RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

A cikin minti 15 ta iso wani supper market, cikin haraban tayi packing sai da tayi kusan mintuna goma tana zaune abunta kafin tabuɗe tafito, cikin wani irin tafiya tare da ficchi take takawa tadoshi cikin supper market ɗin, duk wanda ke haraban wajen sai da yaɗaga kai yana kallon ta, ita kuwa batasan ma suna yi ba, tafiya kawai take yi tana wani irin karairaya tare da lumshe idanu tamkar bata ganin gaban ta

Just 10minute taɗauka aciki before tafito riƙe da Ledoji a hannun ta tatunkari motan ta

“Woww wow Nazee ji wata zazzafan Babe sai kace ita tatsara kanta”.

Nazee da yake ƙoƙarin rufe ƙofar mota yajuyo yana kallon RAUDHA, sai kuma yaɗauke kai yana kallon Abokin nasa da ninyan yayi magana but sai shi yariga sa dacewa

“Kai wlh sai naje wajen ta don bazan bari tasuɓuce min ba, kutttt wannan irin su ai muke so Young Killer Babe”.

Har ya soma tafiya Nazee yajawo shi baya

“Kai rufawa kanka asiri wlh, kai baka san ko ƴar wanene ba ko?”

Saddeq dake kallon sa yace “ƴar wanene to? Kaga da Allah sake Ni kar  tatafi”. Yaƙarike maganar yana fizge rigan sa tare da kallon motan RAUDHA da har tasoma tafiya

Nazee saurin cewa yayi “wlh yarinyan M. makamashi ne, gwara ma kadawo kafin ka kwashi wulaƙanci a wajen ta”.

Cak Sadeeq yatsaya yana kallon Nazee yace “Haba dai kana nufin Alh. Mustapha Makamashi?”

“Wlh kuwa itace”. Nazee yasake tabbatar masa

Rufe baki Sadeeq yayi yace “kai wlh nayi tunanin ko irin Babes ɗina ne, wai kana nufin yanzu wannan musulma ce? Ikon Allah lallai kam huuuuu..”

Kasa ma ƙarisa maganar yayi yana sake bin hanyan da kallo da tuni RAUDHA taɓace a wajen, sai kuma yajuyo yana kallon Nazee yace “wlh nayi tunanin ko Christian CE kasan Ni dasu nafi harka coz waɗannan ƴaƴan musulman babu abinda suka iya sai girman kan tsiya”.

Dariya Nazee yafashe dashi kafin yasoma tafiya yana cewa “kai dalla muyi abinda yakawo mu Ni kaga tafiyana”.

Bayan sa Sadeeq yabi yana cewa “Guy Amma fa ta haɗu, duk sanda nasake ganin ta sai nayi mata magana Yasin”.

         ????????????

WUTA kawai take ba ma Motan har ta’isa gida, wani irin hon take dannawa kamar zata tashi sama, dasauri Gateman yabuɗe mata tashigo aguje tanufi Compound ɗin gidan, anan tayi packing tafito takwashi kayan ta tanufi cikin gida, tana buɗe ƙofan parlour’n suka haɗa idanu dashi, tsaye yake ya sanya hannayen sa cikin aljihun wandon sa yana kallon ta, wani irin ƙara tasaki tazubar da ledojin dake hannun ta tanufe shi aguje, tana isowa wajen sa yacafe ta yasoma juyata tana dariya, shima ɗin dariyan yake yi yana faman wulwula ta sai kace ya ɗauki ƙaramar yarinya, sai da yadaɗe yana faman jujjuya ta acikin parlour’n sannan ya’ajiye ta a ƙasa tabiyo jikin sa suka faɗa saman sofa suna ɓaɓɓaka dariya tare da sakin nishi, sake maƙalƙale shi tayi cike da tsananin murna tace

“I’m so surprise Yaya yaushe kadawo?”

Hannun sa yasaka yana shafa fuskarta cikin murmushi yace “Yesterday Baby, mun dawo gaba ɗaya kenan fa”.

Wani irin tsalle tadaka ajikin sa cikin ihun murna tace “dagaske Yaya?”

Still Murmushi yasaki yace “Yes my dear”.

“But anan gidan zaku zauna ko?” Tasake tambayan sa cike da zumuɗi

Girgiza mata kai yayi yana taɓe baki yace “No muna Abuja fa”.

Hannun sa still dake yawo saman fuskarta tayi saurin cafke yatsan sa da baki tana gantsara masa cizo cike da mugunta, ihu yasaki yana janye hannun yace

“Oshhhhhhh Babe Zaki kashe Ni ne da zafi fa?”

