RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Ɗaya daga ciki ne yabuɗe baki cike da murmushi a face ɗin sa yace “ah Madam Ina zuwa haka?”

Ramcy da har yanzu jikin ta ke faman rawa takalle sa kamar zatayi magana sai kuma taga RAUDHA yake kallo tayi gum da bakin ta

Cikin dashashshiyar muryan ta tabashi amsa a taƙaice tana kawar da kanta

Washe baki yasake yi yana kallon sauran ƴan uwan nasa da suka tsira wa RAUDHA idanu kamar sun sami t.v yace “ku wuce kawai zan ji dasu”.

“Ok”. Suka faɗa atare suka juya suka tafi batare da sun so ba, sai dan shi ɗin shine babban su dole subi umarnin sa

“Baby bakya jin tsoro kike yin irin wannan tuƙin?”

Shiru tayi bata tanka sa ba

 Sai yasake sakin murmushi yakalli Ramcy yana kashe mata ido ɗaya sannan yanuna mata RAUDHA da hannu

*_________________________*

Daga can nesa wani matashin saurayi ne da yake tsaye yana waya amma idanun sa na kan motan su RAUDHA, tun sanda suka taho yake kallon motan yana mamakin ƙarfin hali da rashin hankalin matuƙin

Sanye yake cikin kakinsa da sukayi masa bala’in kyau tare da fito da ƙaƙƙarfan ƙirar jikin sa, wanda kallo ɗaya idan kayi masa zaka san Jarumin Namiji ne na bugawa a jarida, sannan a kallo ɗaya idan kayi masa baza ka iya tantance shi ɗin wani irin yare bane coz ko kusa be yi kama da ɗan Nigeria ba

Wayan yakashe sannan yatura cikin aljihu yanufi wajen motan cikin takunsa na mazantaka da nuna shi ɗin Jarumi ne

Isowar sa wajen maganar Sojan da yake wajen su Ramcy yasauka a kunnen sa, yana tambayan su Numban waya

Ɗaure kyakykyawar fuskar sa tamau yayi don yarigada ya gane mata ne aciki

Jikin motan yaƙarisa yanda zai hangi mutanen ciki, nan kuwa yasauke idanun sa kan Ramcy da itama tazuba masa idanun cike da tsananin firgita da ganin murɗaɗɗen mutumin dake tsaye a gaban ta babu ɗigon annuri

Saurin Solute ɗin sa Sojan yayi

Be kalle sa ba sai sake tamke fuska yayi yakai duban sa side ɗin RAUDHA da takawar da kanta har alokacin kuma bata sauke hannayen ta kan sitiyarin motan ba, sai faman karkaɗa yatsunta take yi

Tsira mata idanu kawai yayi yana kallon kyakykyawar fuskarta

Lokacin ita kuma tajuyo da face ɗin ta sosai yanda zai iya ganin ta sai dai idanun ta suna lumshe ne batare da ta kalle sa ba takwantar da kanta jikin kujeran

Gashin giranta dake haɗe masu yawan gaske yabi da kallo kafin yasoma bin jikin ta da idanunsa kamar wanda ke neman wani abu, sosai yarinyan tatafi da imanin sa sai dai shigan da tayi ya san cewa ita ɗin ba kalan su bane don batayi masa kama da me kallon gabas ba

Ajiyan zuciya yasaki a ɓoye, sannan yakalli sojan dake tsaye yana kallon sa tare da Ramcy sai yaji kunya, amma sai yawayance yakau da kansa yana sake haɗe rai yace

“Jone Aikin da kazo yi kenan tambayan numban su?”

Jin muryan sa cikin kunnen ta yasaka ta buɗe idanun ta tana kallon sa

Shi kuma alokacin kallon Jone ɗin yake yi

“No Sir”. Cewar Jone ɗin yana sake Solute ɗin sa

Gajeren tsaki yaja yana maida idanun sa cikin motan, nan kuwa idanun sa yafaɗa cikin nata da tazuba mishi tana kallon sa batare da kunyan sa ba

Gaban sa ne yafaɗi sai yayi saurin ɗauke nashi idanun murya a kausashe yace “kuna mata kuke irin wannan tuƙin gangancin kuna da hankali kuwa?”

