RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Daga haka dai basu iya cewa komi ba suka juya suka tafi, Napep suka hau yakai su har Zaria Locost inda gidan RAUDHA yake

Bayan sun sauka suka nufi bakin Gate ɗin gidan suka ƙwanƙwasa, babu jimawa Gate Man yabuɗe musu

“Bayin Allah lafiya?’ cewar Gate man yana bin su da kallo

Deeni ne yayi masa bayanin RAUDHA suka zo nema, don haka yace “su jira sa anan yaje ya’isar mata da saƙon zuwan su”

Yanda yafaɗa musu haka sukayi suka jingina a garun gidan suna jiran dawowarsa

Shi kuma yanufi cikin gidan yayi Nocking a bakin ƙofan parlour’n

RAUDHA na kwance cikin one Sitter, sai lilo take yi da ƙafafuwan ta da basu samu zama kan kujeran ba, wayan ta take latsawa kuma tana bin music ɗin da yakaraɗe parlour’n da ƙara wanda tasaka shi a t.v

Har Larai dake Moping wajen Fridge sai da tajuyo Nocking ɗin ƙofa amma RAUDHA bataji ba, hakan yasa ta’ajiye sandan Moping ɗin tanufi ƙofan tabuɗe

Ganin Me gadi yasaka ta faɗaɗa fara’arta tana faɗin “Baba Ashe Kai ne?”

“Eh wlh tun ɗazu ina ta buga ƙofa shiru, dama Hajiya ce tayi baƙi awaje nazo in sanar mata”.

“To Baba bari in faɗa mata”. Larai tafaɗa maganar tana juyawa ciki dasauri

Gaban RAUDHA taje tarisina tasanar mata saƙon me gadi

Yamutsa fuska tayi tana kallon ta kamar baza tayi magana ba, can kuma tace “aje a tambayi su waye?”

“To ranki yadaɗe”. Larai tafaɗa tana miƙewa tsaye takoma tasanar da Me gadi

Sai da yasake komawa yatambaye su kafin yadawo yafaɗa mata

Larai takoma wajen RAUDHA tace “Hajiya wai Mahaifiyar Jawad ne”.

Shiru RAUDHA tayi tana tunanin me irin sunan, sake maimaita sunan tayi cikin ranta amma takasa tuno inda tasan me sunan, kuma bata tunanin tasan me sunan don haka takalli Larai tana jan gajeren tsaki tace

“Ke koma kice idan baza suyi bayani yanda zan gane ba su koma inda suka fito”.

Babu musu kuwa Larai tasake komawa tashaida wa me gadi, shima yasake komawa yafaɗa musu yanda tace

Deeni ne yayi musu bayani yanda zata fahimta sannan akazo aka sanar mata

Umarni taba da a shigo dasu.

Lokacin da suka shigo cikin parlour’n sanyi da ƙamshin daɗi ne kawai ke ratsa ƙofofin hancin su, haka suka koma ƴan ƙauye suna kallon haɗaɗɗen tsararren parlour’n da aka kashe masa maƙudan kuɗi kamar baza’a mutu ba

“Gaskiya kuɗi na inda suke waii”. Cewar Deeni da yayi maganar a maƙoshi yana sake ƙare ma parlour’n kallo alokacin da suka gurfana gaban RAUDHA

Bata yi musu magana ba don kallo ɗaya tayi musu tunda suka shigo

Mahaifiyar Jawad ɗin ne cikin girmamawa tace “dama munzo ne maganar yarona da kika sa aka kama, kuma ance sai munzo mun baki haƙuri kafin asake sa, don Allah kiyi haƙuri da duk abinda yafaru munsan yayi laifi hakan bazai sake faruwa ba, ki taimaka ki saka baki a sakar min ɗa shi kaɗai Allah yabani”. Taƙarike maganar nata tana sharan hawaye da gefen Hijabin ta

RAUDHA kuwa sai faman yamutsa fuska take yi maganar matan duk ya cika mata kunne, sai da tadire aya kafin taɗago lumsassun idanuwanta taƙare musu kallo daga matar har Deeni dashi yakasa furta komi sai kallon RAUDHA yake yi, a ransa yana tunanin rashin mutunci da rashin imani na masu kuɗi

“zan saka a sakar miki yaro amma ki ja masa kunne, duk ranan da yasake muka sake haɗa hanya dashi wlh billahi sai na wulaƙanta rayuwansa, sai nayi masa abinda har ke uwarsa sai kinyi dana sanin zuwan ki duniya”. RAUDHA tafaɗa maganar cike da wani irin fushi da rashin tarbiyya

Sosai ranta yasake ɓaci akan abinda yayi mata kamar yanzu ne abun yafaru, duk idan tatuna cewa shi kaɗai ne mutumin da yataɓa ɗaukan hannu yasaka ajikin ta da sunan duka sai ranta yayi mata ɗaci tare da tsananin tsanar sa me girma, har tana jin kamar hukuncin da taɗauka akan sa yayi kaɗan akan abinda yayi mata