Turo bakin ta tayi tana tashi ajikin sa tace “Yaya meyasaka sai acan zaku zauna?”

“Sorry Baby kinsan can nake aiki dole acan ɗin zan zauna, kinga shiyasaka ma nazo naɗauke ki mu koma can tunda nasan zakiyi fushi dani”.

Cikin dashashshiyar muryan ta tace “No Yaya bazan je ba”.

“Why dear?’ yatambaye ta yana kallon ta

“Ni bana son can nafison Nan”.

Riƙo hannun ta yayi still yana kallon ta yace “yanzu Baby kinfi son kizauna anan ke kaɗai? Why baza ki bini mu tafi tare ba? Idan Daddy yadawo I promise you zan dawo dake kinji?”

Juya kanta tasoma yi cike da shagwaɓa tace “Nooo Yaya bazan je ba”.

Kallon ta kawai yake yi cike da tsananin ƙaunar ta da tausayin ta, yasan halin ta idan takafe a abu to dole sai dai kaƙyale ta, be ce komi ba illa sake mata hannu da yayi yasoma tunani, miƙewa ita kuma tayi tana cewa

“Yaya kaci wani abu?”

Bata jira amsar sa ba kuma tasoma kwaɗa ma ƴan aikin ta jira, kankace me sun fito sun gurfana gabanta

“Uban me kuke yi aciki da bazaku Bama Yayana abinci ba?” Tafaɗa cikin ɗaga murya da baya fita, at the same time kuma tana riƙe da ƙugu tana kallon su

Kafin su buɗe baki suyi mata magana Suhaib ya riga su dacewa “come down Baby sun tarbe Ni mana har naci abinci”.

Hakan yasaka tasauke hannun ta a ƙugu tajuyo tana kallon sa yasakar mata murmushi, takowa tayi tazauna kusa dashi, sai Suhaib ne yabasu umarnin tafiya don ita bata sake bi takan su ba, daga nan hira suka soma yi har lokacin sallan asar yayi sannan yatashi yayi alwala a Toilet ɗin dake parlour yafice masjid

Ita kuma wajen kayan ta da tazubar tanufa takwashe tanufi ɗakin ta, tana shiga ta’ajiye kayan tafaɗa Toilet tasoma wanka, har Suhaib yadawo yashigo ɗakin nata but tana cikin Toilet bata fito ba, don haka yajuya yakoma parlour.

.

Please????????

*Share*

*Vote*

*Comments*

[11/13/2020, 2:47 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What’sapp Number 07065334256~

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON THREE*

_______????Tana fitowa tashirya cikin ƙananan kaya farar Vest da farar wando Three qweater, komi bata shafa a fuskarta ba tafice dasauri, da gudu take taka matattaƙalan benen har ta’isa cikin parlour’n taƙarisa wajen Suhaib dake zaune yana kallo, Bin ta da kallo yayi har tazauna kusa dashi kana yace

“Kinyi sallah dai ko don nasan halin ki?”

Ɗan ware manyan idanuwanta tayi tana ɗauke kai tace “eh yaya”.

Be ce komi ba yamayar da kansa kan kallon sa, ita kuma jingina tayi da jikin sa tana kallon, MBC Action yake kallo ana wrestling????, miƙe wa kuma tayi tanufi wajen Fridge taɗauko Apple guda ɗaya tadawo tazauna tana ci idanunta na kan t.v, Suhaib kallon ta yayi sannan yamiƙa hannu ya’amsa Apple ɗin yakai baki yagutsira yamiƙa mata, can wrestling yayi nisa RAUDHA tasoma ihu tana kiran sunan Jonecena ganin yana shirin cin Kevin Owne (KO), shi kuwa Suhaib kallon kawai yake yi abinsa, can da tadame sa yajuyo yana kallon ta yaga tsaban ihu bata ma san tayar da raguwan Apple ɗin ba, ɗauka yayi yasoma ci kafin yace

“Baby kiyi ahankali Mana karki kashe min dodon kunne”.

Bata ma san yana yi ba, daga ƙarshe ma gaban t.v ɗin takoma kamar zata shige cikin plasma ɗin, Suhaib sai faman ƙorafin tana kare masa yake yi but taƙi tashi, lokacin da Jonesina yaci kuwa wani irin ihu tasaki tamiƙe tsaye tana tsalle cike da murna, sai kuma tasheƙo wajen Suhaib tana cewa

“Kagani Yaya yaci dama nasan shi zai ci, ina son mutumin nan wlh, kai kuma kafison KO yaci ko?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button