RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Babban Katafaren gidan Alh. M. Makamashi yana cikin K.R.G. ne, gidan da RAUDHA kuma ke zaune mallakin ta ne da Daddyn ta yamallaka mata, dawowarta gidan kuma ya samo  asali ne saboda tafiye-tafiyen da Dad ɗin ta yake yi don mutum ne da ba mazauni ba, idan yadawo shine take komawa babban katafaren gidan su acewarta tana jin tsoron gidan.

              “`RAUDHA“`

Duk yanda zan fasalta muku yanda take ta wuce nan, yarinya ce sangartacciya da iyayenta suka ɓata ta da gata tun tana tsunman goyo, sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, basa son kukan ta bare fushin ta, hakan yasaka tataso babu ƙwaɓa take yin duk abinda taso, tun tana ƴar shekara 15 tasoma harkan shaye-shaye kuma hakan ya faro asali ne daga ƙawayen ta na school, ita ɗin yarinya ce me son rayuwan ƴanci don haka take yin duk abinda taso akuma lokacin da taso babu me hana ta, daga mahaifin ta har Yayanta suna matuƙar ƙaunar ta fiye da kansu, haɗuwar su da Ramcy tun fara zuwan ta Club ne, ita yarinya ce me son rawa don haka take zuwa sabida nishaɗin ta, anan suka haɗu da Ramcy har tasu tazo ɗaya

Ramcy ƴar talakawa ne amma suna da rufin asiri sosai, itama gangararriya ce sosai agidan su, haɗuwan su da RAUDHA kuma sai abun yaƙara yin yawa, a kayan maye babu abinda basu sha

Dad da Suhaib sun daɗe da sanin halin da RAUDHA take ciki sai dai har yanzu sun kasa hana ta abinda take yi sai fatan shiriya da suke mata, kuma hakan yana faruwa ne saboda basa ƙaunar su ɓata mata.

     RAUDHA irin yarinyan nan ne masu bala’in taurin kan tsiya, idan har tace zatayi abu to babu wanda ya’isa yahana ta, idan kuma tace bazata yi ba babu wanda ya’isa yasata tayi, ko kaɗan bata damu da rayuwan kowa ba rayuwanta kawai tasani duk wanda yataka ta to tana ƙoƙarin ɗaukan mataki, bata da sabo ko kaɗan idan har bada mahaifinta ko Ƴayanta ba, har ta da saurayi taƙi yarda tayi sabida a rayuwanta ko kaɗan babu tsarin soyayya, babu namijin da yataɓa burge ta bare har tashiga sabgan sa, ita dai ƙyale ta da harkan shaye-shaye anan tafi auki

Yanzu shekaran ta 19years ne, kyakkyawa ce na gaban kwatance, bata da ƙiban jiki sai dai kuma bata da rama ko kaɗan, kai da ka ganta kasan ita ɗin ƴar hutu ce da jindaɗi, skin ɗin ta fari ne me haɗe da sirkin ja, idanuwanta manya masu gazar-gazar ɗin gashi, haka ma gashin giranta me yawan gaske ne har yana haɗewa, sosai take da kufan gashi ajikinta ko ta ina, kallo ɗaya idan kayi mata baza ka so kaɗauke idanunka akanta ba coz haɗuwarta da tsananin kyawun ta, abu mafi burgewa atattare da ita shine muryan ta, idan tana magana har baza ka so tadena ba yanda muryan ta yake fita ɗan siriri kuma kamar tana mura, hakan na ɗaukan hankalin mutune sosai

Yanzu haka ta gama scondary school???? ɗinta tana jiran Admission taci gaba da karatun ta, sosai take da ƙoƙari a makaranta don bata wasa da karatun ta, wannan yasa duk rashin jinta Malamai suna ƙaunarta sosai, kuma ƙoƙarin nata yajawo mata farin jini har take yin duk abinda taso a school ɗin batare da ko harara ta samu ba, sannan kuma ansan matsayin mahaifin ta hakan yasaka da wanda ke sonta don Allah da wanda ke sonta ba don Allah ba duk suna tare da ita.

.