Duƙar da kanta Ramcy tayi duk jikin ta sai mazari yake yi, sosai muryan sa yatsorata ta, tasan da cewa wannan mutumin ba barin su zai yi ba, shikenan yau RAUDHA taja musu ta kawo su inda za’a kashe su

Ita kuwa RAUDHA har yanzu kallon sa take yi batare da  tsoro ba, sai ma lumshe idanun ta tayi bata da ninyan bashi amsa, ko kaɗan a yanzu bata son yin magana sabida ƙwayoyin da tasha

Sosai yaji haushin shirun da tayi, cikin fusata yace “ba da ku nake magana ba?”

A karo na biyu tasake kallon sa shima ɗin tsatstsare ta da idanun sa yayi batare da ya kawar ba

Cikin rawan murya Ramcy tace “yallaɓai kayi haƙuri don Allah”.

Shima Jone cikin girmamawa yace “Oga sorry sun faɗa min abinda yasa…”

Ɗaga masa hannu yayi dole yayi shiru yahaɗiye ƙaryan da yake son shirgawa.

.

_To fa yau RAUDHA da alamun ta taɓo dai-dai ita, bari mu jira me zai faru._

_Kar ku manta da yawan Comment shi zai sa naƙara yawan typing._

[11/14/2020, 8:51 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON ELEVEN*

_______????”Katabbatar sun nuna maka takardun motan su kafin su wuce”. Yafaɗa maganar yana kallon Jone fuska a ɗaure

“Ok sir”. Jone yafaɗa yana me sara masa

Juyawa yayi kawai yatafi cikin tafiyan sa na zaratan maza yabar wajen

Lumshe idanun ta tayi tana sake kwantar da kanta jikin kujeran, tana jin sanda Jone yake sake tambayan Ramcy numban wayan ta, kuma tana jin sanda yayi musu sallama har yana ce mata

“Baby baza ki buɗe idanun ki muyi ban kwana ba?”

Buɗe idanun kuwa tayi sai dai bata kalle sa ba tayi wa motan keey taja da wani irin Speed tabar wajen

Gaba ɗaya sojojin sake kallon motan sukayi suna jinjina ƙarfin hali irin na RAUDHA, tabbas ko basu faɗa ba akwai abinda tataka har take iya yin hakan agaban su

Shima ɗin idanun sa kawai yazuba ma motan cike da mamakin tantiranci irin na yarinyan da har take musu tsaurin ido, har motan taɓace ma ganin sa kafin yadena kallon hanyan. Ahankali yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana me lumshe idanun sa cike da tuno suffarta, murmushin sa me kyau yasaki yana ɗaukan wayan sa dake faman ƙara yakanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin.

          ????????????

Har suka shiga cikin Kaduna babu wanda ke magana cikin su

Akaro na biyu RAUDHA tasake kallon Ramcy da har yanzu bata dawo dai-dai ba, juya kanta tayi kafin tasake maimaita tambayan da tayi mata

“Ramcy tunanin me kike yi ne ina tambayan ki ina muka dosa?”

Sai alokacin Ramcy tadawo hayyacin ta sosai, cikin jan numfashi tace “uhmm Besty wlh ban ji ba duk hankalina ya tashi da ganin wannan dogon mutumin me murɗaɗɗen jiki, nayi tunanin yau kashin mu ya bushe wlh, don nasan halin sojoji basu da mutunci ko kaɗan”.

Siririn tsaki RAUDHA taja batare da tace uffan ba taci gaba da sharara gudu

Ganin haka yasa Ramcy tasoma nuna mata inda zasu yi

A ƙofar wani madaidaicin gida suka tsaya, gidan me dakali ne da yasha suminti tare da sabon penti, koda gani ansan cewa gidan ana sha’ani sabida yanda mutane maza  da mata suka cika ƙofar gidan, da alamun dai wani wajen Za’a tafi don gefe ɗaya motoci ne sun fi biyar afake

Tunda motan tatsaya yawancin mutanen wajen sai idanuwan su yadawo wajajen

Sun ɗau lokaci kafin Ramcy tasoma fitowa, sai da tafito taleƙa da kanta tana kallon RAUDHA da bata da alamun fitowa tace

“My Besty don Allah fito mushiga kiyi haƙuri”.

Yamutsa fuska RAUDHA tayi tana sake kallon mutanen wajen ta cikin motan, cikin ƙare musu kallo da taɓara tace “kinsan bana Son mutane idan nafita kallona zasu riƙa yi”.

Dawowa ciki Ramcy tayi tace “Plz Mana Besty Ina ruwan ki dasu? Kar ma ki kalli kowa kinji?”.

Gyaɗa kanta tayi tana sake ware idanun ta tana kallon su, sai da ta ɗan ja lokaci kafin tabuɗe motan tafito bayan ta mayar da hulanta akai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button