titi a hankali yace “Mu je ku gaisa da ita Iman?” Shiru tayi da farko kafin murya can kasa tace “Toh” yayi murmushi yace “Thanks Ummu Shureim” har suka iso gidan babu wanda yace komai cikin su, yanxu kam ta daina jin xugin da take ji a xuciyarta, yayi parking yana kallonta yace “Toh fito” ba musu ta fita shima ya fita, Yana gaba tana biye da shi har suka shiga parlorn gidan. Maryam kadai ce parlor tana rubutu a takarda, ganinsu ta mike da mamaki tace “Lahh Khadijah ce gidanmu yau, sannu da xuwa” Khadijah ta xauna tana kirkiran murmushi da kyar tace “Yauwa nagode” Aliyu ya wuce sama, Maryam ta bi sa da kallo, kamar yanda Khadijah ke kallonta, tashi tayi daga karshe ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye gabanta tana tambayarta Shureim, a hankali Khadijah tace “Yana schl” Maryam ta xauna tace “Ayya, kin shiga schl kuwa yau?” Khadijah ta gyada kai tace “Daga can nake” Maryam tace “Nima kin ga yanxu na dawo, nama yi ta jiran ya Aliyun don ya ce min xae shigo shi ma amma ban gansa ba….” Fitowar Hajiya Mariya ya sa Maryam ta mike tace “Anty yau ga mum Shureim gidan mu” Da murna Hajiya Mariya ta karaso cikin parlorn tace “Wlh kuwa, maa Sha Allah, sannu da xuwa Khadijah” Khadijah ta sunkuyar da kanta da ladabi tace “Nagode mumy, Ina yini?” Hajiya Mariya tace “Lafiya lau Khadijah ya gidan?” Tace “Alhmdllh” Hajiya Mariya tace “Ya karatun fa?” Khadijah tana wasa da xobenta tace “Alhmdllh Mumy” Hajiya Mariya tace “Maa Sha Allah, Allahu ya baku sa’a, Ina Shureim din?” Aliyu da ya shigo parlorn yace “Yana schl Anty” tace “Allah sarki, ashe ya fara schl din a nan, Allah yayi masa albarka ya raya sa” Mikewa tayi daga haka tace “Mu je sama kiyi sallah ki ci abinci koh” kasa cewa komai Khadijah tayi ganin ta fara tafiya ta mike ta bi bayanta a sanyaye suka haura sama, Maryam na kallon Aliyu tace “Yaya shine ka shanya ni schl koh?” Ya shafa beard dinsa bai ce komai ba, Khadijah na haurawa sama tare da Mumy ta juya tana kallonsu, suna hada ido da Aliyu tayi saurin dauke kanta ta shiga dakin da Mumy ta shiga. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh Maryam ta shigo dakin rike da tray na abinci ta ajiye mata tace “Ga abinci Khadijah” Khadijah ta xaro ido tace “Wallahi na ci abinci kafin mu xo nan am not hungry” Maryam tace “Toh ko kadan ne dai ki ci” Khadijah xata yi magana aka bude kofar, jawahir ce ta fara shigowa, suna hada ido Khadijah ta sunkuyar da kai, Jawahir dake ta kallonta ta ajiye jakar hannunta ta fice daga dakin, sosai jikin Maryam yayi, ita dai Khadijah bata sake dago kanta ba, sai ga deejah ma ta shigo dakin, ta wara ido ganin Khadijah tace “Wow Khadijah ke ce gidan yau?” Murmushi Khadijah tayi tace “Ina yini” Deejah tace “Lafiya lau, ya lectures? Tare da Maryam ku ka xo?” Maryam na yar dariya tace “Ehh mana” Deejah tace “Ayya ya little shureim” Khadijah tace “Yana schl” Deejah tace “Toh maa Sha Allah” daga haka ta fita, Khadijah ta kalli agogon dakin don gaba daya hankalin ta yyi kan yaronta sanin ya kusa tashi a schl, ganin Maryam na sllh ta jira har ta idar kafin tace mata tayi ma Mumy magana xata wuce, Deejah ce ta dawo dakin tana video call ta iso kusa da Khadijah ta durkusa tana murmushi ta haska ta tace “Ammi ki duba fa plss basa kama??” Khadijah ta ki kallon screen din tana murmushi, Deejah tace “Khadijah ki tsaya ku gaisa da Ummar mu pls” sai a sannan Khadijah ta kalli screen din wayar, wata matashiyar mata ta gani gaban wayar, a hankali tana kallonta tace “ina yini?” Matar na kallon ta da fara’a tace “Lafiya lau yan mata, ya kike ya karatu?” Khadijah tayi murmushi tace “Alhmdllh” matar tace “Maa Sha Allah, Allah yayi maku Albarka ya bada abinda aka je nema, sai ayi ta kula kin ji?” Khadijah ta ji dadin addu’ar cikin sanyin murya tace “Ameen mama nagode” matar tayi mata sallama, Deejah ta mike rike da wayar tace “Ammi idan Safeenah ta dawo plss ku kira ni in nuna mata duplicate din ta” murmushi kawai Khadijah tayi, Deejah ta fice daga dakin tana ci gaba da waya da mum dinta. Khadijah ta kalli Maryam dake kallonta tace “Kice ma Mumy xan wuce” mikewa Maryam tayi tace “Toh” daga haka ta fita, tare suka dawo dakin da Mumy tace “Har xa ki koma daughter?” Khadijah tayi murmushi tace “Eh mum, Shureim sun tashi a schl” Hajiya Mariya tace “To maa Sha Allah, mun gode da ziyara Khadijah, Allah yi albarka” a tare suka sakko kasa har da Maryam, Mumy ta ba Khadijah sako a leda ta kai ma Shureim, a kunyace ta amsa tace “Allah saka da alkhairi mum” Deejah vata ji dadi ba ganin wucewa Khadijah xata yi, tace “Ae ko xan xo gidan ki ko gobe” Yar dariya Khadijah tayi tace “Allah ya kai mu” tare da Maryam suka rakota har bakin motar Aliyu don yana cikin motar yana jiranta, daga masu hannu tayi bayan ta shiga tace “Toh nagode, sae anjiman mu” Aliyu ya ja motar ya fita cikin gidan, sae da suka dau hanya tace “Xan dau Shureim a schl” yace “I thought as much, naga it’s time” Mamaki Khadijah tayi ganin ya dau hanyar makarantar, ta kasa daurewa tace “How did you knw d schl?” D’an murmushi yayi murya can kasa yace “Kin raina irin bond dake tsakanin a son and his father?” Shiru Khadijah tayi tana kallonsa, lkci daya ta hade rai ta turo baki tace “Don’t call him ur son, stop calling him that” kallonta yyi, A hankali yace “Ko saboda me?” A takaice tace “His father is a barrister” Murmushi yayi bai ce komai ba, he really really don’t want to hurt her da babu abinda xai hanasa tambayar ta ko barrister ne yayi mata cikinsu, suna isa schl din bayan yyi parking ta bude motar ta fita don dauko d’an ta ya bi ta da kallo, ba a dau lkci ba ta dawo a sanyaye, yace “Where is he?” Ta bude motar ta shiga a hankali tace “Dr ya tafi da shi wai”