_hmm yanzu me zai faru? Me kuke tunanin RAUDHA zatayi wa Jawad?_

*Vote and comments plz*

[11/13/2020, 3:28 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON SIX*

_______???? *THE FOLLOWING DAY*

Tashinta kenan daga barcin da tasha tun daren jiya har ƙarfe 02:00pm. Na yau tana sheƙa barci, wanda hakan ko kaɗan baya damunta daɗewan ta tana barci, kuma hakan na faruwa ne idan tabugu takwanta bata iya tashi sai tai ta sheƙa barci kamar za’a sake mata wani daren, ahankali tamiƙe daga kan gadon ta tanufi Toilet tana murza idanun ta, wanka tayi tafito ɗaure da towel ajikin ta, direct gaban dressing mirror tanufa tazauna kan stool tasoma shafa Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi da tsada, bayan ta gama tamiƙe batare da tasake shafa komi ba tanufi Sif ɗin kayan ta taciro, ƴar shimi tasaka Milk colour da ɗan ƙaramin wandon sa shima Milk taɗau wayan ta tafito, ƙafafun ta babu takalmi haka take taka Steps ɗin benen tana saukowa at the same time tana latsa wayan ta, kan kujerun parlour’n tanufa tashige cikin one sitter tana ɗaura ƙafafuwan ta kan Centre table, latsa wayanta take yi tana girgiza ƙafafu, can taɗago kai tana kwaɗa wa Saude kira, kamar tana jira sai gata tafito ta gurfana gabanta

“Miƙo min Malt”.

Tashi tayi tanufi wajen Fridge tabuɗe taɗauko Mata Maltina takawo mata, bata amsa ba kuma bata ɗago kai daga latsa wayan da take yi ba

“Ranki yadaɗe gashi”.

“Buɗe”. Tafaɗa ataƙaice

Buɗewa tayi tamiƙo mata tasanya hannu ta’amsa, ita kuma tatashi tawuce

Tana nan zaune tana kurɓan Maltinan ahankali tana Chatting wayan ta yasoma ringing, kallon screan ɗin wayan take yi tana ci gaba da kurɓan Maltinan, peacking call ɗin tayi takanga a kunne, daga can Ramcy tace

“Besty komi ya kammala, yanzu haka ina da labarin Saurayin nan”.

“Ok ki taho ina jiran ki”.

Bata jira cewarta ba takatse wayan tana ci gaba da Chatting ɗin ta

Mintuna 20 sai ga Ramcy ta shigo, zama tayi tana kallon RAUDHA da taɗago kai tasauke shanyayyun idanuwan ta akanta, tasan tana jiran tabata bayanan ne hakan yasaka tasoma sanar mata

“Sunan sa

Jawad Abdullahi yana zaune a Tudun wada, sana’ar sa shine harkan zane kuma shagon sa yana bakin titin gidan su ne, anan koda yaushe za’a iya samun shi, sannan shi ɗaya ne ɗa agidan su kuma shi ke ɗaukan  nauyin..”

Tsai da ita tayi da faɗin “wannan bayanin be shafe Ni ba tunda kin gano inda yake”.

Sauke ƙafafuwan ta tayi daga kan Centre table ɗin tamiƙe tsaye tana kai komo a tsakankanin wajen, Ramcy kuma sai kallon ta take yi kamar wata baƙuwa agare ta, tasan halin RAUDHA sosai yanzu haka mugun abu take shiryawa aranta, tasan tunda tayi ninyan ɗaukan fansa babu wanda zai iya hanata That’s why tayi shiru da bakin ta tana jiran taga abinda zata aiwatar

Riƙe ƙugunta tayi da hannayen ta tana sauke manyan idanuwanta da suka sake ƙanƙancewa akan Ramcy ɗin, cije laɓɓanta tayi cike da tsananin ɓacin rai tace “Ramcy ina zan samu Ƴan daba?”

Ramcy zaro idanuwanta waje tayi tana kallon RAUDHA da lokaci ɗaya tarikiɗe babu ko ɗigon rahma a fuskarta, idanun ta sunyi jazur haka ma fuskarta yayi ja tamkar tattasai, haɗiye yawu Ramcy tayi don ita akwai ta da tsoro, cikin tashin hankali tace

“Me kike shirin aikatawa ne Besty? Kar kuma daga baya asamu..”

“Ban tambaye ki wannan ba, ki sanar dani inda zan samu ƴan daba”.

Cike da sanyin murya Ramcy tace “sai dai anemo su tunda kina buƙata”.

Murmushi me kyau RAUDHA tasaki tana wani lumshe idanuwa tana buɗewa, kana kuma takoma tazauna tana harɗe ƙafafu tace “good My Besty”.

Daga haka tayi shiru tana jingina kanta da kujera talumshe lumsassun idanun ta tana jan numfashi, shiru ne yagibta a tsakanin su ita dai Ramcy idanuwanta na kan ta sai dai tunanin abinda take shirin aikatawa take yi da abinda zai biyo baya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button