RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

        Ba ita tatashi ba sai washe gari ƙarfe 01:30pm. Ahankali take buɗe kyawawan idanunta da suke ashanye koda yaushe, hannun ta duk ka biyun tasaka tariƙe kanta tana sake lumshe idanuwanta, ta ɗan jima ahaka kafin tacire hannun tana sake gyara kwanciyarta cike da tsananin gajiya, ko kaɗan barcin be ishe ta ba so take yi tasake komawa, sai dai ƙarar wayan ta shi yawartsakar da ita, hannu tasaka taciro cikin jakan ta tana kallon screan ɗin, MY DEAR DAD aka rubuta, peacking tayi tasaka a kunne still tana gyara kwanciyarta, daga ɗaya side ɗin Dad ɗin ta ne yasoma magana

“My Baby good morning”.

Lumshe idanu tayi tana buɗe wa kana ta’amsa mishi “morning Daddy”.

“Baby har yanzu baki tashi barcin bane?”

“Eh”. Tabashi amsa ataƙaice

“Ok Allah yasa bani natashe ki ba don bana son takura miki?”

Memakon ta’amsa mishi tambayan sai canza maganar tayi dacewa “Daddy yaushe zaka dawo ne I miss You More?”

“Sorry My Baby umm? very soon Zaki ganni”.

Cikin dashashshiyar muryan ta cike da shagwaɓa tace “Daddy kasaka mana azo a ɗauke ni nagaji da zama Ni kaɗai, komi babu daɗi”.

Daddy cikin lallami tare da ƙaunar ƴar tasa yace “sorry Babyna ai nace miki nakusa dawowa very soon zaki ganni, and kuma kinga kin kusa fara school bazai yiwu ki biyo ni ba”.

“Daddy to ba sai kasaka Ni school ɗin nan ba, dama bana son anan”.

Murmushi yayi yace “Sweetheart kinsan ba zama nake yi ba, bana son kiyi nesa Dani that’s why nafison kiyi karatun ki anan Nageria”.

Turo baki kawai tayi bata sake cewa komi ba, Daddy lallaɓa ta yai tayi don yasan fushi tayi, shi kuma baya son ne taje Abroad tasake lalacewa coz yasan ta ba tarbiyya ne ya’ishe ta ba, yanzu haka ma nema mata shiriya yake yi Allah yashirye ta don duk abinda take yi yana sane dashi, sai dai tsananin ƙaunar da yake mata bazai saka yayi mata faɗa ba

Muryan ta shi yadawo dashi gajeren tunanin sa

“Daddy I will call you back idan nayi Lunch”.

“Ok My Baby Baki buƙatar komi ko?”

Cikin nuna sangarta tace “Daddy katura min kuɗi zan fita Shopping yau”.

“Ok byee take Care”.

“Byeeee Daddy”.

Ajiye wayan tayi sannan tatashi tazauna tasoma cire Hill shoes ɗin ƙafanta, Ribom ɗin kanta dake yashe a ƙasa taɗauka taɗaure gashin ta sannan tamiƙe tanufi gaban plasma t.v dake ɗakin takunna, Remote taɗauka tasoma sauya Channels, a BOM t.v tabar shi sannan tasaka Volume gaba ɗaya, nan da nan ko’ina yaƙaraɗe da Music ɗin da akeyi kasancewar akwai irin manya-mayan speakers???? masu matuƙar ƙara da ɗaukan duma, Toilet tashige tana bin waƙar kamar ita take rerawa, Brosh kawai tayi tafito tanufi ƙofan fita tafice ƙafarta ko takalmi, Steps tasoma takawa da gudu-gudu don ita akwai son gudu, tana jinta kamar ƴar chali-cahli ce

lokacin da ta’isa tanƙamemen parlour’n tabuɗe muryan ta da yake adishe koda yaushe tamkar tana mura tasoma kiran masu aikin ta, kafin tarufe baki suka fito suka gurfana gaban ta

“Where is my lunch?”. Tatambaye su tana bin su da kallo da shanyayyun idanun ta

Saude wacce take kula da abincin ta tace “yanzu zan zuba a warmers in kawo dainning”.

“Ok ki kawo min ɗakina ne”.

“An gama ranki yadaɗe”. Saude tafaɗa sannan tajuya takoma kichen

Kallon Larai tayi tace “ke kuma je ki sanar da Idi yawanke min Motan Daddy yanzu”.

Cike da girmamawa Larai ta’amsa mata sannan tafice dasauri don isar da saƙon uwargijiyarta, ita kuma juyawa tayi tasoma taka steps ɗin da gudu takoma ɗakinta, tana shiga tanufi Drower tabuɗe taciro wasu Tables taciri ɗaya tasaka a bakin ta, Fridge tanufa tabuɗe taɗau Faro water takora dashi, kan sofa tanufa tana riƙe kanta tazauna dai-dai lokacin da Saude tashigo riƙe da farantin Silver ta’iso gabanta ta’ajiye kan Centre table dake gaban kujeran da yake guda ɗaya cikin ɗakin

“Ranki yadaɗe gashi”.