Su kuwa tsananin mamakin maganar ta ne yake ɗawainiya dasu, sai dai sun kasa furta komi sai sake bata haƙuri da Maman Jawad tasake yi

Hannu kawai tanuna musu alamun su bar mata gida, haka suka tashi suka fice suna me sake mamakin yarinyan da babu ko ɗigon tarbiyya atare da ita

Larai dake tsaye tana ganin abinda ke faruwa taɓe baki kawai tayi taci gaba da aikin ta, aranta tana mamakin abinda waɗannan mutanen sukayi da har suka fusata Hajiyar tasu haka don tasan ba abu bane ƙanƙani

Ƙaran gudun RAUDHAN ne yasa tasake ɗaga kanta tana bin RAUDHA da kallo da har ta haye sama, gashi dama takalmi ne me tsini a ƙafafun ta da tafita dashi bata cire ba kasancewar a parlour tayaɗa zango dawowarta inda taje

Jinjina kanta Larai tayi tana al’ajabin wannan kasada na RAUDHA, ko tsoron tagurɗe tafaɗo bata yi

Ita kuwa tana shiga ɗakin Fridge tanufa tasaka keey tabuɗe taciro Wine ???? takoma Kan kujera tazube tana sha, yanda fuskarta yayi jazur zaka gane ba cikin Mood ɗinta take ba, sai faman kurɓan wine ɗin take yi babu ko sassautawa

Ringing ɗin wayan ta yadawo da ita cikin hayyacin ta, taɗau wayan taduba screan ɗin, DPO ne yakira ta sai tayi peacking batare da tajira yayi magana ba cikin muryan maye tace

“D..P..O kasakeee shiii kawai”.

Tsinke wayan tayi batare da taji me zai faɗa ba, ta’ajiye taci gaba da kwankwaɗan Wine ɗin ta, sai da tasha tayi tatul sannan tahaƙura, daga nan barci ne yaɗauke ta a zaune akan kujeran kan ta na jingine jikin sofan.

       ????????????

     Sai bayan magriba tafarka, idanunta tasoma buɗe wa tana rufewa, daƙyar ta’iya buɗe su gaba ɗaya tana faman yamutsa fuska, hannunta ɗaya taɗago taɗaura kan wuyan ta da yasanƙare sakamakon yanda takwanta ɗin, sake yamutsa fuskarta tayi jin azaban zafi ya ziyarce ta kasancewar wuyan yayi tsami sosai, daƙyar ta’iya ɗago kanta tana faman runtse idanu, a wannan karon duka hannunta taɗaura saman wuyan ta tana faman matsawa tare da juya kanta, ta jima ahaka kafin tasoma jin dai-dai

Wayan ta da tasoma tsiwa tana neman agaji takai dubanta ga wayan, sai kuma tasauke hannayen nata tana sake jujjuya kanta kafin taɗau wayan tana kallon screan ɗin

MY BLOOD yafito ɓaro-ɓaro a gaban wayan, peacking tayi takara a kunne cike da muryan maye da yahaɗe dana barci tace

“Ya..yah..”

Suhaib da yaji muryan ƙanwar tasa ta ratsa masa kunne sai yalumshe idanun sa cike da ƙaunar ta yace. “my Sweetheart Ina kika shiga ne na kira wayan ki but baki ɗauka ba?”

“Uhmm.. uhm ina.. barci ne Ya..yaah..”

Shiru yayi Suhaib yana sauraron yanda take masa magana, babu shakka yasan da cewa har yanzu ƙanwar sa bata bar halin ta na shaye-shaye ba, a duniya babu abinda yatsana sama da wannan ɗibi’an da ƙanwar tasa ta koya, but ƙaunar da yake mata yafi rinjayar komi hakan yasaka baya iya ɗaukan mataki wajen ganin ya hanata banzan ɗabi’an nan..

“Ya..ya kana jiiinaaa kuwa..?” Takatse masa ɗan guntun tunanin sa

Ajiyan zuciya yasauke cikin taushin murya yace “Baby Wai yaushe ne zaki dena shaye-shayen nan da kike yi? Babu shakka naji ajikina sai da kika sha kafin kiyi barci, ina ƙaunar ki My sister bazan taɓa iya juran abinda zai same ki ba nan gaba, kinsan da cewa duk wanda yake shaye-shaye ƙarshen sa baya kyau? Bana son kina cutar da kanki ƙanwata don Allah ki dena kinji?”

Shiru kawai tayi tana sauraron sa ba wai don taji maganar nasa ba, sai tamatse baki kawai tana cije leɓen ta batare da ta kula sa ba

Shi kuma shirun ta ya san cewa baza ta amsa bane, kuma yasan idan yaci gaba da mata magana zata iya yin fushi yanzu takashe wayan wanda baya fatan hakan tafaru

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button