RAUDHA da tasoma hawa kan network ɗago shanyayyun idanunta tayi takalle ta kafin tayi mata alama da hannu tatafi, juyawa Saude tayi tanufi ƙofa, sai da tabuɗe ƙofar kafin tajuyo tana kallon RAUDHAN da har yanzu take riƙe da kanta, cikin ranta sosai take tausayin yarinyan kuma take  mata fatan shiriya, duk da wani lokacin bata da kirki idan har sukayi mata ba dai-dai ba haka zata zazzage musu tijara son ranta, but idan har zasu kiyaye ƙa’idan ta to babu abinda ke shiga tsakanin su don ita ɗin ba me son shiga rayuwan wasu bane idan be shafe ta ba

Saude ganin RAUDHA zata ɗago kai yasaka tayi saurin fita tana rufo ƙofan.

     Ahankali tasaka zara-zaran hannunta tabuɗe abincin, Jolof Raice ne da yaji meat and veggies a sama, ɗayan Coolar’n kuma da tabuɗe ferfesun kayan ciki ne, a plate tazuba tasoma ci, sosai taci abincin kasancewar batayi breakfast ba, bayan ta gama miƙe wa tayi tacire kayan jikin ta tashige toilet, ita kuma Saude lokacin tadawo takwashe kayan abincin tafitar dasu

Minti 15 yaɗauke ta kafin tafito, doguwar riga tazira sannan tasaka Hijab tasoma gabatar da sallan asuba kafin tayi azahar, dama haka take yi koda yaushe, wani lokacin ma gaba ɗaya haɗe su take yi da dare tayi su, akwai ta da son wasa da ibada duk da ba wani addini tasani ba, but ko ta tara su idan tatashi sai tahaɗe tayi, tana idarwa ko tsayawa addu’a batayi ba tamiƙe tasoma tuɓe rigan, towel taɗaura tanufi gaban mirror tazauna tasoma shafa Lotions tana bin music ɗin dake tashi cikin t.v at the same tana kaɗa jikinta tana rawa, Light makeup tayi tamiƙe tanufi gaban sif ɗin kayan ta tazaɓo kayan da zata saka tazube kan gado, komawa tayi tazauna a bakin gadon taɗau wayan ta tana latsawa, ta ɗan jima kafin tamiƙe tasanya kayan, ƙaramar riga ce White wanda tatsaya mata iya cibiya, don idan har zata ɗaga hannun ta ko tayi motsi me ƙarfi ana hango cibiyanta, sai tasaka wandon rigan Robber iya gwiwarta shima fari, gaba ɗaya santalelen ƙaurin ƙafanta a waje yake, zama tayi tasoma zira socks white da yakawo mata har kusa da wandon ta sannan tasaka Hill shoes Black me igiya, miƙewa tayi takoma gaban mirror tasake gyara gashinta da yake baƙi siɗik taɗaure da Black Ribom sannan tafeshe jikinta da Parfomers masu shegen ƙamshi, miƙewa tayi tana wani jujjuya wa tana sake kallon kanta a mirror, sosai tayi matuƙar kyau kamar wata baturiya, dama ita irin shigan Turawa ke burge ta kuma shi ɗin take yi, ko kaɗan bata ta’ammali da kayan Hausa don haka farat ɗaya idan kaganta baza ka taɓa tunanin ta haɗa hanya da Hausawa ba coz babu ta inda take kama dasu, sai da tagama jujjuya jikin ta kafin taje tazaro Wizy Bag ɗin ta tare da ɗaukan wayan ta tafice batare da tayafa komi ba, haka tabar ɗakin ko T.v bata kashe ba, sai dai idan Larai me aikin ta tazo gyara ɗakin itace zata kashe mata.

[11/13/2020, 2:32 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What’sapp Number 07065334256~

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON TWO*

_______????Packing space tanufa tabuɗe motan tashiga but sai dai bata shigar da ƙafafunta ciki ba, Lockern cikin motan tabuɗe taciro wani farin Robber tabuɗe, Coken ne aciki sai tazuba a tafin hannun ta tana shaƙa, sosai tashaƙa don sai da taji ta kan network kafin tajinginar da kanta tana lumshe idanu, as usual tana son taji ta kan network that’s why bata rabo da shan kayan maye, abin ma har yabi jininta, kana kallon idanunta da kuma yanda take yawan lumshe su zakasan ita ɗin ƴar ƙwaya ce, sai da taɗau kamar minti 5 kafin tashigar da ƙafafuwan ta tarufe murfin, key tayi wa motan tafige ta tayi bakin Gate, oready dama Gateman yarigada ya buɗe mata Gate don yasan halin ta bata da jimirin jira, tana fita tahau kan titi kasancewar gidan nasu a bakin titi yake, da wani irin speed take Jan motan Wanda idan kagani kasan Drever’n ciki ba ƙalau take ba, duk inda tawuce sai an kalle ta, haka take over taking Cars tana wuce wa babu ruwan ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button